Yadda za ku gane warin jikinku na damun na kusa da ku

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

"Wani lokaci hancinka kan saɓa da warin jikinka, har ba ka iya lura da shi ko da yana wari. Amma akwai wasu alamomi da hanyoyi masu sauƙi da za su taimaka maka ka gane ko warin jikinka yana damun wasu mutane."

Kowane mutum kan yi fama da warin jiki a wasu lokuta. Wannan na faruwa ne lokacin da ƙwayoyin cuta ke ƙaruwa a cikin zufar da jiki ke samarwa.

Warin jiki matsala ce da aka sani wadda ke iya shafar jin daɗin rayuwar mutum. Masana sun bayyana cewa abin ba zufar kanta ba ne, sai dai yawan ƙwayoyin cuta da suke girma a cikin zufar.

Akwai hanyoyin da za a rage ko a shawo kan wannan matsala. Ɗaya daga cikin hanyoyin ita ce ka goga yatsun hannunka masu tsabta a fatar kanka ko ƙarƙashin hammatarka, sannan ka shaki ƙamshin yatsun da kyau domin ka gano ko akwai wari.

Saƙon da jiki ke aikewa

Warin jiki na iya sauyawa, kuma abubuwa kamar sinadaran hormones na jiki, irin abincin da mutum yake ci, kamuwa da cututtuka, magungunan da ake sha, ko wasu cututtuka da ke ɓoye kamar ciwon sukari na iya shafar sa.

Ana iya rage ko magance warin jiki ta hanyar amfani da magungunan hana zufa masu ƙarfi da kuma wasu magunguna da likitoci ke bayarwa idan akwai buƙata.

Mene ne warin jiki?

Warin jiki shi ne warin da ke fitowa idan zufa ta haɗu da ƙwayoyin cuta da ke zaune a kan fata. Zufa da kanta ba ta da wari, amma idan ta haɗu da bakteriya, sai a fara samun wari.

Warin jiki yana samuwa ne lokacin da bakteriya suke karya da sarrafa sunadaran proteins da ke cikin zufa domin samun abinci. A yayin wannan tsari ne ake samar da sinadaran da ke haifar da wari.

Saboda haka, ba zufa ce kai tsaye ke haifar da warin jiki ba, sai dai bakteriya da ke rayuwa a wuraren da zufa take taruwa. Jikin mutum kan sauya wasu sinadarai zuwa wasu sindaran asid masu haifar da wari. Wannan ne ya sa mutanen da ke yawan zufa suka fi fuskantar matsalar warin jiki.

Manyan ƙwayoyin halittar jikin ɗan adam da ke da alaƙa da samuwar warin jiki sun fi yawa a ƙarƙashin hammata da kuma wasu sassan jiki masu laushi.

Akwai wurare da dama a jikin mutum da iska ba ta shiga sosai, musamman wurare masu laushi ko masu ɓoyuwa. A irin waɗannan wurare ne zufa kan taru, wanda ke ba bakteriya damar hayayyafa da kuma samar da warin jiki.

Ƙananan halittu da ke samar da zufa

Waɗannan suna fitar da zufa kai tsaye zuwa saman fata. Lokacin da zufar ta bushe, tana taimakawa wajen daidaita zafin jiki da sanyaya jiki. Waɗannan halittu ba sa samar da warin jiki kai tsaye.

Idan zafin jiki ya ƙaru sakamakon motsa jiki ko yanayin zafi mai tsanani, zufa kan fito zuwa saman fata sannan ta ƙafe. Wannan ƙafewar zufa ne ke taimakawa wajen sanyaya jiki.

Ana samun halittun ne a kusan dukkan sassan jikin mutum, har da:

  • Tafin hannu
  • Tafin ƙafa
  • Goshi
  • Hannaye da ƙafafu
  • Sauran mafi yawan sassan fata

Zufar da ke sa warin jiki

Halittun da ke samar da zufa na buɗewa ne a wuraren da gashi ke fitowa -ƙananan ramuka ne ko bututu a cikin fata da ke riƙe da gashi. Ana samun waɗannan halittu a:

  • Ƙarƙashin hammata
  • Al'aura da wuraren da ke kewaye da su

Suna samar da wani nau'in zufa wanda kan iya haifar da wari idan ya haɗu da ƙwayoyin cuta da ke kan fata. Waɗannan halittu suna fara aiki sosai ne bayan mutum ya balaga, shi ya sa ƙananan yara ba sa fuskantar warin jiki kamar manya.

Yin zufa abu ne na dabi'a, amma wasu abubuwa kamar:

  • Irin abincin da mutum yake ci
  • Rashin tsaftar jiki
  • Gado

Na iya sa mutum ya fi yin zufa ko ya fi samun warin jiki.

Idan ka lura cewa yawan zufarka ko warin jikinka ya sauya ba zato ba tsammani, wannan na iya zama alamar wata matsalar lafiya. A irin wannan yanayi, yana da kyau a tuntubi likita domin a gano musabbabin matsalar.

Mutanen da suka fi samun warin jiki

..

Asalin hoton, Getty Images

Maza sun fi saurin samun warin jiki saboda halittarsu da ke samar da zufa masu haifar da warin jiki (apocrine glands) sun fi aiki sosai, sannan kuma suna da gashi fiye da mata.

Kwayoyin halittar na fara aiki ne lokacin da mutum ya kai ga balaga. Saboda haka, warin jiki kan fara bayyana ne a lokacin balaga.

Me ke janyo warin jiki?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yawancin warin jiki kan fara bayyana ne lokacin balaga, domin a wannan lokaci ƙwayoyin halittar zufa masu haifar da warin jiki (apocrine glands) suna ƙara aiki sosai, kuma sauye-sauyen sinadaran jiki suna ƙaruwa.

Mutanen da suke da ƙiba da kuma waɗanda ke fama da wasu matsalolin lafiya kamar ciwon sukari suna iya fuskantar warin jiki fiye da sauran mutane.

Warin jiki yana samuwa ne lokacin da ƙwayoyin cuta da ke kan fata suka haɗu da zufa. Fatar jikinmu tana da bakteriya a dabi'ance. Lokacin da muke yin zufa, ruwa, gishiri da kitse da ke cikin zufar suna haɗuwa da waɗannan ƙwayoyin cuta, wanda ke haifar da wari.

Wannan warin na iya zama mara daɗi, mai sauƙin jurewa, ko kuma ba a ji wari sosai ba. Abubuwa kamar irin abincin da mutum yake ci, sauye-sauyen sinadaran jiki da kuma wasu magunguna na iya canza warin jiki.

Akwai wata matsala ta lafiya da ake kira "hyperhidrosis", wadda ke sa mutum yin zufa fiye da kima. Mutanen da ke fama da wannan matsala kan fi samun warin jiki saboda yawan zufa. A mafi yawan lokuta, manyan ƙwayoyin da ke samar da zufa ne ke haddasa yawan zufa a tafukan hannu da tafukan ƙafa.

Duk lokacin da mutum ya yi zufa, akwai yiwuwar a samu wani nau'in wari. Sai dai wasu mutane sun fi sauran saurin jin ƙamshi ko wari mai ƙarfi.

Sauran abubuwan da kan shafi warin jiki sun haɗa da:

  • Motsa jiki
  • Damuwa ko tashin hankali
  • Tsananin zafi
  • Kiba
  • Halayen gado daga iyaye

A taƙaice, warin jiki ba zufa kaɗai ke haddasawa ba; haɗuwar zufa da ƙwayoyin cuta a kan fata, tare da abubuwa kamar sinadarin jiki, abinci, lafiya da yanayin gado, su ne manyan abubuwan da ke jawo shi.

Me ya sa zufata take wari?

Akwai dalilai da dama da kan sa zufarka ta yi wari. Misali, wasu magunguna, bitamin ko irin abincin da mutum yake ci na iya canza warin zufa.

Ka tuna cewa ba zufa ce da kanta ke wari ba. Warin yana samuwa ne lokacin da ƙwayoyin cuta da ke kan fata suka haɗu da zufa.

Akwai wasu cututtuka da yanayin lafiya da suke da alaƙa da canjin warin jiki na yau da kullum. Waɗannan sun haɗa da:

  • Ciwon sukari
  • Tsayawar al'ada ga mata
  • Aikin halittar thyroid fiye da kima
  • Cututtukan hanta
  • Cututtukan ƙoda
  • Wasu cututtuka masu yaɗuwa

Idan kana da ciwon sukari, canjin warin jikinka na iya zama ɗaya daga cikin alamomin cutar. Wasu masu ciwon sukari na iya fitar da wani wari mai kama da 'ya'yan itace masu zaƙi sakamakon sauye-sauyen sinadaran da ke cikin jikinsu.

Shin ana iya hana warin jiki?

"Mutane su kan fi lura da wari da ke fitowa daga sassan jiki da tufafi ke rufewa, saboda tufafin kan ƙara zafi da danshi a wuraren, abin da ke sa bakteriya su yawaita," in ji Dakta Abubakar.

Ya ce babu shakka wannan yana daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da warin jiki.

"Kafin saka tufafi masu tsabta bayan wanka, yana da muhimmanci a tabbatar an busar da waɗannan sassan jiki sosai," in ji shi.

Ko da yake masana ba su bayyana takamaiman magani ko hanyar rigakafin warin jiki ga kowa ba, suna ba da shawarar wasu matakai da za su iya taimakawa wajen ragewa ko kawar da warin jiki:

  • Yin wanka

Ya kamata mutum ya rika yin wanka da ruwa mai tsafta da sabulu mai ƙamshi, tare da tabbatar da cewa an wanke jiki sosai. Yin wanka sau biyu ko sau uku a rana na iya taimakawa wajen rage warin jiki, musamman ga masu yawan zufa.

  • Sanya tufafi masu tsabta

Baya ga kula da tsaftar jiki, yana da matuƙar muhimmanci a rika sanya tufafi masu tsabta domin hana taruwar zufa da bakteriya.

  • Aske gashin hammata da sauran wuraren da suka dace

Barin gashi a ƙarƙashin hammata na iya taimakawa wajen tara zufa da ƙwabakteriya, wanda kan haifar da wari. Aske gashin na taimakawa wajen rage warin jiki a waɗannan wurare. Ana iya yin hakan da reza ko kuma amfani da sinadaran cire gashi.

  • Yin amfani da man shafawa da kayan hana wari

Yana da kyau a rika amfani da man shafawa ko kayan hana warin jiki akai-akai domin taimakawa fata ta kasance cikin tsafta da kuma rage wari.