Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda INEC za ta gudanar da zaɓen shugaban Najeriya na gwaji gabanin 2027
Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) ta fitar da bayanai kan yadda za ta gudanar da zaɓen gwaji na shugaban ƙasa a matsayin wani shiri na tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, ya sanar da cewa hukumar na shirin gudanar da zaɓen gwaji a ranar 28 ga watan Nuwamban 2026, amma mutane da dama na tambayar yadda za a gudanar da irin wannan zaɓe.
Kakakin hukumar Mohammed Kudu Haruna ya bayyana cewa zaɓen gwajin shugaban ƙasa wani atisaye ne da hukumar ke son yi domin tantance yanayin dukkan kayayyakin aiki da take amfani da su wajen gudanar da zaɓe.
Mohammed Kudu Haruna ya ce, kamar yadda sunan ya nuna, wannan gwaji ne kawai ba zaɓe na haƙiƙa ba.
Ya ce: "Ba za a gudanar da wannan gwaji da sunan wata jam'iyyar siyasa ba, kuma ba za a yi amfani da wata jam'iyya wajen gudanar da shi ba."
Ya ƙara da cewa dukkan zaɓukan da INEC ta gudanar a jihohi daban-daban tun daga shekarar 2023, zaɓukan gwaji ne, sai dai wannan na shugaban ƙasa shi ne wanda hukumar ke shirin gudanarwa a yankuna daban-daban na Najeriya.
Wace hanya INEC za ta bi wajen gudanar da zaɓen gwajin?
Mai magana da yawun hukumar INEC, Mohammed Kidu Haruna, ya yi wa BBC bayani kan yadda hukumar za ta gudanar da zaɓen gwajin, a tattauna da muka yi da shi kan shirin da kuma tambayoyi daban-daban da mutane ke yi game da shi.
Haruna ya amsa tambayoyin tare da bayyana muhimmancin wannan gwaji a tsarin zaɓe na Najeriya.
Ya yi bayanin yadda INEC za ta gudanar da zaɓen gwajin shugaban ƙasa na 2027.
Mohammed Kudu Haruna ya shaida wa BBC cewa: "A ranar zaɓen, sunayen jam'iyyun siyasar da mutane za su gani ba za su kasance sunayen jam'iyyun da suka sani ba. Sunaye ne da aka ƙirƙira musamman domin wannan zaɓen gwaji."
Ya ƙara da cewa: "A rumfar zaɓe, za a bai wa mutane takardar zaɓe wadda ke ɗauke da sunan jam'iyyar siyasar da aka yi wa rajista da ita."
Shin an taɓa gudanar da irin wannan zaɓen a baya?
Haruna ya ce tun daga shekarar 2023, dukkan zaɓukan da INEC ta gudanar, ciki har da na shugaban ƙasa, gwamnoni, 'yan majalisu da sauran zaɓuka, hukumar ta riƙa gudanar da su ne a matsayin zaɓukan gwaji.
Ya bayyana cewa wannan gwaji zai taimaka wa hukumar wajen gano wuraren da na'urorinta ko kayan aikinta ke samun matsala, domin ta gyara su kafin gudanar da babban zaɓen.
Abubuwan da za su dauki hankali a kamfe
Wasu masu lura da al'amuran siyasar kasar ta Najeriya na ganin matsalolin tsaro da tsadar rayuwa za su kasance cikin manyan batutuwan da za su mamaye yakin neman zaben na 2027.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman sake komawa mulki, sai dai rahotanni na nuna cewa farin jininsa ya ragu a tsakanin matasa, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Daga cikin manyan 'yan takarar hamayya da ake sa ran za su fafata akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na jam'iyyar ADC.
Sai kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, wanda ya yi wa jam'iyyar Labour takarar shugaban kasa a zaben 2023 Peter Obi, wanda a wannan karon zai yi wa jam'iyyar NDC takara.
Jam'iyyun hamayya dai na fuskantar rarrabuwar kai, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin zai iya yin tasiri kan karfinsu a zaben.
A wani rahoto, Bankin Duniya ya ce fiye da rabin al'ummar Najeriya a yanzu na rayuwa ne a cikin matsanancin talauci.
Masu sa ido na ganin yadda 'yan takara za su tunkari matsalolin tsaro, tattalin arziki da walwalar jama'a na daga cikin abubuwan da za su taka muhimmiyar rawa wajen rinjayar masu kada kuri'a.