Me ya sa INEC ta ƙi sanya Aminu Abdulsalam a jerin ƴantakarar gwamnan Kano?

Asalin hoton, Aminu Abdussalam Gwarzo Facebook
Ana ci gaba da tafka muhawara kan rashin ganin sunan ɗan takarar jam'iyyar NDC a zaɓen gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo a cikin jerin ‘yan takara da hukumar INEC ta fitar bayan korafin da jam’iyyu suka gabatar.
Sai dai a daidai lokacin da wasu ke bayyana cewa an cire ɗan takarar baki ɗaya, ita Kwankwasiyya murna take yi cewa INEC ta karɓi kokenta ta hanyar amincewa da jam'iyyar NDC ta shiga zaɓen.
Kwankwasiyya ta bayyana matuƙar farin cikinta ne bayan da Hukumar INEC ta sanya sunan jam'iyyar a cikin jerin ƴan takarar zaɓen 2027 da ta fitar na ƙarshe a ranar Juma'a.
Sai dai duk da cewa an sanya sunan jam'iyyar a cikin jerin, INEC ba ta bayyana sunan ɗan takarar gwamna na jam'iyyar, Kwamared Aminu Abdulsalam ba, inda ta rubuta cewa akwai batun umarnin kotu da ke da alaƙa da takarar.
Lamarin ya zo ne bayan cece-ku-ce da suka biyo bayan fitar da jerin sunayen farko, lokacin da ba a ga sunan Farfesa Isa Ali Pantami na PDP a Gombe da kuma Aminu Abdulsalam na NDC a Kano ba.
Rashin sunayen ya jawo martani daga magoya bayan jam'iyyun da abin ya shafa, lamarin da ya sa INEC ta bayyana cewa za ta sake nazarin korafe-korafen da aka gabatar mata.
Babbar nasara ce gare mu – NDC
A makonnin baya, wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa hukumar ta kammala aikin nazarin nata, inda wasu rahotanni suka ce za a mayar da sunayen Pantami da Aminu Abdulsalam, yayin da wasu rahotannin suka nuna cewa Pantami ne kaɗai aka amince da mayar da sunansa.
A sabon jerin da INEC ta fitar, an dawo da sunan Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe, amma a Kano, an rubuta cewa akwai batun umarnin kotu kan takarar Aminu Abdulsalam, amma hukumar ta rubuta sunan jam'iyyar NDC, wadda yake takara a cikinta.
Da yake magana da BBC, sakataren ƙungiyar Kwankwasiyya kuma ɗan takarar kujerar majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukmar birni a jam'iyyar NDC a Kano, Dokta Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata, ya ce matakin da INEC ta ɗauka babbar nasara ce ga jam'iyyar.
"Wannan babbar nasara ce a gare mu. Da farko ma babu sunan NDC a cikin jerin, sannan babu sunan ɗan takararmu na gwamna. Bayan mun gabatar da ƙorafi da hujjoji, INEC ta duba ta gano babu wani dalili da zai hana saka jam'iyyarmu."
Ya ce daga cikin hujjojin da suka gabatar akwai rajistar Aminu Abdulsalam da aka yi kafin ranar 10 ga Yuni, tare da takardun shaidar da ya ce suna da su, wadanda INEC ta karɓa.
"Babbar nasarar ita ce INEC ta tabbatar da cewa za mu shiga zaɓe."
Me ya sa babu sunan kwamared a jerin yan takara?
Kofar Mata ya shaida wa BBC cewa a wajen INEC ne suka samu bayanan da ke cewa akwai umarnin kotu da ya hana a sanya sunan Kwamared Gwarzo cikin jerin ‘yan takarar gwamna, yayin da ita kuma jam’iyyar ba ta da wannan masaniya tun farko.
"Abin da ake cewa shi ne akwai umarnin kotu da ake jira, ba hukuncin ƙarshe ba ne. Wasu ne suka je suka buƙaci kotu ta hana INEC saka sunan ɗan takararmu. Mu ma ba mu san da ƙarar ba, domin a ɓoye aka shigar da ita," in ji Kofar Mata.
Ya ƙara da cewa lauyoyin jam'iyyar za su garzaya kotu domin neman warware lamarin.
"Ina tabbatar maka cewa za a iya warware wannan umarnin idan aka saurari dukkan ɓangarori. Ranar Litinin lauyoyinmu za su je kotu domin dubawa tare da gabatar da hujjojin kare haƙƙinmu," a cewarsa.
Su wane ne suka shigar da kara a kotu?
Yayin da aka tambaye shi ko suna zargin wata jam'iyya da hannu a rikicin, Dokta Yusuf ya ce ba su da wata hujjar zargi kai tsaye, amma ya ce siyasa ba ta rasa dabaru da ƙulle-ƙulle.
"Ba ma zargi kai tsaye, amma siyasa ba ta rasa ƙulle-ƙulle. Wataƙila wasu ne suka haɗa baki. Amma APC ba ta so ta shiga zaɓe da kowa a Kano ba. Abin da ya sa na faɗa haka shi ne za ka ga suna murna da zarar an ce babu sunan ɗan takararmu."
Sai dai Dr Ƙofar Mata ya ce yanzu murnar ta koma cikin "domin a yanzu an tabbatar cewa NDC za ta shiga zaɓe."
Jigon na NDC ya kuma yi iƙirarin cewa Kwankwasiyya na da babban tasiri a Kano, yana mai cewa magoya bayan tafiyar za su goyi bayan jam'iyyar a zaɓen 2027.
"Mutanen Kano sun san tsarin Kwankwasiyya kuma suna binsa. Tunda Kwankwasiyya tana cikin NDC, muna da yaƙinin cewa mutane za su zaɓe ta ko da lokacin ba a kammala shari'ar ba."

























