Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/11/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza ya yi gargaɗin rugujewar tsagaita wuta

    Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza, wanda Amurka ke mara wa baya, ya miƙa wani rahoto mai tayar da hankali ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya gargaɗi jami’an diflomasiyya kan yanayin da ke barazana ga yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da ta shafe shekara guda tana aiki.

    A cikin sabon rahoton da aka fitar ranar Talata, kwamitin ya ce idan ba a ɗauki matakan gaggawa domin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2025 ba, to yarjejeniyar da ke tsakanin Isra’ila da Hamas na iya fuskantar barazanar rugujewa.

    Rahoton ya ce: “Babbar barazanar da ke fuskantar wannan tsari ita ce giɓi da ke tsakanin abin da aka amince da shi a yarjejeniyar da kuma abin da ke wakana a zahiri a filin daga.”

    Kwamitin ya yi nuni da cewa gazawar ɓangarorin wajen cika alƙawuran da suka ɗauka na iya ƙara dagula halin da ake ciki tare da kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

    Kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) ya ce ya samu kwafin rahoton, wanda ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin kare yarjejeniyar daga rushewa.

  2. UAE ta ce mutum 11 sun raunata bayan harin jirgin dakon mai a mashigar Hormuz

    Kamfanin man fetur na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Abu Dhabi National Oil Company (ADNOC), ya sanar a safiyar yau cewa ma’aikaci guda ɗaya a cikin ma’aikatan wani jirgin takon mai ya ɓace, yayin da wasu mutum 11 suka jikkata sakamakon harin da aka kai wa jirginsa a ranar Talata yayin da yake ratsawa ta Mashigar Hormuz.

    Kamfanin ya ce an kwashe sauran ma’aikatan jirgin zuwa wurare masu aminci.

    Da yake magana kan mutumin da ya ɓace, ADNOC ya ce: “Ana ci gaba da gudanar da aikin nema da ceto tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa.”

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ambato majiyoyin tsaron harkokin jiragen ruwa, na cewa an fitar da ma’aikatan wani jirgin daga cikin jirgin a ranar Talata bayan wani abu mai kama da makami mai linzami ya same shi.

    A ranar Talata, rundunar juyin juya halin Iran da kuma rundunar ruwan ƙasar suka wani jirgin dakon iskar gas da wasu tankokin ɗaukar man fetur guda biyu sun kama da wuta yayin da suke wucewa ta Mashigin Hormuz.

    Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan musabbabin gobarar da ta tashi a jiragen ba, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.

  3. Amurka ta rasa matsayin ƙasar da ta kawar da cutar ƙyanda

    Hukumar Pan American Health Organization (PAHO), wata hukuma ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta bayyana cewa Amurka ta rasa matsayinta na ƙasar da ta kawar da cutar kyanda, bayan shekaru biyu na karuwar masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace sakamakonta a ƙasar.

    Hukumar ta ce wani nau’in ƙwayar cutar kyanda na ci gaba da yaɗuwa a nahiyar Amurka sama da watanni 12 a jere, lamarin da ya sa ba za a ƙara ɗaukar cutar a matsayin wadda aka kawar da ita ba.

    Daraktan PAHO, Jarbas Barbosa, ya ce ƙasashen Mexico da Bolivia ma sun rasa matsayinsu na ƙasashen da suka kawar da cutar ta ƙyanda.

    Ya danganta sake ɓullar cutar da abin da ya kira “ci gaba da giɓin da ake da shi wajen yi wa al’umma rigakafi.”

    A nasa ɓangaren, Cibiyar dakile cututtuka ta Amurka (CDC) ta ce tana da ƙudirin tabbatar da cewa ƙasar ta dawo da matsayin kawar da cutar, ta hanyar faɗaɗa samun rigakafin kyanda ga jama'a.

    A bana kaɗai, Amurka ta tabbatar da samun mutane 5,400 da suka kamu da cutar kyanda da kuma mutuwar mutum 10, wanda shi ne mafi girman adadi tun daga shekarun 1990.

    Masana kiwon lafiya na gargaɗin cewa raguwar yawan mutanen da ke karɓar rigakafi na iya ƙara bai wa cututtuka masu saurin yaɗuwa kamar kyanda damar sake bazuwa a sassa daban-daban na duniya.

  4. Chadi ta ce ba za ta karɓi Larabawan Mahamid da Nijar ke shirin kora ba

    Ƙasar Chadi ta ce ba za ta karɓi dukkan Larabawan Mahamid da Nijar ke son kora kai-tsaye ba.

    Gwamnatin Chadi ta shaida wa BBC cewa ba za ta karɓi dubban Larabawan Mahamid da ke fuskantar kora daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar ba, tana mai cewa dole ne a tantance asalin ƙasar kowane mutum ɗaya bayan ɗaya.

    Ma’aikatar harkokin wajen Chadi ta ce za a tsaurara kula da iyakokinta, kuma mutanen da aka tabbatar ‘yan ƙasar Chadi ne kawai za a ba su damar komawa ƙasar.

    “Za a ba ‘yan ƙasar Chadi da aka tantance damar komawa gida, yayin da za a duba sauran shari’o’in daban-daban,” kamar yadda gwamnatin ta shaida wa BBC.

    A makon da ya gabata ne hukumomin Nijar suka bai wa al’ummar Larabawan Mahamid umarnin ficewa daga ƙasar kafin ranar 31 ga Disamba, 2026.

    Dubban Larabawan Mahamid ne ke zaune a Nijar, musamman a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    Da dama daga cikinsu sun shafe shekaru da dama a Nijar, inda iyalai na farko suka fara zuwa daga Chadi da Sudan tun a shekarun 1970.

    Hukumomin Nijar ba su bayyana inda suke sa ran al’ummar za ta nufa ba bayan ficewar.

    Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Chadi ta shaida wa BBC cewa bai kamata a ɗauki membobin al’ummar a matsayin ‘yan ƙasar Chadi kai-tsaye ba saboda asalinsu na ƙabila.

    ''Larabawan da ake magana a kansu ‘yan Nijar ne. An haife su a Nijar, sun taso kuma sun yi rayuwarsu a can, kuma tushensu yana cikin ƙasar. Kasancewarsu membobin wata al’umma ko ƙabila ba hujja ba ce da ke tabbatar da cewa su ‘yan ƙasar Chadi ne,'' a cewar gwamnatin Chadin.

  5. ADC ta nemi kotu da hana INEC sauya shugabanninta

    Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) tsagin Sanata David Mark ta nemi ƙotun ɗaukaka ƙara ta hana hukumar zaɓen ƙasar INEC sauya bayanan shugabancinta da kuma bayanan ƴan takararta na shugaban ƙasa da gwamnoni, har sai an yanke hukunci kan ƙarar da ta ɗaukaka game da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke.

    Jam’iyyar ta ce ta shigar da ƙorafi mai ƙunshe da buƙatu 17 ga kotun ɗaukaka ƙarar.

    Tsagin na David Mark na ƙalubalantar hukuncin da aka yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, wanda ta bayyana da kuskure.

    A hukuncin da ta yanken babbar kotun tarayyar da soke shugabancin tsagin David Mark da duka abubuwan da tsagin ya aiwatar ciki har da takatar Atiku.

    Sai dai a ƙarar da ta shigar gaban kotun ɗaukaka ƙarar, ADC tsagin David Mark ta ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron taƙaddamar shugabancin jam’iyyar.

    A wata sanarwa da daraktan sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Talata, jam’iyyar ta ce tana kuma ƙalubalantar wani hukunci da ya bai wa Bala Gombe damar yin gyara ga ƙarar da ya shigar tun farko, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale kan hurumin kotun na sauraron shari’ar.

    Jam’iyyar ADC ta yi gargaɗin cewa idan aka bai wa INEC damar aiwatar da hukuncin ranar 5 ga Nuwamba kafin kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan batutuwan da aka gabatar, hakan na iya raunana tasirin ƙarar da ta ɗaukaka tare da jefa ƴan takararta cikin rashin tabbas.

    Saboda haka, ta buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da cewa bayanan shugabancinta da na ƴan takararta sun ci gaba da kasancewa yadda suke a halin yanzu har sai an kammala shari’ar.

  6. Iran ta ce ta kai hari sansanin sojin Amurka a Kuwait

    Rundunar sojin Iran ta sanar da kai hari kan sansanin sojin Amurka na Ali al-Salem da ke Kuwait.

    Cikin sanarwar da sojojin Iran suka fitar da safiyar Laraba, sun ce jiragen yaƙinta marasa matuƙa sun kai hari kan dakarun Amurka da ke sansanin Ali al-Salem da ke Kuwait.

    Sanarwar Iran ɗin na zuwa ne sa'a guda bayan rundunar sojin Kuwaiti ɗin ta sanar da kunna tsarin kariyar sararin samaniyarta domin daƙile makaman da ake harbowa.

    "Domin kare Iran, ba za mu rusuna wa wata ƙasa ko wata runduna ba. Duk da haka, martaninmu ga duk wata barazana ko hari zai kasance mai tsauri, kuma ba tare da iyakancewa da wani yanki na duniya ba," a cewar sanarwar ta Iran.

    A safiyar Laraba, baya ga Kuwait, an kuma kunna ƙararrawar gargaɗin hare-haren sama a Bahrain, yayin da rahotanni suka ce an ji fashe-fashe da dama a ƙasar.

    Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (Revolutionary Guard) ta ce tsarin radar na sojojin Amurka da ke Bahrain ne ya kasance manufar waɗannan hare-haren.

  7. Putin ya yaba da ganawar da aka shirya tsakaninsa da Trump da Xi

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce yana sa ran ganawar da aka shirya yi tsakaninsa da Shugaban Amurka Donald Trump da kuma Shugaban China Xi Jinping, za ta kasance mai matukar amfani.

    Da yake jawabi a wani taron tattalin arziki na yanki da ake gudanarwa a birnin Shenzhen na ƙasar China, Mista Putin ya ce akwai matuƙar buƙatar haɗin kai a wannan lokaci da tattalin arzikin duniya ke ƙara taɓarɓarewa.

    Ganawar shugabannin za ta kasance karon farko da mutanen uku za su haɗu a wuri guda.

    Ana sa ran batutuwan da suka haɗa da yaƙin Ukraine, da rikicin Iran, da batun ƙirƙirarriyar basira ta AI da kuma makaman nukiliya za su kasance cikin abubuwan da za a tattauna.

  8. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar dai jiya, Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Muna sanar da ku cewa mun buɗe sabuwar manhajar da za su iya samun labaranmu da bidiyoyin da muke wallafawa.

    Ku shiga Play Store ko Apple Store domin sauke manhajar.