Idan Amurka ta sake taɓa mu, za mu iya kai hari a duk inda take da sojoji - Iran

Asalin hoton, isna
Mohammad Akraminia, kakakin rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya ce idan aka sake samun wani yaƙi, "rikicin ba zai tsaya a yankin Yammacin Asiya kaɗai ba."
A cewarsa, "wuraren da Amurka ke da cibiyoyi, kayan aiki, sojoji da muradunta, a duk inda za a iya kai musu hari, na iya zama abin hari."
Da yake magana kan “ƙarfafa shirin aiki da kuma sabunta jerin manufofin da aka tanada domin kai hare-hare,” Mista Akraminia ya ce duk wa yaƙin da zai iya tasowa nan gaba na iya kasancewa "mai tsawo fiye da yaƙin da ya gabata."
Kakakin rundunar sojin ya kuma ce: "Tun a baya aka fara sauya akidar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga ta kariya kawai zuwa wadda ta haɗa da kai farmaki, kuma hakan ya bayyana a aikace a yaƙin baya-bayan nan."
Shafin yanar gizon hukuma na Mojtaba Khamenei ya ruwaito jiya cewa, a wani taro da kwamandojin rundunonin sojin Iran, an umarce su da su mayar da martani "cikin gaggawa kuma ba tare da wani iyakar yanki ba" ga duk wata barazana daga abokan gaba.
An kuma ruwaito Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana cewa, idan aka sake kai wa Iran wani hari na soja ko kuma abin da ya bayyana a matsayin "ta'addanci", Iran ce za ta ƙayyade lokacin da kuma yanayin da rikicin zai ƙare.




















