Mutane 5 da ke wakiltar Amurka da Iran a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran

Asalin hoton, others
Yayin da wakilan Amurka da Iran suka isa birnin Islamabad domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka, hankula sun koma kan su wane ne wakilan ɓangarorin biyu.
A irin wannan tattaunawa dai kowace ƙasa kan aika da ƙwararrun mutane ta fuskar diplomasiyya domin kare muradunsu.
Iran dai ta gabatar da sharuɗaɗɗa 10 da take son a amince da su domin kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Amurka ta gabatar da 15.
Duka ƙasashen jimilla sun tura wakilai biyar da za su yi wannan tattaunawa bisa jagorancin Pakistan domin samar da yarjejeniyar zaman lafiyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin.
Suwa ne wakilan ɓangarorin biyu?
Tawagar Amurka
JD Vance: Washinton ta aike da wakilai ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar.
Ana sa ran Vance zai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar.
A baya Mista Vance ya sha bayyana adawarsa da yaƙe-yaƙe, ya kuma nuna rashin goyon bayan ƙazancewar yaƙin Iran.
Steve Witkoff: Sakataren harkokin wajen ƙasar, Steve Witkoff, wanda amini ne ga Shugaba Trump kuma ƙwararren jami'in diplomasiyya.
Ya taka muhimmiyar rawa a manyan al'amuran duniya ciki har da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza da na Ukraine.
Jered Kushner: Suruki ne ga shugaba Trump, shi ma ya ƙware a fannin diplomasiyya.
Ya taka rawar gani a diplomasiyyar yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da yarjejeniyar Abraham Accord.
Kusher na gudanar da harkokinsa tsakanin kasuwanci da siyasar duniya.
Tawagar Iran
Abbas Araghchi: Wakilan Iran na ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, wanda ƙwararren jami'in diplomasiiya ne.
Yana da gogewar kusan shekara 40 a fannin diplomasiyya, wanda ya sha shiga manyan tattaunawa musamman da Amurka kan shirin nukiliyar Iran.
Mohammad Bagher Ghalibaf: Kakakin majalisar dokokin Iran, wanda ya jagorancin rundunonin ƙasar da dama a matsayin kwamanda a baya.
Ya taɓa riƙe muƙamin magajin garin birnin Tehran.
Ghalibaf ya kasance kan gaba a shafukan sada zumunta wajen mayar wa Amurka martani.
Waɗannan mutanen biyar za su yi amfani da gogewarsu ta aikin soji da siyasar duniya da kasuwanci da diplomasiyya wajen kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe kusan kwana 40 ana gwabzawa.
Sakamakon tattaunawar da za a yi a Pakistan shi ne zai tantance makomar alaƙar Amurka da Iran.










