Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gasar kofin duniya 2026: Abin da kuke son sani kan wasan Brazil da Morocco
Brazil, wadda ta lashe kofin duniya sau biyar, za ta kara da mai rike da kofin nahiyar Afirka, Morocco a ɗaya daga cikin wasannin da zai ja hankali a matakin rukuni a gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Kuma BBC Hausa za ta kawo muku wasan kai-tsaye a shafinmu na bbchausa.com
Wannan shi ne wasan farko da za a kara ranar Asabar a rukuni na uku da ya haɗa har da Haiti da kuma Scotland, waɗanda sai a ranar Lahadi za su buga nasu wasan.
Brazil, wadda yanzu ke karkashin jagorancin shahararren koci, Carlo Ancelotti na fatan taka rawar gani a wannan gasa da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Brazil ɗin za ta fuskanci kalubale a wajen Morocco, wadda ta kafa tarihin zama ta farko daga Afirka da ta kai matakin daf da karshe a gasar duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Karon farko da Morocco za ta buga babbar gasar tamaula da sabon koci, Mohamed Ouahbi, bayan da ya ja ragamar matasan kasar a watan Satumba da suka lashe kofin duniya na matasa ƴan kasa da shekara 20.
Shi kansa Carlo Ancelotti, wannan shi ne karon farko da ya ja wata kasa zuwa gasar cin kofin duniya a tarihi, sai dai ya taɓa yin mataimakin Arrigo Sacchi a 1994 tare da tawagar Italiya da ta kai zagayen karshe, amma ta yi rashin nasara a hannun Brazil.
Sai dai Ancelotti ya buga wa Italiya gasar cin kofin duniya a 1986 da kuma 1990 a matsayin ɗan wasan da ke taka leda a tsakiya.
Za a buga wasan da karfe 11:00 na dare agogon Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Kididdigar da ta kamata ku sani a kan wasan
- Karo na biyu da za su fuskanci juna a gasar kofin duniya, bayan da Brazil ta ci 3-0 a ranar 16 ga watan Yunin 1998.
- Wannan shi ne karo na 23 da Brazil ke halartar gasar cin kofin duniya.
- Brazil ta lashe kofin duniya sau biyar, sai dai rabon ta da kofin tun 2002.
- Morocco tana halartar gasar cin kofin duniya karo na bakwai.
- Lokacin da ta fi nuna kwazo shi ne kaiwa matakin daf da karshe a Qatar a 2022.
- Morocco ba ta taɓa yin nasara a wasan farko a Kofin Duniya ba, kuma ba ta taɓa fuskantar wata tawagar daga Kudancin Amurka ba, tun bayan 1998.
- Brazil ta yi nasarar doke Morocco a birnin Nates a 1998 tare da ƙwararrun ƴan wasa irin su Ronaldo da Rivaldo da Bebeto da dai sauransu.
Abubuwan da suka sauya bayan wasan da kasashen suka yi a 1998
Wannan babban wasa ne da za a buga a cikin rukuni na uku tsakanin Brazil da Morocco a filin New York, New Jersey.
Karon farko da za a ga kamun ludayin kociyan Brazil, Carlo Ancelotti, wanda karon farko da zai yi koci a gasar cin kofin duniya, wanda a baya ya mayar da hankali kan horar da manyan ƙungiyoyin tamaula daga nahiyar Turai.
Ya kuma koma Brazil, bayan barin Real Madrid, sakamakon kalubalen da ƙungiyar Sifaniya ta fuskanta a 2024/2025.
Kofin duniya yana hannun Argentina wadda ta ɗauka a Qatar a 2026, kenan Brazil za ta so karɓar shi daga abokiyar hamayya daga Kudancin Amurka, sai dai za ta fuskanci kalubale, domin akwai fitattun kasashe a gasar ta bana.
Morocco tana daga cikin kasashe 10 da ke wakiltar Afirka a gasar bana, kenan wannan dama ce da wata kasa daga Afirka za ta taka rawar gani, musammam da Morocco ta kai zagayen daf da karshe a gasar 2022.
Tun farko Afirka ta Kudu ta fara da rashin nasara 2-0 a wasan farko da Mexico, kuma da ƙyar ne idan Bafana-Bafana za ta kai bante, kenan hankula na kan Morocco ranar Asabar domin ganin abin da za ta buga da Brazil.
Daga nan ne za a fayyace ko za ta yi nisa a gasar da ake buga wa a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Abin da mai horar da Brazil da na Morocco suka ce
Carlo Ancelotti, kocin Brazil:
"Tsoro wani muhimmin bangare ne na rayuwa. Idan ba ka jin tsoro, za ka iya ganin zaki tamkar kyanwa. Tsoro zai iya taimaka maka tsara rayuwa. Akwai lokutan da za ka shiga damuwa domin ba ka da tabbas ko tawagarka za ta buga wasan da ya dace. Amma kuma dole ne ka kasance mai cike da kwarin gwiwa. A dabi'ata ni mutum ne mai fatan samun nasara a koda yaushe, kuma ina ganin Brazil ta shirya sosai domin wannan wasan farkon da kuma na Kofin Duniya baki ɗaya."
Mohamed Ouahbi, kocin Morocco:
"Mutane da yawa suna cewa wannan ba ita ce Brazil ta baya ba, mai abin ban mamaki. Amma kuma har yanzu Brazil ce. Gaskiya idan ka kalli ingancin ƴan wasanta da kuma ƙudirin da suka sa na lashe wannan Kofin Duniya, za ka ga cewa har yanzu Brazil ce. A gare mu, wannan wasa yana da matuƙar daraja da mahimmaci. Babban abin alfahari ne mu fara wasan farko a cikin rukuni da Brazil a gasar cin Kofin Duniya ta 2026."
Ƴan wasa 11 da ake sa ran za a fara karawar da su
Ƴan wasan Brazil 11:
Alisson; Danilo, Marquinhos, Gabriel Magalhaes, Alex Sandro; Bruno Guimaraes, Casemiro, Lucas Paqueta; Raphinha, Matheus Cunha, Vinicius Junior
Ƴan ƙwallon Morocco 11:
Bounou; Hakimi, Riad, Diop, Belammari; El Aynaoui, Bouaddi, Ounahi; Brahim Diaz, Rahimi, Saibari
Filin wasan da za a kara tsakanin Brazil da Morocco
Filin Wasan New York New Jersey Stadium, wanda aka bude a shekarar 2010, filin wasa ne da ake amfani da shi a fannoni da dama, wanda a halin yanzu zai karɓi bakuncin wasan ƙwallon zari ruga na Amurka, NFL tsakanin New York Giants da New York Jets da za a buga cikin watan Agusta.
Wannan filin ya zama wajen da aka buga wasan karshe a gasar Fifa ta zakarun Duniya, wato Fifa World Cup Cup a 2025, inda magoya baya daga sassa daban-daban na duniya suka kalli yadda Chelsea ta lallasa Paris Saint-Germain da ci 3-0 ta lashe kofin a wasan karshe da ya kayatar.
A wannan lokacin da aka fara gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026, za a buga wasa takwas a wannan filin, ciki har da biyar daga cikin rukuni.
Daga nan filin zai karɓi bakuncin ɗaya daga zagayen kasashe 32 da kuma ɗaya a zagayen ƴan 16.
A kuma filin ne za a buga wasan karshe da kuma bikin rufe gasar a ranar 19 ga watan Yuli.