An kama wasu da ake zargi da kai hari jihar Oyo
Gwamnatin Jihar Oyo ta tabbatar da cafke wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a harin da ’yanbindiga suka kai kan sansanin dakarun hadin gwiwa na Operation Burst a Karamar Hukumar Oorelope, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a yankin Oke-Ogun.
Mazauna yankin sun ce maharan dauke da muggan makamai ne suka mamaye sansanin sojojin ne da mislain karfe 5 na asuba zuwa 6 na safiyar Lahadi, tare da budewa jami'an tsaron da ke gadin sansanin.
Sun kuma cinnawa wani bangare na wurin wuta da kona motar jami'an tsaro ta sintiri, sannan babu asarar rai ko jikkata ya yin harin.
Wannan hari na zuwa kasa da sa’oi ashirin da hudu da Hukumar tsaro ta farin kaya DSS a kasar ta sanar da cewa wasu ‘yan ta’adda na shirin kafa sansani a Jihar Osun domin jin dadin kai hare-hare a shiyyar gabanin babban zabe na shekara ta 2027 a Naeriya.
Maharan sun kuma yi awon gaba da injin bada wutar lantarki da Babur. Mukdashin gwamnan jihar Oyo Mista Bayo Lawan ya kai ziyarar gani da ido a inda aka kai harin.



























