Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴanmajalisa 12 da suka fi daɗewa a majalisar dokokin Najeriya
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ƴantakarar majalisar wakilai na jam'iyyar APC na ci gaba da martani game da sakamakon zaɓukan fitar da gwani da jam'iyyar da gudanar a ƙarshen mako.
Yayin da sakamakon ya yi wa wasu daga cikinsu daɗi, wasu kuwa kokawa suke yi game da yadda aka gudanar da zaɓukan.
Najeriya dai na amfani da tsarin majalisun dokoki guda biyu, da a turance ake kira 'Bicameral Legislature', wato majalisar dattawa mai mambobi 109 da ake zaɓo uku daga kowace jiha da ɗaya daga Abuja, babban birnin ƙasar.
Sai kuma majalisar wakilai mai mambobi 360 da ake zaɓowa gwarwadon yawan jama'ar kowacxe mazaɓar tarayya, don haka jihar da ta fi yawan al'umma ta fi yawan wakilai idan aka kwatanta da wadda ba ta yawan jama'a.
Jihohin Kano da Legas da suka fi yawan jama'a na da ƴan majalisun tarayya 24 fiye da kowace jihar, yayin da jihar Bayelsa ke da biyar a matsayin mafi ƙaranci.
Kujerar ɗan majalisa a Najeriya ba ta da wa'adi, don haka ne wasu ƴanmajalisun ke ci gaba da neman kujerun a duk lokacin da zaɓe ya zagayo, yayin da wasu kuma ke sauya majalisa daga da ta wakilai zuwa ta dattawa.
Wasu ma tun da ƙasar ta koma jamhuriya ta huɗu a 1999 suke majalisar har yanzu.
A cikin wannan muƙala mun yi duba kan wasu ƴan majalisa da suka fi daɗewa a majalisar dokokin ƙasar, waɗanda suka kwashe ƙalla shekara 19 ko fiye a zauren majalisar.
Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Ibrahim Lawan daga jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya na daga cikin mutane biyu da suka fi jimawa a majalisar dokokin Najeriya inda ya kwashe shekara 27 a majalisar zuwa yanzu.
An fara zaɓensa ne tun lokacin komawar Najeriya tafarkin dimokraɗiyya a 1999 a matsayin ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Bade/Jakusko.
Ya yi kujerar har sai biyu, zuwa 2007, inda ya tsaya takarar sanatan Yobe ta Arewa ya kuma yi nasara.
Tun 2007 ne Sanata Ahmad Lawan ke majalisar dattawan Najeriya har zuwa yau.
Ya kasance shugaban majalisar dattawan ƙasar ta tara daga 2019 zuwa 2023.
A shekarar 2023 ya tsaya takaar shugaban ƙasa, amma ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani a hannun Shugaba Tinubu.
Daga nan kuma ya koma takarar majalisar dattawan ya kuma yi nasara, inda a yanzu yake neman takarar majalisar dattawan a karo na shida.
Nicholas Mutu Ebomo
Hon. Nicholas Mutu Ebomo shi ne wanda ya fi kowane ɗan majalisa jimawa a zauren majalisar wakilan Najeriya, inda ya fara majalisar tun 1999.
Ɗanmajalisar mai wakiltar mazaɓar Bomadi/Patani daga jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya ya shafe shekara 27 a majalisar..
Kafin zamansa ɗan majalisa ya yi shugaban ƙaramar hukumar Bomadi daga 1996 zuwa 1997, daga nan kuma ya yi takarar majalisar wakilai a 1999, inda kuma har yanzu yake cikinta.
Duk da tsawon lokacin da ya kwashe a majalisar bai taɓa riƙe wani babban muƙami a majalisar ba, baya ga shugaban kwamiti.
Sai dai burinsa na zama ɗanmajalisa a karo na takwas ya gamu da cikas bayan da ya sha kaye a zaɓukan fitar da gwanin jam'iyyar na ƙarshen mako.
Ali Ndume
Kamar dai Ahmad Lawan, Sanata Ali Ndume ya fara ne a matayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Chibok/Damboa/Gwoza daga jihar Borno a 2003.
Ya maimata kujerar har sau biyu zuwa 2011, inda ya koma majalisar dattawa don wakiltar Borno ta Kudu, kujerar da yake kai har yanzu.
Sanata Ndume ya kasance ɗaya daga cikin ƴanmajalisar Najeriya da aka fi jin muryoyinsu.
A tsawon shekaru 23 da ya kwashe a majalisar dokokin Najeriya ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai a 2007 zuwa 2011.
Sannan ya riƙe muƙamin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa da babban mai tsawatarwa.
Hon. Oluwole Oke
Hon. Oluwole Oke, ya fara zuwa majalisar wakilai a 2003 domin wakiltar mazaɓar Oriade/Obokun da a yanzu aka fi sani da Ijesa ta arewa a jihar Osun.
Yanzu haka ɗan majalisar na wa'adinsa na shida a zauren majalisar, inda ya shafe shekara 23 a kan kujerar.
A iya cewa Hon. Nicolas Mutu ne kawai ya fi shi jimawa a majalisar wakilan ƙasar.
Khadija Bukar Abba
Mai ɗakin tsohon gwamnan jihar Yobe, Marigayi Bukar Abba Ibrahim ta kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka jima a majalisar wakilan Najeriya.
A shekarar 2007 ne aka fara zaɓenta domin wakilatar mazaɓar Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa a majalisar inda ta kasance a majalisar har yanzu
Bayan an sake zaɓarta a 2015, tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa ta matsayin ƙaramar ministar harkokin waje a 2016.
Ta riƙe muƙamin har zuwa farkon 2019, lokacin da ta ajiye bisa raɗin kai sannan ta sake tsayawa takarar majalisar a zaɓukan 2019 ta kuma yi nasara.
Tun daga lokacin ne kuma take zama a majalisar har yanzu, lamarin da ya sa ta zama ɗaya daga cikin matan da suka fi daɗewa a majalisar dokokin ƙasar.
Sai dai da alama wa'adinta ya zo a majalisar, bayan ta ta gaza samun takarar 2027.
Tahir Munguno
Sanata Mohammed Tahir Monguno daga jihar Borno ya kasance a majalisar dokokin Najeriya tun 2007, inda a yanzu yake cikin shekararsa ta 19 a majalisar.
Ya fara ne a majalisar wakilai, inda ya wakilci mazaɓar Marte/Nganzai/Monguno, tsawon shekara 16 a jere.
A shekarar 2023 ne ya koma wakiltar Borno a majalisar dattawan ƙasar, inda yanzu yake riƙe da muƙamin babban mai tsawatarwa na majalisar, irin muƙamin da ya riƙe a lokacin da yake majalisar wakilai.
Alhassan Ado Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa daga jihar Kano na daga cikin fitattun ƴanmajalisar da suka fi jimawa, bayan da ya kwashe shekara 19 a jere a majalisar wakilan ƙasar.
Kafin nan an taɓa zaɓarsa a jamhuriya ta uku a 1992 don wakiltar mazaɓar, lokaci yana ɗan ƙasa da shekara 30.
Hon. Doguwa ya taɓa riƙe muƙamin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan ƙasar, kuma ya taɓa neman muƙamin kakakin majalisar, amma bai samu ba.
Tijjani Abdulkadir Jobe
Kamar dai Alhassan Ado Doguwa, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe ya shafe shekara 19 a zauren majalisar wakilan Najeriya.
Hon. Jobe, wanda ke wakiltar mazaɓar Dawakin-Tofa, Tofa, da Rimingado ya fara zuwa majalisar ne a 2007.
A tsawon shekarun da ya yi a majalisar bai taɓa riƙe wani babban muƙami a zauren ba, baya ga shugaban kwamiti.
Enyinnaya Harcourt Abaribe
Sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe daga jihar Abia a yankin kudu maso gabashin Najeriya na ɗaya daga cikin sanatocin ƙasar da suka jima a majalisar.
An fara zaɓen sanatan a 2007 domin wakiltar Abia ta Kudu, daga nan kuma har yanzu yana majalisar, kuma yanzu aka shi ne sanata mafi daɗewa a majalisar.
Ya taɓa riƙe muƙamin shugaban marasa rinjaye na majalisar tsakanin 2019 zuwa 2023.
Ahmed Idris Wase
Hon. Ahmed Idris Wase na daga cikin ƴanmajalisar da suka shiga zauren a 2007, bayan da aka zaɓe shi domin wakilatar mazaɓar Wase ta Yamma daga jihar Plateau.
Tun daga lokacin ne kuma yake ci gaba da kasancewa a majalisar har zuwa yanzu bayan kwashe shekaru 19, inda yanzu yake neman wa'adi na shida bayan da ya samu tikitin takarar 2027.
A tsawon wannan lokaci ya riƙe muƙamai daban-daban a majalisar, ciki har da mataimakin kakakin majalisar a 2019 zuwa 2023, kafin nan ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban masu rinjaye tsakanin 2018 zuwa 2019.
A baya ya taɓa neman muƙamin kakakin majalisar, amma bai samu nsara ba
Muktar Aliyu Betara
Hon. Muktar Aliyu Betara da ke wakiltar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar daga jihar Borno.
Ya fara zuwa majalisar tun 2007, kujerar da ya ci gaba da riƙewa har ya zuwa yanzu.
Ɗanmajalisar ya kwashe shekara 19 yana wakiltar mazaɓarsa a majalisar wakilan ƙasar, yana kuma neman tsawaita wa'adinsa bayan samun tikitin takarar 2027.
Ɗan majalisar wanda yanzu ke kan wa'adinsa na biyar, ya nuna sha'awar zama kakakin majalisar wakilan a 2023.
Abdullahi Idris Garba
A shekarar 2007 ne Abdullahi Idris Garba, da aka fi sani Mai Solar ya fara shiga zauren majalisar wakilan Najeriya domin wakiltar mazaɓar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu daga jihar Neja.
Daga nan ne kuma aka riƙa zaɓarsa a majalisar har tsawon wa'adi na biyar da ya lashe zaɓe a 2023.
Ɗanmajalisar ya kuma samu tikitin zaɓen 2027, a wani shiri na tsawaita zamansa a a majalisar zuwa wa'adi na shida.