Rigunan ƙasashe da za su fi ƙayatarwa a Gasar Kofin Duniya ta 2026
- Marubuci, Ciaran Varley
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
- Lokacin karatu: Minti 9
Yayin da rage Gasar Kofin Duniya ta 2026 ke kara matsowa, sashen wasanni na BBC ya zaƙulo wasu daga cikin rigunan ƙwallo mafiya ƙayatarwa da ƴan wasan ƙasashen duniya za su sanya a lokacin gasar, wadda za a yi a ƙasashen Amurka da Kanada da Mexico.
Yayin da aka ƙara yawan ƙasashen da za su halarci gasar zuwa 48, za a gudanar da wasanni 104 a faɗin birane 16, da yiwuwar samun ƙarin ƙasashen da za su yi bajinta a gasar ta bana.
Tuni dai ƙasashen suka fitar da kalolin riguna biyu (gida da waje) da za su yi amfani da su a lokacin gasar.
Zaɓi kalar rigunan da suka fi burge ka cikin wannan jeri.
Algeria (waje)

Asalin hoton, @lesverts.faf
Aljeriya na amfani da korayen riguna, la'akari da tutar ƙasar.
Tawagar ƙasar da ake yi wa laƙabi da 'Desert Foxes' za ta bugar gasar ne karon farko tun 2014, lokacin da Jamus ta fitar da su a zagayen ƴan 16 ta kuma lashe kofin.
Argentina (waje)

Asalin hoton, @afaseleccion
Ƴan wasan baya za su fuskanci babar barazanar tare Messi, wanda zai sanya wata riga baƙa mai ratsin shuɗi.
Argentina mai riƙe da kofin, ita ce ta ja ragamar teburin kudancin Amurka a wasannin neman gurbin gasar.
Austria (waje)

Asalin hoton, @oefb_1904
Austria ta samu gurbin zuwa Gasar Kofin Duniya karon farko tun 1998.
Tawagar ƙasar, wadda Ralf Rangnick ke jagoranta, za ta yi amfani da rigunan waje masu matuƙar ƙayatarwa da ke nuni da al'adun ƙasar.
Belgium (waje)

Asalin hoton, @belgianreddevils
An tsara rigunan da tawagar Belgium za ta saka a wasannin waje domin tunawa da tsohon fitaccen mai zanen ƙasar, Rene Magritte.
Kamar dai ayyukan Magritte, ƙungiyar ta kai gasar ne bayan da ta burge magoya bayanta wajen casa ƙasashen Liechtenstein da Kazakhstan 6-0 kowannensu.
Brazil (gida)

Asalin hoton, @brasil
Ko akwai wanda ya lashe Gasar Kofin Duniya kamar kalolin ruwan ɗorawa da kore na Brazil?
Brazil ta kare a matsayi na biyar a kan teburin wasannin neman gurbi na yankin kudancin Amurka, inda ta yi rashin nasara shida cikin 18, amma duk da haka ƙasar da ta lashe gasar har sau biyar a baya, ta samu gurbi a gasar.
Canada (gida)

Asalin hoton, @canmnt
An tsara rigunan wasannin gida na Canada ne daga alamar ƙasar ta ganyen maple.
Ƙasar- wadda ke cikin masu ɗaukar baƙuncin gasar - ta buga gasanni biyu da suka gabata, amma kuma ba ta wuce matakin rukuni ba.
Colombia (gida)

Asalin hoton, @fcfseleccioncol
Rigunan wasannin gida da ƴan wasan Columbia za su sanya na daga cikin mafiya ƙayatarwa a gasar ta bana.
Ɗan wasan gefe na ƙungiyar Luis Diaz ne ƴan ƙasar suka sanya fata a kansa.
Croatia (gida)

Asalin hoton, @hns_cff
Rigunan Croatia masu samfurin gidan dara ja da fari, na cikin rigunan wasan gida da za su ɗauki hankalin gasar.
Duk da ƙanƙantar ƙasar, maia ywan jam'a sama da miliyan huɗu, tawagar ƙasar na da tarihi mai kyau a Gasar Kofin Duniya, inda ta ƙare a mataki na biyu a 2018, sannan suka yi na uku a 2022.
Curacao (waje)

Asalin hoton, @thebluewaveffk
Ƙasar mai yawan jama'a 156,115, wadda tsibiri ce a yankin Karebiya ta kasance ƙasa mafi ƙanƙanta da za ta halarci gasar Kofin Duniya a tarihi.
Magoya bayan ƙwallon ƙafa da dama za su yi sha'awar rigunan ƴanwasan ƙasar.
Czech Republic (waje)

Asalin hoton, @ceskarepre
Czech ta fitar da wannan kalar ne da aka ƙawata.
Jamhuriyar Czech ta samu gurbin gasar ne karon farko cikin shekara 20 bayan doke Denmark a bugun fenareti a wasan cike gurbi a watan da ya gabata.
DR Kongo (gida)

Asalin hoton, fecofadrc
DR Congo ta samu gurbin gasar ne karon farko cikin shekara 52 bayan doke Jamaica a wasan cike gurbi tsanakin nahiyoyi, bayan da Axel Tuanzebe ya ci ƙwallo a ƙarin lokaci.
Rigunan tawagar ƙasar ta cikin gida za su yi matuƙar ƙayatar da ƴan kallo.
Ecuador (gida)

Asalin hoton, @marathon_ecuador
Moises Caicedo da sauran ƴanwasan Ecuador za su fatan haskaka ƙasarsu a gasar ta bana.
Wannan ne karo na biyar da ƙasar ke buga gasar a tarihinta.
Lokacin da suka fi nuna bajinta a gasar shi ne a 2006 lokacin da suka ƙare a matakin ƴan 16.
Masar (gida)

Asalin hoton, @egyptnt
Rigunan tawagar Masar masu ratsin baki a daidai ƙirji na nuna alamar tarihin ƙasar.
Tawagar da ake yi wa lakabi da 'Pharaohs' ta lashe Gasar Kofin Afirka har sau biyar, amma sau uku kawai ta buga gasar a 1934 da 1990 da kuma 2018.
Ingila (gida)

Asalin hoton, @england
Ingila na fatan ɗaukar hankali a gasar ta bana, yayin da ta ƙawata rigunanta na wasannin gida.
Tsohon kocin tawagar Gareth Southgate ya taɓa kai ƙasar wasan kusa da ƙarshe a 2018, sannan ta kai zagayen kwata fayinal a gasar 2022, baya ga zuwa wasan ƙarshe a gasar Euro sau biyu a jere, 2021 da 2024.
Tuchel na fatan a wannan shekara ƙasar ta lashe gasar, domin kafa tarihi
Faransa (gida)

Asalin hoton, @equipedefrance
Faransa na cikin tawagogin da rigunansu za su ɗauki hankali a gasar ta bana.
Tawagar da ake yi wa laƙabi da Les Bleus ta kasace ta biyu a gasar da ta gabata da aka buga a Qatar shekara huɗu da suka wuce, kuma ana yi musu kallon waɗanda za su iya lashe gasar bana.
Jamus (gida)

Asalin hoton, @dfb_team
Rigunan tawagar Jamus na gasar 2026 su ne na ƙarshe da kamfanin Adidas zai buga wa tawagar ƙasar.
Rigunan sun so yin kama da waɗanda ƙasar ta sanya a shekarar 1990 da 2014 lokacin da ƙasar ta lashe kofin.
Ivory Coast (waje)

Asalin hoton, @fif.ci
Riguna ne masu kyau da sheƙi a lokaci guda, masu launin kore, fari da ruwan lemo.
Ivory Coast ta buga Gasannin Kofin Duniya uku da suka gabata - 2006 da 2010 da kuma 2014, amma ba su taɓa wuce matakin rukuni ba.
Japan (away)

Asalin hoton, @japanfootballassociation
Japan za ta je Gasar Kofin Duniya bayan da ta doke Ingila a wasan sada zumunci a Wembley.
Rigunan ƙasar masu launi da yawa na daga cikin masu ɗaukar hanakali.
Mexico (gida)

Asalin hoton, @miseleccionmx
Riguna ne da ke kan gaba a mafiya kyau a gasar bana, wanda suka taɓa sanya irinsu a Gasar Kofin Duniya da aka buga a Faransa a 1978.
Karo na ƙarshe da ƙasar ta ɗauki baƙuncin Gasar Kofin Duniya a 1986 sun kai matakin kwata fayinal.
Norway (gida)

Asalin hoton, @herrelandslaget
Ƙasar Norway ta samu nasara komawa gasar karon farko cikin shekara 28.
A Gasar da aka buga a Faransa a 1998, ta doka Brazil da 2-1 a wasannin cikin rukuni kafin Italiya ta fitar da ita a zagayen ƴan 16.
Tawagar ƙasar a wannan gasa na cike da manyan ƴanwasa irinsu Martin Odegaard da Erling Haaland.
Portugal (gida)

Asalin hoton, @portugal
Portugal za ta ɗauki hankali da waɗanna riguna d aak tsara da siffar tekun Atalantika da ya yi iyaka da ƙasar.
Tawadar ƙasar da Roberto Martinez ke jagoranta ta nuna bajinta awasannin neman gurbi bayan doke Armeniya ta ci 9-1.
Qatar (gida)

Asalin hoton, @qfa
Bayan rashin nasara a gasar 2022, Qatara na fatan kafa tarihi a wannan gasa.
Ƙasar ta buga riguna masu ɗauke da kalar tutar ƙasar da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Saudi Arabia (gida)

Asalin hoton, @saudint
Saudi Arabia ta girgiza duniyar ƙwallon ƙafa a lokacin da ta doke Argentina da ci biyu da ɗaya a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.
Sai dai ƙasar ta ba mutane mamaki da ta sallami kocinta Herve Renard kimanin wata biyu kafin fara gasar ta bana.
Rigar ƴanwasan tawagar ta bana tana da jan hankali, inda aka ratsa kalar zinare da launin purple a koren da aka saba ganinsu da shi.
Afirka ta Kudu (waje)

Asalin hoton, @bafanabafanaofficial
Rigar Afirka ta Kudu ta wasannin waje ta zo da sabon salo a gasar da aka yi ta shekarar 2010.
Ƙasar ta kuma ba duniya mamaki da doke Faransa da ci biyu da ɗaya.
Spain (waje)

Asalin hoton, @sefutbol
Rigar Spain ta wasannin waje tana ɗauke da wani zane na musamman da aka tsakuro daga rubutun zamanin baya.
Tawagar ƙasar na cikin ƙasashen da ake sa ran za su iya lashe gasar ta cin kofin duniyar ta bana.
Sweden (gida)

Asalin hoton, @swemnt
Sweden na da tarihin nuna bajinta a gasar cin kofin duniya, inda ta zo ta biyu a gasar shekarar 1958, sannan ta zo ta uku a shekarar 1950 da 1944.
Uruguay (gida)

Asalin hoton, @aufoficial
Ƙasar Uruguay da ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyu za ta kasance cikin ƴan ƙwalisa a gasar ta bana.
Duk da cewa zaratan ƴan wasan ƙasar irin su Luis Suarez da Edinson Cavani sun yi ritaya daga taka leda, Federico Valverde da sauran su za su ƙuduri aniyar nuna bajinta.
Amurka (gida)

Asalin hoton, @usmnt
Kasancewar tana cikin ƙasashe masu masaukin baƙi, Amurka za ta so ta fito fes a gasar.
Mai horasa da ƴanwasa Mauricio Pochettino zai jagoranci tawagar ƙasar, kuma sukunin D tare da Paraguay da Australia da Turkiyya.











