Me ya sa matan Afrika da dama ke amfani da man ƙara hasken fata?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Oyenike Balogun
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Conversation*
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A wasu ƙasashen Afrika, fiye da kashi 50 cikin ɗari na mata suna amfani da man shafawa mai ƙara hasken fata.
A Afrika ta Kudu yawan matan a Najeriya ya kai 77%, wata ƙididdiga da ta zarce wadda ake da ita a sauran sassan duniya.da ke shafa man bilicin ya kai 32%, kuma
Wannan ɗabi'a tana da illoli sosai. Man bilicin da ƙwayoyin ƙara hasken fata abubuwa ne da ake saidawa ba tare da ƙayayyade hanyoyin amfani da su daga ƙwararru ba, saboda haka suna janyo illoli kamar lalacewar fata da jefa mai amfani da su cikin haɗarin shanyewar sassan jiki da kuma rashin warkewar ciwo da sauri bayan tiyata.
Amma har yanzu masu bincike ba su gano dalilin da ya sa mata ke ci gaba da amfani da irin wannan mai da kuma ƙwayoyin ƙara hasken fata ba. Wannan na da muhimmancin gaske saboda zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar al'umma.
Hasashen da ake yi dai shi ne cewa mata suna shafa man ƙara hasken fata ne saboda rashin gamsuwa da yadda fatarsu ta asali take ba. Amma wannan wani abu ne mai wahalar tabbatarwa.
Mafi yawan nazarin da aka gudanar sun mayar da hankali ne ga tambayar mutanen yadda suke ji dangane da kalar fatarsu.
Amma aikin da na gudanar a matsayin mai bincike kuma ƙwararre kan halayyar ɗan Adam ya nuna cewa waccan hanyar ta amfani da ra'ayoyin jama'a kacal ba zai wadatar ba saboda hanya ce marar inganci.
Mutane ba su cika amsa tambayar da ake masu tsakani da Allah ba. A wasu lpkutan, ana kallon masu sauya kalar fatarsu a matsayin masu raina halittar da Allah ya yi masu. Saboda haka wannan ƙyama da ake masu tana iya sanya mutane su ƙi amsa tambaya kai tsaye game da abin da ya sa suke amfani da man shafawa mai ƙara hasken fata.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin samar da mafita ga wannan matsala, ni da abokan aikina mun ɓullo wa batun ta wata hanya ta daban.
A rahoton bincike mu da aka wallafa, mun yi ƙoƙarin gano ko dabarar amfani da gwajin da ake yi wa fata na Skin IAT (Impulse Skin Association Test) a turance zai fi wanda aka saba yi inganci.
Wannan wata hanyar gwaji ce da ake amfani da saurin mutum wajen bayar da amsa da kuma yadda ya yi amfani da kalma mai kyau ko mummuna game da baƙar fata ko kuma farar fata.
Dabarar a nan ita ce, idan mutum ya alaƙanta farar fata da alheri kuma ya alaƙanta baƙar fata da sharri, to masana sun gamsu cewa mutum na goyon bayan ƙara hasken fata, ko da kuwa a amsar da ya bayar bai furta hakan da bakinsa ba.
Wannan salon gwaji ya taimaka wajen kaucewa jefa tambaya kai tsaye ga mutane kan abubuwan da suke neman karewa ko ɓoyewa. Masana sun kuma yi amfani da wannan dabara wajen tantance zaɓin mutane kan abubuwan da suka shafi ƙabila da addini da ƙiba ko rama.
Sakamakon binciken mu ya yi nuni da rashin daidaito mai ban mamaki: Aƙalla kashi 79 cikin 100 n mutanen da aka yi wa gwajin sun fi karkata ga son farar fata, yayin da nazarin da aka yi inda aka yi wa mutane tambaya kai tsaye kan laufin fatar da suka fi so ya nuna akasin haka.
Waɗannan sakamako na da muhimmanci saboda sun fitar da haƙiƙanin gaskiyar cewa abubuwan da ke ruruta wutar amfani da man bilicin a nahiyar Afirika, sun zarce batu na zamantakewa kaɗai.
Abin ya samo asali ne daga zamanin mulkin mallaka da yadda aka fifita fararen fata wajen nuna ƙarfin tattalin arzikin duniya da kuma yadda kafafen yaɗa labaran yamma suka kambama wannan yekuwa.
Duk wani nazari da ya fito da irin wannan batutuwa na buƙatar amfani da salon tattara alƙalumma kala-kala domin samun cikakkun bayanai, inda za a bai wa mata damar bayyana dalilan su na yadda kalar fatar su ke da alaƙa yadda rayuwarsu take.
Nazari kan bayanan da mutane ba su bayyana ƙarara ba
Binciken mu ya yi nazari kan mata baƙar fata 221, mafi yawan su daga Afirika ta Kudu. Wannan ne mafi yawan mata da aka yi nazari kan su domin yin nazari kan abin da ya shafi baƙaƙen matan Afirika.
Bayan wancan gwajin, mun kuma buƙaci su yi wani gwajin tattara bayanai dangane da launin fatarsu har sau biyu.
Matan da suka shiga wannan gwaji dole sai da suka zamo baƙaƙen mata, masu shekara aƙalla 18 kuma waɗanda suka amince za su amsa tambayoyi kan yadda halittarsu ta ke.
Bayan gwajin IAT (Impulse Skin Association Test) sakamako ya nuna cewa kashi 79 cikin 100 na matan sun fi ƙaunar farar fata.
Gwajin kai tsaye na tambayoyin da aka yi masu kuma ya nuna cewa kashi 18 cikin 100 ne suka fi son farar fata, yayin da aka sake yin gwaji na biyu wanda ya nuna cewa kashi 29 cikin 100 n suka fi son farar fata.
Sakamakon da muka samu a binciken mu (kashi 79 cikin 100) na masu son farar fata a nahiyar Afirika ya yi kusan daidai da kashi 77 cikin 100 masu amfani da man shafawa don ƙara hasken fata a Najeriya.
Wannan banbanci na da muhimmanci. Ƙila alama ce cewa da dama a cikin baƙaƙen matan Afirika ba su fahimci haƙiƙanin dalilin da ya sa suka fi ƙaunar farar fata ba, ko kuma basu gamsu cewa ya kamata su iya fitowa fili su bayyana dalilan nasu ba.
Waɗannan mata ne da a zahiri suke bayyana cewa sun gamsu 100 bisa 100 da launin fatar su, amma gwajin ɓoye da aka yi ya nuna cewa sun fi ƙaunar farar fata.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Dabarun da suka fi dacewa a yi bincike da su
A matsayin masu bincike, ba mu kore amfani da salon tambaya kai tsaye wajen tattara irin wannan bayanai. Suna taimaka mana wajen tantance abubuwa masu alaƙa da halayyar ɗan Adam. Kuma salon yana da tasiri sosai a muhimman bincike da ƙwararru suka gudanar.
Asali ma, binciken mu ya nuna buƙatar amfani da dabaru da dama wajen tantance zaɓin mutane a kan abubuwan da suka shafe su.
Amfani da wasu dabaru kamar tattaunawa mutum da mutum ko tattaunawar cikin jama'a zai taimaka wajen tatsar muhimman bayanai da ba lallai a iya fitar da su ta amfani da salo ɗaya kacal ba.
Domin haka wannan salo ne da ke taimakawa wajen fitar da ƙarin bayanai da ingancin bincike kan abubuwa da suka shafi zaɓin mutane a kan rayuwa da al'adu da kuma sauran al'amurran da suke so ko kuma suke ƙi.
A yanzu da ƙasashen nahiyar Afirika ke fama da ƙalubalen kiwon lafiya saboda wannan mummunar ɗabi'a, nauyi ne kan ƙwararru a fannin kimiyya su tashi tsaye domin magance matsalar. Wannan na nufin ƙara bullo da dabarun tantance bayanai daga baƙaƙen mata ƴan Afirika da kuma yin haɗin gwiwa da su wajen aikin.
Wannan kuma na nuni da buƙatar tantance cewa ba komai bane da mata ke faɗi game da jikin su ake ɗauka haƙiƙanin abin da suka gamsu da shi.










