Sana'o'i takwas da za a iya farawa da Naira 100,000

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A Najeriya, matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da sa mutane da dama neman sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga.
Duk da yadda ake ganin fara kasuwanci na buƙatar babban jari, masana na cewa akwai sana'o'i da dama da mutum zai iya farawa da kuɗi kaɗan idan yana da kyakkyawan tsari da dabarun kula da jari.
Wani masanin tattalin arziƙi a Kano, Sani Umar, ya ce ƙananan sana'o'in da za a iya farawa da kusan naira 100,000 na iya taka muhimmiyar rawa wajen rage matsin tattalin arziki, musamman a lokacin da yawan masu neman aiki ke ƙaruwa.
Ya ce duk da cewa naira 100,000 ba babban jari ba ne a halin yanzu, tana iya zama matakin farko ga wanda ke son fara sana'a da bunƙasa ta a hankali.
"Naira 100,000 matakin farko ne, ba ƙarshen kasuwanci ba. Idan aka yi amfani da ita da kyau, za ta iya taimaka wa mutum ya fara sana'ar da za ta haɓaka a gaba," in ji shi.
Ga wasu sana'o'i biyar da masana ke ganin mutum zai iya farawa da kusan Naira 100,000 domin samar da wata hanyar samun kuɗin shiga:
Sayar da abinci da kayan ciye-ciye

Asalin hoton, Getty Images
Sani Umar ya ce sayar da abinci na daga cikin sana'o'in da ke da kasuwa a kowane lokaci.
Ya ce da naira 100,000 mutum zai iya fara sayar da ƙosai, waina, masa, samosa, ƙuli-ƙuli ko abincin rana ga ma'aikata da ɗalibai.
Ya jaddada cewa tsafta, ɗanɗano da samun amintattun kwastomomi su ne muhimman abubuwan da ke taimakawa wannan sana'a bunƙasa.
Sana'ar gyaran gashi ko kwalliya

Asalin hoton, Getty Images
Masanin ya ce mata da suka iya kitso da gyaran gashi za su iya fara sana'ar da Naira 100,000 ta hanyar sayen kayan aiki da fara aiki daga gida.
Ya ce ana iya ƙara samun kuɗi ta hanyar hidimar amarya, lalle da sauran ayyukan gyaran jiki.
Sana'ar ƴaƴan itatuwa da ruwansu

Asalin hoton, Getty Images
Sani Umar ya ce sana'ar matse ruwan 'ya'yan itatuwa na samun karɓuwa saboda yadda mutane ke ƙara kula da lafiyarsu.
Ya ce da naira 100,000 mutum zai iya fara matse ruwan lemu, mangwaro, abarba ko aya ya sayar a wuraren aiki, makarantu, kasuwanni da wajen taruka.
Sana'ar kayan masarufi na yau da kullum

Asalin hoton, Getty Images
Masanin tattalin arziƙin ya ce sayar da kayan masarufi kamar sabulu, man girki, kayan miya da sauran abubuwan yau da kullum na da kasuwa.
Ya ce mutum zai iya farawa da ƙaramin jari, ya sayar a unguwarsa ko ta kafafen sada zumunta, tare da mayar da riba cikin kasuwanci domin bunƙasa shi.
Sana'ar kayan sawa
Kayan sawa kamar hijabai, mayafai, huluna da wasu ƙananan kayan ado suna da kasuwa a tsakanin mutane daban-daban in ji masanin.
"Mutum zai iya fara da sayen kaya kaɗan daga manyan kasuwanni ya riƙa sayarwa ta yanar gizo ko a tsakanin abokai da maƙwabta." in ji shi.
Sayar da kayan kwalliya da turare

Asalin hoton, Getty Images
Sana'ar kayan kwalliya na da kasuwa saboda yawan amfani da turare, man shafawa da sauran kayayyakin gyaran jiki, in ji masanin.
Da Naira 100,000, mutum zai iya fara sayar da waɗannan kayayyaki ta hanyar amfani da WhatsApp da sauran kafafen sada zumunta ba tare da hayar shago ba.
Sana'ar wanki da guga

Asalin hoton, Getty Images
Sani Umar ya ce ana iya fara sana'ar wanki da guga da Naira 100,000 daga gida, kuma mutum ma zai iya sayen ƙaramin injin wanki domin sauƙaƙa aiki.
Ya ce sana'ar na da kasuwa musamman a birane, saboda wasu mutane na neman irin wannan sabis saboda ƙarancin lokaci.
Sana'ar POS

Asalin hoton, Getty Images
Masanin ya kuma ce mutum zai iya fara sana'ar POS da jarin Naira 100,000, musamman ganin yadda mutane da dama a yanzu ke amfani da POS wajen cire kuɗi ko tura su saboda sauri da sauƙin da ke tattare da hakan, maimakon zuwa banki.
Sai dai ya ce samun nasara a wannan sana'a ya danganta da zaɓar wurin da mutane ke yawan zirga-zirga, tare da kula da harkokin tsaro.
Muhimman abubuwan da ke taimakawa sana'a bunƙasa
A cewar masanin tattalin arziƙin, samun jari kaɗai ba ya tabbatar da nasarar kasuwanci.
Ya ce akwai wasu muhimman abubuwa da mai sana'a ya kamata ya kula da su domin bunƙasa kasuwancinsa kamar haka;
- Fahimtar yanayin kasuwanci
- Zaɓar wurin da ya dace
- Kula da kuɗin shiga da fita
- Raba jari da riba
- Kyakkyawar mu'amala da kwastomomi
- Kula da ingancin kaya ko hidima
- Yin talla
- Gujewa bashi marar tsari
- Girmama masu saye da sauraron korafe-korafensu
- Mayar da wani ɓangare na riba cikin kasuwanci
- Jajircewa da haƙuri
Masanin ya ce ƙananan 'yan kasuwa na fuskantar matsaloli da dama da kan hana sana'o'insu bunƙasa, ko da kuwa suna da jari. Daga cikin matsalolin akwai:
- Rashin raba kuɗin kasuwanci da na kai
- Kashe riba ba tare da bunƙasa kasuwanci ba
- Rashin rubuta kuɗin shiga da fita
- Rashin kyakkyawan tsarin kasuwanci
- Yawan bayar da kaya bashi
- Rashin haƙuri
- Rashin ilimin tafiyar da kasuwanci
Duk da ƙalubalen da ke tattare da fara ƙaramar sana'a, masanin na ganin cewa tana iya zama wata hanya ta samun kuɗin shiga idan aka gudanar da ita da tsari da kuma haƙuri.











