Da gaske ɗaurin rai-da-rai za ku sha idan kun kasa biyan bashin NELFUND?

Asalin hoton, NELFUND
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A ƙarshen makon da ya gabata ne wata sabuwar dambarwa ta ɓarke a Najeriya game da biyan bashin karatu da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi na NELFUND.
Mahawarar ta ɓarke ne bayan da aka fitar da hoton wata jarida ɗauke da wani labari da ke nuna shugaba Bola Tinubu ya amince da hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan ɗaliban da suka gaza biyan bashin da suka karɓa daga asusun ba da Lamunin karatu na Najeriya (NELFUND).
Labarin wanda aka wallafa a wata jarida da ke ɗauke da kwanan watan ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, 2027, ya yi iƙirarin cewa Tinubu ya bayyana cewa: "Dukkan daliban da suka gaza biyan bashinsu bayan kammala karatu za su fuskanci hukuncin ɗaurin rai-da-rai a gidan yari."
Wannan labarin dai ya tayar da ƙura tsakanin ɗaliban ƙasar musamman waɗanda suka amfana daga shirin lamunin, lamarin da ya sanya dayawa daga cikin su zullumi kan makomarsu idan har suka gaza biyan wannan bashi.
Ko da yake hukumomi sun ƙaryata labarin, amma dai ya ci gaba da ɗaukar hankali musamman a shafukan sada zumunta.
Mene ne martanin NELFUND?

Asalin hoton, NELFUND/X
Hukumar kula da asusun ba da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ta musanta wannan labari da ke yaɗuwa, inda ta ce labarin ba shi da tushe ballantana makama.
Hukumar ta bayyana iƙirarin a matsayin "labarin karya" a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na dandalin X ranar Lahadi, inda kuma ta nuna hoton sanarwar ta bogi da ake yaɗawa a shafukan intanet.
Wannan ƙarin haske dai shi ne na baya-bayan nan cikin jerin gargaɗin da hukumar ta yi game da bayanan da ke haifar da rudani dangane da shirin bayar da rancen kuɗi ga dalibai.
A baya, NELFUND ta ƙaryata wasu bayanai na bogi da aka ƙirƙira game da dakatar da bai wa ɗalibai bashin karatun.
An kafa asusun ne bisa tanadin dokar rancen karatu wadda Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu tare da sake tabbatar da ita a shekarar 2024.
Asusun yana bayar da rance marar riba ga daliɓan Najeriya da suka cika sharuɗɗa a manyan makarantun gwamnati, inda rancen ke biyan kuɗaɗen makaranta da kuma kuɗaɗen kula da rayuwa.
Yaushe ake fara biyan bashin?
A tsarin biyan bashin na yanzu, ba a buƙatar waɗanda suka ci gajiyar shirin su fara biyan kuɗin nan take bayan sun kammala karatu.
Lokacin biyan bashin yana fara aiki ne shekaru biyu bayan kammala shirin yi wa ƙasa hidima (NYSC), muddin wanda ya karɓi bashin yana da aikin yi ko kuma yana samun kuɗin shiga.
Ga ma'aikata masu karɓar albashi da suka karɓi bashin karatun, za a riƙa cire yana cire kashi 10 cikin 100 na albashinsu na wata-wata, da sauran kuɗaɗen shigarsu kai tsaye domin biyan bashin.
Waɗanda ke gudanar da sana'ar kansu kuma za su biya kashi 10 na jimillar ribar da suka samu a wata zuwa asusun.
Waɗanda suka ci gajiyar shirin amma har yanzu ba su samu aikin yi ba kuma ba su da hanyar samun kuɗi bayan wa'adin biyan kuɗin ya wuce, za su iya neman ƙarin wa'adi ta hanyar gabatar da takardar rantsuwa, kamar yadda hukumar NELFUND ta tsara.
Hanyoyin samun bashin NELFUND
Bisa ƙa'idar hukumar ta NELFUND bayar da lamunin karatu ta Najeriya, Nelfund Umar Mukhtar ya ce lissafa hanyoyin da ɗalibi mai son samun lamun karatu daga hukumar kamar haka:
- Dole me neman lamunin ya zama ɗalibi
- Dole ne ya mallaki lambar kasancewarsa ɗan Najeriya
- Dole ya mallaki lambar banki ta BVN
- Makarantar da mutum yake so ta tabbatar da bayanan gamsuwa a kan ɗalibi
Jami'in ya ƙara da cewa bayan ɗalibi ya kammala karatunsa ne sannan bayan shekara biyu da gama yi wa ƙasa hidima lokacin ne ake sa ran zai fara biyan kaso 10 cikin 100 na albashinsa domin fara biyan bashin.
Dangane kuma da batun kuɗin ruwa da wasu mutanen ke shakka, sai jami'in ya ce "babu kuɗin ruwa shi ya sa ma muke kiran sa da lamuni maimakon bashi."
Ya ƙara da cewa kawo yanzu ɗalibai sama da 40,000 ne suka karɓi bashin karatun.











