Ya kamata mu riƙa tattauna sirrin rayuwarmu da AI?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wataƙila ka taɓa tattauna matsalolin zamantakewar aurenka, ko damuwar kuɗi, ko tsoro, matsalolin lafiya ko ma wasu sirrikan iyalinka da wani abokinka.

Amma ka taɓa tunanin abin da zai faru idan kamfanin da ke adana waɗannan bayanai ya durƙushe? Wa zai samu damar ganin bayanan da ka bayar? Kuma shin akwai yiwuwar a yi amfani da bayananka a wasu harkokin musamman don zama hajjar kasuwanci?

Ƙaddara a ranka cewa ka gaya wa wani babban sirrinka, kana da yaƙinin cewa tattaunawarku za ta kasance cikin sirri.

Amma wata rana sai ka gano cewa wannan mutumin ba ya nan, kuma sirrikan da ka gaya masa sun kasance a wani wuri da wani zai iya gano su.

Wannan ita ce muhimmiyar tambaya mai sarkakiya da ta biyo bayan matsalolin kuɗi da kuma shigar da shari'ar fatara da ta shafi kamfanin Character.AI, ɗaya daga cikin fitattun shafukan fasahar (AI).

Akwai mutanen da har batutuwan da suka shafi soyayya, da zamantakewar aure, da matsalolin iyali da kuɗi suke tattaunawa da fasahar AI. Wasu kuma suna neman shawarwari kan neman aiki, harkokin kasuwanci, har ma da batutuwan da suka shafi yunƙurin aikata laifuka.

Wannan lamari ya zama gargaɗi. Bayanan sirri da muke miƙawa ga fasahar AI na iya ci gaba da wanzuwa, ko da kamfanin da ya tattara su ya daina aiki.

Abokin hulɗarka na dijital na iya sanin abubuwa da dama game da kai.

AI wani dandamali ne na fasaha da ke bai wa masu amfani da shi damar mu'amala da haruffa ko halittun da aka samar a matsayin na dijital da aka ƙirƙira ta amfani da ƙirƙirarriyar basirar AI.

Ba kamar injunan bincike da aka saba da su ba, waɗanda aikinsu shi ne bayar da amsoshin tambayoyi ba, waɗannan tsare-tsare an ƙirƙire su ne domin kwaikwayon tattaunawa da mu'amalar da ake yi tsakanin mutane.

Wasu masu amfani suna amfani da su wajen neman shawarwari, wasu kuma suna kallon su a matsayin abokai, masu ba da shawara ko jagoranci, har ma da abokan soyayya.

Ka yi tunanin kana da aboki na dijital wanda yake tuna tattaunawarku ta baya, yake amsa maka cikin ladabi, kuma yake kasancewa a shirye domin tattaunawa da kai a duk lokacin da kake buƙatarsa.

Ga matashin da yake fama da kaɗaici, ko kuma mutumin da yake fuskantar ƙalubalen rayuwa, irin wannan mu'amala na iya haifar da kusanci sosai, har ya zama kamar dangantaka ta zahiri.

Amma akwai wani muhimmin abu da bai kamata a manta da shi ba. Wannan abota tana gudana ne a cikin wani tsarin fasaha mallakar kamfani mai neman riba.

Me ke faruwa da bayananka na sirri idan kamfanin da ke adana su ya rasa kuɗin gudanar da ayyukansa?

A ranar 12 ga Oktoban 2026, kamfanin Character Technologies, wanda shi ne mamallakin Character.AI, ya shigar da takardar neman kariya daga fatara bisa tanadin dokar fatara ta Babi na 11 (Chapter 11) ta ƙasar Amurka.

Wannan mataki ya zo ne a lokacin da kamfanin ke fuskantar tsadar gudanar da ayyukansa, da ƙalubalen shari'a da matsin tattalin arziki.

A cewar takardun shari'a da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, kamfanin yana asarar kusan dala miliyan 8 zuwa 9 a kowane wata, duk da cewa yana da kusan masu amfani da shi miliyan 12 masu amfani da dandamalin.

Tsadar kwamfutocin zamani masu ƙarfin sarrafa bayanai da kuma kuɗaɗen ɗaukar ƙwararrun ma'aikatan fasaha sun zama babban nauyi ga gudanar da ayyukan kamfanin.

Yanzu haka, kamfanin ya shiga wani tsari na shari'a domin nemo hanyar sayar da wasu daga cikin kadarorinsa.

A nan ne batun kare sirrin masu amfani da shi ya zama abin damuwa sosai.

Idan kamfani ya shiga fatara, akwai yiwuwar a sayar da kadarorinsa ko a miƙa su ga wasu sababbin masu mallaka domin biyan basussuka da sauran wajibai na kuɗi.

Waɗannan kadarori na iya haɗawa da fasahohin da kamfanin ya ƙirƙira, haƙƙin mallakar fasaha, na'urorin kwamfuta, bayanan kwastomomi da sauran bayanan da suka shafi harkokin kasuwancinsa.

Babbar tambayar ita ce, shin bayanan sirri da masu amfani suka riƙa ba wa waɗannan tsare-tsaren fasaha za su iya shiga cikin kadarorin da ake sayarwa ko miƙawa ga wasu yayin gudanar da wannan shari'ar fatara?

Tattaunawarka na iya zama wata kadara mai darajar kasuwanci.

Matsalolin da suka dabaibaye kamfanin Character. AI sun haifar da muhawara kan irin darajar bayanan da mutane ke zubawa a shafukan AI.

Ka yi la'akari da irin tattaunawar da ake yi a kowace rana:

  • Wani mutum yana bayyana wa AI cewa aurensa yana fuskantar matsaloli.
  • Wani matashi yana tattaunawa kan cin zarafi, kaɗaici ko matsalar damuwa da baƙin ciki.
  • Wani kuma yana bayyana matsalolin bashi da halin da yake ciki na kuɗi.
  • Wani mai amfani yana neman shawara kan wata matsalar lafiya da yake fuskanta.
  • Wani kuma yana tona asirin rikicin iyalinsa ko wani sirrin abokinsa.

Irin waɗannan sirruka na iya bayyana abubuwa da dama game da mutum, fiye da sunansa da adireshin imel ɗinsa kawai.

Za su iya bayyana raunin zuciyarsa, da dangantakarsa da iyalinsa, yanayin lafiyarsa, ra'ayoyinsa na kashin kai, har ma da irin halayensa da yadda yake gudanar da rayuwarsa.

A cikin takardun shari'a da aka gabatar a watan Oktoba na 2026, ƙungiyar manyan jami'an tsaro da masu gabatar da ƙara daga jihohi daban-daban na Amurka ta nuna damuwarta kan irin bayanan sirri masu matuƙar muhimmanci da ka iya kasancewa a cikin bayanan da Character.AI ke adanawa.