Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Allah ne kaɗai zai iya magance matsalolin tsaron - Matawalle

    Ƙaramin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya bayyana dalilin da ya sa ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a Najeriya.

    A hirarsa da BBC ya ce, ‘duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi, al’umma na da rawar takawa sannan Allah ne kaɗai zai iya magance matsalolin tsaron.’

  2. Gwamnatin Sokoto za ta raba wa manoma takin zamani

    Gwamnatin jihar Sokoto ta ware kuɗi domin sayo takin zamani da iri ingacce da magungunan feshin gona da sauran ayyuka, inda gwamnatin ta ce za ta kashe naira 1,652,400,000, wanda a cewarta ɗoriya ce ga manoman jihar bayan wanda ƙananan hukumomi ta raba.

    An bayyana haka ne bayan taron majalisar zarwarwar jihar, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

    Ya ce gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da an ba manoman kayyakin aiki a cikin lokaci domin su yi amfana da su yadda ya kamata, sannan noma ya musu sauƙi.

    Haka kuma gwamnatin jihar ta ware naira 1,609,146,000 domin sayo baburar da za a raba wa ma'aikata a matsayin lamuni mai sauƙi.

    "Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da bai wa ma'aikatan jihar baburar ne domin cika alƙawarin da ya ɗauki a jawabinsa na ranar ma'aikata a Sokoto," kamar yadd sanarwar ta bayyana.

    Haka kuma gwamnatin jihar ta amince da gina asibitoci ƙanana a garuruwan Majemar Korino da Tudun Wada da ke ƙaramar hukumar Sokoto ta Kudu.

  3. Rasuwar Janar Rabe babban rashi ne ga Najeriya - Rundunar tsaro

    A saƙon jaje da rundunar tsaron Najeriya ta fitar, ta bayyaa rashin a matsayin babba, inda ta ce za ta ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar baki ɗaya.

    "Muna miƙ saƙon ta'aziyya da jaje kan rasuwar abokin aikinmu Manjo Janar Abubakar ga iyalansa da sauran ƴan Najeriya baki ɗaya. A lokacin da yake aiki a matsayin mai magana da yawun rundunar tsaro, ya taimaka matuƙa wajen yaƙi da matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta."

    Rundunar ta ƙara da cewa jajircewarsa da ƙoƙarinsa wajen tabbatar a zaman lafiya da haɗin kan Najeriya abin koyi ne babba.

    Sai dai rundunar ta ce sun yi shiru ne game da sacen shi da aka yi saboda yunƙurin da ake yi ne ceto shi, inda jami'an tsaron Najeriya sun kasance suna ta ƙoƙarin tabbatar da ceto shi cikin ƙoshin lafiya.

    "Mutuwarsa za ta sa jami'anmu su ƙara ƙaimi wajen cigaba da aiki ba dare ba rana domin kare martabar ƙasarmu Najeriya da kuma tabbatar da kariyar al'ummar ƙasar baki ɗaya," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "muna tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da tsaro a ƙasar, tara da cimma duk waɗanda suke da hannu a matsalolin tsaro."

  4. Masu zanga-zanga kan satar mutane da kashe-kashe sun toshe babbar hanya a Abuja

    Wasu masu zanga-zanga sun toshe wata babbar hanya a Abuja domin nuna fushinsu kan ƙaruwar hare-hare da garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a ƙasar.

    Masu zanga-zangar, waɗanda ke neman a inganta tsaro, sun kulle gada da ke kan titin Karu-Nyanya, wacce ke haɗa jihar Nasarawa da Abuja, inda suka rika daga alluna tare da rera waƙoƙin suka ga gwamnati.

    Rahotanni sun ce zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani a titin Abuja zuwa Keffi, lamarin da ya bar matafiya da dama a makale na tsawon lokaci.

  5. Wane ne Janar Rabe da ya rasu a hannun ƴanbindiga?

    A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun ƴanbindiga a jihar Katsina.

    Gwamnatin Katsina ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Nasiru Mu'azu ya fitar, inda ya ce tsohon hafsan ya rasu ne sakamakon ta'azzarar ciwon siga da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

    Sanarwar ta bayyana cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar tare da jami'an tsaro suka yi na ganin an kuɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya, ba su samu nasarar ceto shi da rai ba.

    Mutuwar tasa ta jefa iyalansa da al'ummar jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya cikin alhini da jimami.

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin tare da bayyana lamarin a matsayin babbar asara.

  6. Za a binne tsohon jagoran addinin Iran Ali Khamenei ranar 8 ga Yuli

    An sanar da cewa za a binne tsohon jagoran Iran, Ali Khameneia ranar 8 ga watan Yulin 2026, watanni uku bayan mutuwarsa a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai masa.

    A cewar sanarwar da ofishin wallafa ayyukansa ya fitar, za a fara gudanar da jana’izarsa a ranar 4 ga Yuli a Tehran, kafin a binne shi a ranar 8 ga watan Yuli a harabar masallacin Imam Reza da ke Mashhad.

    An kuma ce za a gudanar da jana’izar wasu daga cikin ’yan uwansa da suka mutu tare da shi a hare-haren, a garuruwa daban-daban da suka haɗa da Tehran, Qom da Mashhad.

    Haka zalika, jami’ai sun bayyana cewa ana sa ran taron zai tara miliyoyin jama’a, inda aka tsara shirye-shirye na musamman ciki har da gangamin jama’a na kwanaki uku.

  7. Sojoji sun daƙile hare-haren 'ƴan ta’adda' a Arewa mas Gabasin Najeriya

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun samu nasarar daƙile wani yunkurin kutsen '’yan ta’adda' tare da lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

    Wannan na daga cikin kokarin da rundunar ke yi na kakkabe karfin ’yan ta’adda da hana su ci gaba da kai hare-hare.

    A Jihar Borno, sojoji sun yi gaggawar mayar da martani bayan hangen motsin ’yan ta’adda da ke kokarin isa cibiyar horas da sojoji a Buni Yadi a ranar 9 ga watan Yuni in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

    Rundunar ta ce sojojinta sun bude wa maharan wuta inda suka fatattaki su tare da kashe wasu daga cikinsu, inda aka gano gawar ‘yan ta’adda biyu da kuma babur daya a wurin.

    A wani bangare kuma, farmakin sirri da aka gudanar ya kai ga kama wasu da ake zargi suna samar wa ’yan Boko Haram da ISWAP kayan aiki a yankin Damboa.

    Rundunar sojin ta jaddada cewa wadannan nasarori na nuna yadda take da kudurin karya hanyoyin taimaka wa ’yan ta’adda tare da tabbatar da tsaro da dawowar zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

  8. An harba wani abu kan jirgin mai a gabar tekun Oman

    Hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Birtaniya ta sanar cewa wani jirgin ɗanyen mai ya samu matsala bayan wani abu da ba a tantance ba ya bugi jikinsa a kusa da gabar tekun Oman.

    A cewar hukumar, lamarin ya faru ne kimanin kilomita 11 gabashin gabar Oman a ranar da ta gabata, inda harin ya shafi gaban jirgin.

    Rahotanni sun ce dukkan ma’aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya, kuma babu wani gurɓatar muhalli ko zubar mai da aka samu sakamakon harin.

    An kuma bayyana cewa jirgin ya ci gaba da tafiyarsa zuwa inda ya nufa, yayin da ba a fitar da cikakken bayani kan inda harin ya fito ba.

  9. Janar Rabe mai ritaya ya rasu a hannun 'yanbindiga

    Tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun ’yan bindiga a jihar Katsina.

    Gwamnatin Katsina ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida ya fitar, inda ya ce tsohon hafsan ya rasu ne sakamakon ta’azzarar ciwon suga da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

    Sanarwar ta bayyana cewa duk da kokarin da gwamnatin jihar tare da jami’an tsaro suka yi na ganin an kubutar da shi cikin koshin lafiya, lamarin ya kare da wannan mummunan sakamako.

    Mutuwar tasa ta jefa iyalansa da al’ummar jihar Katsina da ma kasa baki ɗaya cikin alhini.

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin tare da bayyana lamarin a matsayin babbar asara.

    Ya ce wannan wata alama ce dake nuna bukatar kara hada kai domin tinkarar matsalar tsaro da ke addabar al’umma.

    A kwanaki baya ne dai yanbindida suka sace Jamar Rabe da matarsa a Katsina, inda suka nuna su a bidiyo suna kira ga hukumomin Najeriya su ceto su.

  10. Tsarin kula da mashigar Hormuz zai magance dukkan matsaloli - Iran

    Shugaban kwamitin tsaron ƙasa na majalisar dokokin Iran ya bayyana cewa tsarin kula da mashigar Hormuz tabbataccen abu ne ga Iran kuma mai dorewa da zai magance dukkan matsaloli.

    Ɗan majalisar, Ebrahim Azizi, ya ce shirin ya ƙunshi dukkan fannoni da suka haɗa da dokokin zirga-zirga a yankin, tare da jaddada cewa Iran na ɗaukar matakai ne bisa muradun ƙasa cikin hikima da tsari.

    An shirya wannan tsari ne domin mayar da cikakken iko a hannun Iran kan mashigar Hormuz, musamman bayan ƙara tsanantar rikici da kuma matakan da ƙasar ta ɗauka wajen takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

  11. Sojoji sun daƙile hare-haren 'ƴan ta’adda' a Arewa mas Gabasin Najeriya

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun samu nasarar daƙile wani yunkurin kutsen '’yan ta’adda' tare da lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

    Wannan na daga cikin kokarin da rundunar ke yi na kakkabe karfin ’yan ta’adda da hana su ci gaba da kai hare-hare.

    A Jihar Borno, sojoji sun yi gaggawar mayar da martani bayan hangen motsin ’yan ta’adda da ke kokarin isa cibiyar horas da sojoji a Buni Yadi a ranar 9 ga watan Yuni in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

    Rundunar ta ce sojojinta sun bude wa maharan wuta inda suka fatattaki su tare da kashe wasu daga cikinsu, inda aka gano gawar ‘yan ta’adda biyu da kuma babur daya a wurin.

    A wani bangare kuma, farmakin sirri da aka gudanar ya kai ga kama wasu da ake zargi suna samar wa ’yan Boko Haram da ISWAP kayan aiki a yankin Damboa.

    Rundunar sojin ta jaddada cewa wadannan nasarori na nuna yadda take da kudurin karya hanyoyin taimaka wa ’yan ta’adda tare da tabbatar da tsaro da dawowar zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

  12. Hezbollah ta ce ta yi artabu da sojojin Isra’ila a Kudancin Lebanon

    Ƙungiyar Hezbollah ta sanar da cewa dakarunta sun yi arangama da sojojin Isra’ila da ke ƙoƙarin isa garin Majdal Zun da ke kudancin Lebanon.

    Ta ce ta harba roƙoƙi kan sojojin Isra’ila a ranar Alhamis, lamarin da ya tilasta musu ja da baya.

    A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ƙara da cewa a ranar Juma’a ta sake kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma roƙoƙi.

    Har ila yau, ta ce ta kai wasu ƙarin hare-hare kan sojojin Isra’ila a yankunan kudancin ƙasar.

    A ɓangare guda, sojojin Isra’ila sun buƙaci mazauna wasu ƙauyuka uku a kudancin Lebanon da su bar gidajensu, yayin da rahotanni suka ce ana ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban.

    Hukumomin labaran Lebanon sun kuma ruwaito ƙararrakin fashe-fashe masu ƙarfi da harba makamai a kusa da yankin Ali Taher.

  13. Farashin mai ya faɗi sosai saboda hasashen cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka

    Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya faɗi sosai cikin kusan watanni huɗu, sakamakon fatan da ake da shi na cewa za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran nan ba da jimawa ba.

    Farashin danyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 87.33 a kowanne ganga, inda ya ragu da dala 3.05, wato kimanin kashi 3.4 cikin ɗari idan aka kwatanta da ranar da ta gabata.

    Haka zalika, farashin danyen mai na Amurka ya sauka zuwa dala 84.88 a ganga, ragin dala 2.83, ko kuma kashi 3.2 cikin ɗari kenan.

    Wannan shi ne mafi ƙasƙancin farashin danyen mai na Texas cikin kusan watanni uku, tun daga watan Afrilu da ya gabata.

    Masu kasuwa na ƙara samun kwarin gwiwa cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran na dab da kammaluwa, abin da ke rage fargabar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Wani masani a harkar saka hannun jari, John Kilduff na kamfanin Again Capital, ya ce abin da ya janyo faduwar farashin shi ne bayanan da Iran ta bayar na cewa akwai takardar fahimtar juna da ake shirin kullawa da Amurka, wanda ya sa masu zuba jari ke sa ran samun daidaito a kasuwar mai.

  14. Ɗalibai da malamai da aka sace na cikin gandun dajin Old Oyo - Makinde

    Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ɗalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire na jihar har yanzu suna hannun masu garkuwa a cikin gandun dajin Old Oyo National Park.

    Ya bayyana hakan ne a sabon bayanin da ya fitar game da ƙoƙarin ceto su, kusan makonni hudu bayan aukuwar lamarin.

    Makinde ya ce jami’an tsaro na ci gaba da aiki tukuru domin kubutar da wadanda aka sace a yayin hare-haren da aka kai makarantu a garuruwan Yawota da Ahoro-Esinle a ranar 15 ga watan Mayu, 2026.

    A cewarsa, rahotannin sirri sun nuna cewa har yanzu ana tsare da su a cikin babbar gandun dajin Old Oyo, wadda ke da fadin kusan kilomita murabba’i 2,500 a yankuna da dama na jihar.

    Ya kara da cewa girma da wahalar shiga yankin na kawo kalubale ga jami’an tsaro, don haka ana bukatar tsari mai kyau da hadin gwiwa domin samun nasarar aikin ceto.

    Gwamnan ya tabbatar wa al’umma cewa ana bin duk wata sahihiyar hanya domin ganin an ceto wadanda aka sace ba tare da wata illa ba.

    Ya kuma bukaci jama’a da su kasance cikin shiri su kai rahoton duk wani abin da ke da alaka da laifi ta hanyar layin gaggawa na jihar, tare da gargadin cewa yada jita-jita na iya kawo cikas ga aikin ceto

  15. Iran ta yi iƙirarin nasara yayin da tace saura ƙiris a cimma matsaya da Amurka

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ta samu muhimman nasarori waɗanda suka kawo su kusa da cimma yarjejeniya da Amurka domin kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi.

    Ya ce batutuwan da ake tattaunawa sun haɗa har da batun buɗe mashigar ruwan Hormuz, wanda ya ce yana da matuƙar muhimmanci a yarjejeniyar.

    A wata hira da ya yi a gidan talabijin na cikin gida a Iran, Araqchi ya ce bangarorin biyu sun kai mataki mafi kusa da cimma matsaya fiye da kowane lokaci a baya.

    Ya bayyana cewa yanzu haka ana dab da fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, yana mai cewa “an kusa cimma matsaya, saura kaɗan ne.”

    Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai na Iran da su guji yin hasashen da zai iya jefa shakku ko ya dagula tattaunawar, yana mai cewa irin waɗannan rahotanni na iya lalata damar da ake da ita na cimma yarjejeniya.

    A cewarsa, takardar fahimtar juna da ake aiki a kanta ba ta wuce shafi ɗaya da rabi zuwa biyu ba, amma duk da haka an shafe watanni biyu ana nazari da tattauna kowace kalma da ke cikinta sosai.

    Araqchi ya ƙara da cewa an kasance ana sanar da hukumomin tsaro, ciki har da Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa, game da duk wani ci gaba a kai a kai.

    A ƙarshe ya jaddada cewa sakamakon wannan aiki zai ƙara ƙarfafa matsayi da ƙarfin Iran a cikin gida da kuma a idon ƙasashen duniya, yana mai cewa mashigar Hormuz na ƙarƙashin ikon Iran da Oman.

  16. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Asabar.

    Aisha Babangida ce ke fatan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.