KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 07/09/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 07/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Jirgin yaƙin Amurka na USS Ross ya isa Kenya bayan yaƙin Iran

    Jiragen

    Asalin hoton, US NAVY

    Wani jirgin ruwan yaƙin Amurka mai ɗauke da makamai masu linzami, USS Ross, ya isa tashar jiragen ruwa ta Mombasa a wata ziyara da aka tsara tun da farko, yayin da Amurka da Kenya ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu kan tsaron teku da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

    Jirgin yakin na USS Ross, wanda ke cikin rukunin jiragen ruwa na Arleigh Burke-class, ya isa Mombasa ne a ƙarshen mako, a yayin wani aiki da rundunar sojin ruwan Amurka ke gudanarwa a yankunan Afirka da Turai.

    Muƙaddashiyar Jakadiyar Amurka a Kenya, Susan M. Burns, ta ce ziyarar na nuna irin ƙarfin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    ''Wannan ziyara ta nuna ƙarfin haɗin gwiwar Amurka da Kenya da kuma dogon tarihin da muke da shi na aiki tare kan batutuwan yankin da suke da muhimmanci ga ɓangarorin biyu," in ji Mrs Burns.

    Ta ƙara da cewa tasoshin jiragen ruwa na yankin kamar ta Mombasa na bai wa sojojin Amurka damar samun muhimman ayyuka kamar samar da kayayyaki da man fetur da sauran abubuwan da suke buƙata, yayin da irin waɗannan ziyarce-ziyarcen jiragen ruwa ke taimakawa wajen musayar ƙwarewa tsakanin dakarun Amurka da na Kenya.

    Kwamandar jirgin na USS Ross, Kyaftin Pia Chapman, ta ce ziyarar ta kuma bai wa sojojin da ke cikin jirgin damar hutawa bayan wani lokaci da suka shafe suna yaƙi da Iran.

    "Dakarunmu sun yi aiki tuƙuru matuƙa a yayin wannan aiki, inda suka gudanar da ayyukansu cikin tsari da ƙwarewa da haɗin kai," in ji Chapman.

  2. Mutum biyar sun mutu bayan jirgi ya yi hatsari a Amurka

    Jirgin dakon kaya

    Asalin hoton, Reuters

    Wani jirgin dakon kaya na kamfanin Amazon Air ya kauce daga titin saukar jiragen sama yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jiragen sama na Miami International Airport, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu biyar da munanan raunuka.

    Jirgin dakon kayan ƙirar Boeing 767-300 ya yi hatsarin ne jim kaɗan kafin ƙarfe biyu na rana agogon ƙasar (19:00 agogon GMT), bayan da ya tashi daga filin jirgin sama na Luis Muñoz Marín da ke San Juan, Puerto Rico.

    Har ila yau, jirgin ya bugi wasu motoci da ke kusa da wurin da hatsarin ya auku.

    Kamfanin Amazon ya ce yana "aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomi da sauran jami'an da abin ya shafa domin gano ainihin abin da ya faru."

    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta dakatar da duk wani tashin da saukar jirage a filin jirgin saman, yayin da jami'an kashe gobara da na agajin gaggawa suka garzaya wurin da hatsarin ya faru.

    Hatsarin ya afku ne a daidai lokacin hutun Ranar Ma'aikata - ɗaya daga cikin lokutan tafiye-tafiye mafi yawan cunkoso a shekara.

    Magajin garin gundumar Miami-Dade, Daniella Levine Cava, ta bayyana a wani taron manema labarai da yammacin ranar Lahadi cewa, "Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata."

  3. Yaƙinmu da Rasha zai iya ci gaba har zuwa lokacin hunturu - Zelensky

    Volodymyr Zelensky ya ce yana sa ran ci za a ci gaba da gwabza yaƙi da Rasha har cikin lokacin hunturu.

    Ya bayyana haka bayan tattaunawarsa ta farko da jakadun Donald Trump a Kyiv-Jared Kushner da Steve witkoff.

    ''A yanzu mutane da dama a nan na shiryawa don tsananin da wannan rikici zai yi da kuma tsananin faɗa a lokacin hunturu,'' in ji shi.

    Amurkawan sun fara tattaunawa ta biyu da Shugaban Ukraine bayan sun yiwa ƙasashen ƙawance ƙarin haske.

    Mista Zelensky ya jaddada buƙatar ƙulla yarjejeniyar sulhun da ba za ta bai wa Rasha damar sake kai wani hari ba.

  4. Iran ta ce za ta sanar da sabon yankin tsaro a mashigar Hormuz

    Mohsen Rezaei

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban jami'in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya ce Iran za ta sanar da sabon yankin da aka sanya wa tsaro a wajen mashigin Hormuz.

    Ya ce yankin zai kai har zuwa wasu sassan Tekun Fasha.

    Duk jirgin ruwan da ya shiga yankin da nufin ketare mashigin ruwan, za a saka shi cikin jerin wadanda aka sanyawa takunkumi.

    Tun da farko, mai shiga tsakani na Iran Mohammad Ghalibaf, ya yi gargadin cewa Iran za ta dauki matakin mayar da martani mai tsanani cikin kan Amurka cikin gaggawa.

  5. Sallama

    Assalamu alaikum, masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu d asafiyar wannan rana da Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoronka, kamar yadda Hausawa ke yi wa kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.