KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ƙungiyar Kurɗawa a Iraƙi ta zargi Iran da kashe mata mayaƙa tara

    Wata ƙungiyar Kurɗawa a Iraƙi mai adawa da Iran ta ce wani harin jirgi maras matuƙi da roka ya kashe mambobinta tara.

    Ƙungiyar Komola na da mazauni a kusa da arewacin Iraƙi kusa da birnin Sulaymaniyah.

    Mai magana da yawun ƙungiyar ya ce an kai harin ne da sanyin safiyar yau Juma'a kuma gwamnatin Iran ce ke da alhakin kai harin.

    A baya dai Iran ta sha kai hare-hare kan ƙungiyoyin da take adawa da su a Iraƙi sai dai kashe mutanen tara ka iya zama silar da rikicin zai iya caɓewa tsakanin ɓangarorin.

  2. Hare-haren Iran sun lalata tashar lantarkin Kuwait

    ....

    Asalin hoton, ....

    Ƙasar Kuwait ta ce hare-hare ta sama da Iran ta kai ƙasar ya lalata tashar samar da wutar lantari da kuma cibiyoyin ruwa a ƙasar.

    Tehran ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin martanin munanan hare-haren da Amurka ta kai kan gadoji biyar da hanyoyin sufurin jiragen ƙasa da kuma filin jirgi cikin dare.

    Iran ta kuma ce ta kai hare-haren kan sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Kuwait da Bahrain da Jordan da kuma Siriya.

    Idan har hakan ta tabbata, zai zama karon farko da Iran ta kai babban hari Siriya ƙarƙashin mulkin shugaba Ahmed al-Sharaa, wanda ke ƙoƙarin ganin Siriya ba ta shiga cikin rikicin ba.

  3. An sanya wa sabon babban titin Legas zuwa Calabar sunan Tinubu

    Babban titi

    Asalin hoton, Dr Dípò Awójídé/X

    Gwamnatin Najeriya ta sanya wa babban titin gaɓar teku - da ya tashi daga Legas zuwa Calaba - sunan shugabana ƙasar Bola Tinubu.

    Ministan ayyuka na ƙasar, David Umahi ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne domin nuna yabo ga hangan nesan shugaban ƙasar game da aiki.

    Ya ce ma'aikatar ayyuka ta ƙasar ce ta yanke shawarar sanya wa titin sunan shugaban ƙasar, bayan tuntuɓar jagororin ma'aikatar.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, David Umahi ya ce Shugaba Tinubu ya amince da faɗaɗa aikin titin da kilomita 400.

    Babban titin wanda ya ratsa jihohin Najeriya aƙalla tara ke bakin gaɓar ruwa zai an tsara zai laƙume kuɗi naira tiriliyan 15.

    Titin mai tsawon kilomita fiye da 700 zai tashi daga Legas da kudu maso yammcin ƙasar, zuwa Kalaba da ke kudu maso kudancin ƙasar.

  4. Iran ta gargaɗi ƙasashen Gulf kan bai wa Amurka damar kai mata har

    Abbas Araghchi

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta gargaɗi ƙasashen yankin Gulf kada su bari Amurka ta yi amfani da yankunansu ko sararin samaniyarsu ko kuma gaɓoɓin ruwansu wajen kai hari cikin ƙasar.

    Tehran ta ce irin wannan mataki zai janyo mummunan sakamako ga waɗannan ƙasashe.

    Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Saleh Jokar, ya ce idan Amurka ta yi amfani da yankunan waɗannan ƙasashe wajen kai hari kan Iran, to za su fuskanci mummunar asara.

    A wani ɓangaren kuma, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce sake kakaba takunkumi kan harkokin sufurin ruwa zai zama saɓa wa yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Tehran da Washington.

    Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kuma zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi, tana mai nuni da hare-haren da aka kai wa muhimman cibiyoyin fararen hula da kuma wuraren samar da ayyukan jama’a a matsayin misalai.

    Iran ta ce wuraren da aka kai wa hari sun haɗa da cibiyar lafiya ta rundunar soji ta Brigade na 388 da cibiyar ajiye kayayyaki da Hoveizeh da kuma wasu wurare daban.

    Tehran ta ce wannan ne karo na uku cikin shekara guda da Amurka ta kai mata hari alhali ana tsakan da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu.

  5. INEC za ta shirya zaɓen shugaban ƙasa na gwaji

    Shugaban INEC

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya ta ce tana duba yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasar na gwaji, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

    Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar hukumar zaɓen da ke Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

    Farfesa Amupitan ya ce hukumar na wannan shiri ne domin tabbatar da sahihanci da ingancin na'urorin zaɓen, la'akari da ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan zaɓukan 2023.

    Ya ƙara da cewa INEC na duba yiwuwar gwada kayayyakin hukumar zaɓen gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe.

    “Muna duba yiwuwar gwada duka kayyaki da na'urorin zaɓenmu, gabanin babban zaɓen da ke tafe, da kuma yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasa na gwaji, domin gwaja ingancin kayayyaki da na'urorin namu,'' in ji shi Farfesa Amupitan.

    Ya ƙara da cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen hukumar na inganta tsarin fasahar hukumar ciki har da tsarin tantance masu zaɓe da hanyar na'ura da amfani da shafin IRev wajen tura sakamakon zaɓe, da tsarin tsaron shafin.

  6. Hukumar tace fina-finai da hisbar Kano sun samu saɓani kan masu dawulodin

    Kano

    Asalin hoton, Abba El-Mustapha/FB

    A jihar Kano, takaddama ta kaure tsakanin hukumar Hisba da kuma hukumar Tace Fina-Finai game da sana'ar tura fina-finai wato downloading.

    Tun da farko dai hukumar Hisbah ce ta fara sanar da haramta sana'ar bisa zargin cewa ana amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.

    To sai dai hukumar Tace Fina-Finai ta yi fatali da wannan matakin tana mai cewa sana'ar halastacciya ce kuma ita ce ke da ikon yi ko hana sana'ar.

    ''Wannan mataki abu da ya kamata a ce mu da su mun zauna mun tattauna a kan makomar yin haka kasancewar mu ke da hurumi da doka ta ba mu na kula da masu wannan sana'a'', a cewar Abdullahi Sani Sulaiman kakakin hukumar.

    ''Akwai wani tsari da muka yi musu na rigima da suke samu tsakaninsu da masu shirya fina-finai da cewa ba za su sake ɗaukar fim ba, sai da sahalewar masu fina- finai,'' in ji shi.

    A nata ɓangare, hukumar Hisba ta ce ta ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-ƙorafe da dama da hukumar ta samu daga al'umma.

    Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen ya shaida wa BBC cewa akwai masu fakewa da sana'ar suna tura wa jama'a hotuna da bidiyon tsiraici, lamarin da ya ce na matuƙar gurɓata tarbiya.

    ''Ana samun wasu ɓata-gari masu sana'ar dowulodin da ke tura wasu fina finai na batsa'', in ji shi.

  7. Iran ta yi iƙirarin lalata wasu cibiyoyin Amurka a yankin Gulf

    Ɓarna

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun juyin juya halin Iran sun bayyana cewa sun lalata na;urorin sadarwar Amurka biyu a ƙasar Oman.

    Cikin wata sanarwar da rundunra ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce rundunar sojin ruwanta ta lalata na'urar da ke kula da sadarwar jirage a tashar ruwa ta Salalah da kuma wadda ke tashar Ghanem duka a Oman da safiyar yau Juma'a.

    Sanarwar ta jaddada cewa Iran za ta ci gaba da ɗaukar matakan martani, kuma mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon dakarun sojin ruwa na rundunar juyin juya halin.

    IRGC ta kuma ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al-Tanf da ke kudancin Siriya.

    Rundunar ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga kisan sojojinta a harin Iranshahr.

    ''Dakarun sojin sama na rundunar IRGC sun kai hari kan sansanin sojojin Amurka na musamman a Al-Tanf, da na'urorin sadarwar jirage da kan jirage na musamman masu saukar ungulu da wasu sojojin na Amurka'', in ji sanarwar ta IRGC.

    To sai dai kakakin rundunar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM ya shaida wa kafar yaɗa labarai na Al Jazeera cewa hare-haren an Iran kan ƙasashen yankin Gulf ''ba su haifar da wani lahani da ayyukan sojojin ba''.

  8. Amurka ta ce ta kai hari kan ɗaya daga cikin tasoshin ruwan Iran

    Tashar ruwa

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya bayar da rahoton cewa Amurka ta kai hare-hare kan na'urar lura da zirga-zirgar jirage a tashar ruwa ta Chabahar har sau uku da safiyar yau Juma'a.

    Rahoton ya ce hare-haren sun lalata ilahirin na'urar, amma ba a samu wata ɓarna ga jiragen ruwan ko sauran kayyakin da ke tashar ba

    Majiyoyi sun ce ƙarar manyan abubuwan fashewa ne suka lalata na'urar.

    IRNA ya ce tawagogin masana da masu bincike na auna yanayin, da nufin gyara na'urar domin ci gaba da gudanar da ayyuka a tashar.

    Babu dai labarin jikkata ko rasa rai a lokacin harin.

  9. Trump ya zargi China ta yin katsalandan a zaɓen Amurka na 2020

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi China da yin katsalandan mai yawa a zaɓen shekarar 2020, tare da iƙirarin cewa hukumomin leƙen asirin Amurka sun yi ƙoƙarin ɓoye abin da ya bayyana a matsayin yunƙurin Beijing na cutar da shi a siyasance a zaɓen wancan lokaci.

    A wani jawabi da ya yi wa al'ummar ƙasar, Mista Trump ɗin, wanda ya sha kaye a zaɓen a hannun Joe Biden, ya sake nanata zarginsa cewa an tafka maguɗi a zaɓen domin hana shi samun nasara.

    Gwamnatin China ta mayar da martani a sanarwar da ofishin jakadancinta da ke birnin Washington ya fitar tana mai cewa babu wani kutsen da ta yi a harkar zaɓen Amurka.

    Haka kuma bincike da shari'o'i da dama da aka gudanar a matakai daban-daban sun kasa gano wata hujja da ke tabbatar da zargin maguɗi a zaɓen.

  10. An ci gaba da musayar wuta tsakanin Iran da Amurka

    hari

    Asalin hoton, Reuters

    An kwana na shida a jere na musayar wuta tsakanin Amurka d Iran bayan karyewar yarjejeniyar tsagaita wuta da ɓangarorin biyu suka cimma.

    Amurka na kai hare-hare a wasu yankuna na ƙasar Iran, yayin da a nata ɓangare, ita ma Iran ɗin ke ci gaba da mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan wasu cibiyoyin Amurka a yankin Gulf.

    Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ce an ji fashe-fashe a birnin Bushehr, inda a nan ne tashar nukiliya ƙasar take.

    Haka kuma suna bayar da rahoton cewa mutum uku sun mutu, yayin da wasu tara suka jikkata, sakamakon hare-haren da aka kai kan wasu gadoji a wani gari da ke kusa da mashigin ruwan Hormuz.

    A farkon makon da muke ciki ne shugaba Trump ya yi barazanar kai wa gadoji da tashoshin wutar lantarkin ƙasar hari idan Iran ta ƙi ba da ikon Mashigin ruwa na Hormuz.

    Rundunar sojin Kuwait ta ce ta girke na'urar kare sararin samaniyarta domin tunkarar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ke kaiwa.

  11. Assalamu alaikum

    Mabiya shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yui mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.