Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyi 7 da ya kamata abi don kauce wa rikici a zaben Najeriya na 2027
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC World News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, tambayar da ke ƙara ɗaukar hankali ita ce yadda za a gudanar da zaɓen cikin lumana, ba tare da an samu asarar rayuka ko dukiyoyi ba.
Duk da cewa yaƙin neman zaɓe wani ɓangare ne na tsarin dimokuraɗiyya, kalaman tunzura jama'a, da zafafan maganganun siyasa da kuma rikicin magoya bayan jam'iyyu na daga cikin abubuwan da ke ƙara tayar da hankalin al'umma a lokutan zaɓe.
Duba da yadda zaɓukan da suka gabata suka fuskanci zarge-zargen maguɗi, da tashin hankali da rashin jituwa tsakanin magoya bayan 'yan takara, masu sa ido kan harkokin zaɓe na ganin akwai buƙatar ɗaukar matakan kariya tun kafin ranar zaɓe, tare da tabbatar da zaman lafiya yayin zaɓe da kuma bayan sanar da sakamakonsa.
To, waɗanne matakai ne ya kamata 'yan siyasa, da hukumomin tsaro, da hukumomin zaɓe da sauran al'umma su ɗauka domin kauce wa sake afkuwar rikicin zaɓe a Najeriya?
Dangane da wannan batu, BBC ta tattauna da Farfesa Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja da ke Najeriya, domin jin ra'ayinsa kan hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya gudana cikin lumana.
1. Guje wa kalaman tunzura jama'a
A cewar masanin, ɗaya daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen rage rikicin zaɓe shi ne yadda 'yan siyasa da magoya bayansu za su gudanar da yakin neman zaɓe.
''Ya kamata 'yan takara su mayar da hankali kan manufofi, da shirye-shiryen ci gaba da hanyoyin magance matsalolin al'umma, maimakon amfani da kalaman batanci, barazana ko tunzura magoya baya'' a cewarsa.
Haka kuma, akwai buƙatar shugabanni da ma waɗanda ke nema a yanzu, su riƙa jan hankalin magoya bayansu kan muhimmancin mutunta ƴan adawa da kuma 'yancin kowane ɗan ƙasa na zaɓar wanda yake so.
A watan Agustan 2026, shugabannin jam'iyyu da wasu 'yan takarar shugaban ƙasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasa, wadda ke da nufin inganta kamfen na lumana da kuma hana tashin hankali yayin zaɓen 2027.
Sai dai sanya hannu kan yarjejeniya kaɗai ba zai wadatar ba idan ba a tabbatar da bin ƙa'idojin da ke cikinta ba.
2. Gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci
Ya ƙara da cewa wani muhimmin mataki shi ne tabbatar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓe cikin gaskiya, adalci da kuma nuna cikakken tsaka-tsaki.
A cewarsa rashi adalci ne tushen kowacce irin fitina, don haka ya kamata INEC wacce ke da alhakin gudanar da zaɓen ta tabbatar da ta samar da bayanai a kan lokaci, bayyana yadda ake gudanar da ayyukan zaɓe da kuma tabbatar da cewa ana bin ƙa'idoji iri ɗaya ga dukkan jam'iyyu.
''Haka kuma, ya kamata a tabbatar da gaskiya wajen tattara ƙuri'u da sanar da sakamakon zaɓe, domin kauce wa shakku da ka iya haifar da rikici'' a cewarsa.
Masu sa ido kan zaɓe sun sha jaddada cewa rashin amincewar jama'a da tsarin zaɓe na iya ƙara tsananta rikici, musamman idan aka samu rashin fahimta game da yadda aka gudanar da zaɓe.
3. Adalcin jami'an tsaro
A cewar masanin siyasar hukumomin tsaro ma suna da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce ''Ana buƙatar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye, tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'a''
Sai dai ya ce akwai buƙatar jami'an tsaron su kasance masu nuna adalci ba tare da nuna bambanci tsakanin jam'iyya mai mulki da 'yan adawa ba.
Haka kuma, ya ce ya kamata a gudanar da bincike kan duk wani rahoton barazana ko tashin hankali, tare da hukunta waɗanda aka samu da laifi bisa doka.
A cewar wani rahoton kwamitin zaman lafiya na Najeriyar a ranar 11 ga Nuwamban 2026, an samu rahotannin karya yarjejeniyar zaman lafiya guda 109 a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya Abuja cikin makonni goma na sa ido.
Rahoton ya bayyana cewa rikicin siyasa da ayyukan daba, tare da yaɗa bayanan ƙarya, na daga cikin manyan abubuwan da aka gano.
4. Yaƙi da labaran ƙarya a kafafen sada zumunta
A wannan zamani, kafafen sada zumunta na taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa bayanai game da harkokin siyasa da zaɓe.
Sai dai yaɗa bidiyo, da hotuna ko saƙonnin ƙarya da ke zargin wata jam'iyya ko ƙungiya da aikata laifi ba tare da tantance sahihancinsu ba, na iya haifar da tashin hankali.
Saboda haka, masanin ya ce akwai buƙatar jama'a su riƙa tantance sahihancin bayanan da suke yaɗawa, musamman a lokacin zaɓe da bayan sanar da sakamako.
Ya ce ''Ƴan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta su guji amfani da kalaman ƙiyayya da kuma bayanan da za su iya tayar da hankalin al'umma.
5. Rungumar ƙaddara da ra'ayin masu zaɓe
Bayan kammala zaɓe, ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta shi ne yadda wasu magoya bayan 'yan takara ke mayar da martani idan ɗan takararsu bai yi nasara ba.
Farfesa Abubakar Kari, na ganin cewa ya kamata jam'iyyu da 'yan takara su wayar da kan magoya bayansu cewa rashin nasara a zaɓe ba dalili ba ne na kai hari kan abokan hamayya ko lalata dukiyoyin jama'a.
''Duk wanda bai gamsu da sakamakon zaɓe ba yana da damar neman hakkinsa ta hanyar shigar da ƙara a kotu, maimakon ɗaukar doka a hannu'' in ji masanin.
Haka kuma, ya ce ya kamata 'yan takarar da suka yi nasara su guji kalaman raini ko nuna ƙyama ga waɗanda suka sha kaye, su kuma yi ƙoƙarin haɗa kan al'umma domin ci gaban ƙasa.
6. Tsayuwar dakar jagororin al'umma
Masanin ya ce shugabannin addini da na gargajiya suna da tasiri a tsakanin al'ummominsu, don haka za su iya taka muhimmiyar rawa wajen hana rikicin siyasa.
Ta hanyar wa'azi, da tarukan wayar da kai da tattaunawa tsakanin al'ummomi, za su iya ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna.
''Haka kuma, ƙungiyoyin farar hula za su iya taimakawa wajen gano wuraren da ake fargabar samun rikici tun da wuri, tare da sanar da hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakan da suka dace
Matakin sa ido kan zaɓe da tattara bayanai kan duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali ma zai taimaka wajen gano matsaloli kafin su rikide zuwa rikici.
7. Gujewa ɗaukar doka a hannu
Farfesa Abubakar Kari, ya ce idan aka samu tashin hankali yayin zaɓe ko bayan sanar da sakamako, ya kamata jama'a su guji ɗaukar fansa ko shiga cikin tarzoma.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi su bi umarnin hukumomin tsaro, su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, sannan su kai rahoton duk wani abu da zai iya jefa rayukan mutane cikin haɗari ga hukumomin da suka dace.
''Hukumomi kuma su gaggauta shiga tsakani domin kwantar da tarzoma, kare fararen hula da kuma tabbatar da cewa an gudanar da bincike mai zaman kansa kan duk wani zargi na cin zarafi'' a cewarsa.