Yadda laƙantar tsuguno zai yi tasiri ga lafiyarku

    • Marubuci, Esther Kahumbi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Health
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A duk faɗin China da Japan da yawancin Asiya, yin tsuguno mai zurfi wani ɓangare ne na rayuwar yau da kullun. Mutane suna hutawa ba tare da wahala ba ta hanyar tsugunnawa inda duga-dugansu ke shimfiɗe a ƙasa yayin da suke jiran jiragen ƙasa, ko hira da abokai, ko kuma cin abinci.

Amma bidiyon ƴan yawon buɗe ido da ke ƙoƙarin kwaikwayon wannan tsugunon ya zama abin kallo a shafukan. Yawancin suna faɗuwa da baya, suna shan ƙasa a rigingine ko kuma su jingina da bango don samun tallafi.

Masana motsin jiki sun ce sha'awar wannan tsugunon yana amsa babbar tambaya game da mahimmancin kiyaye motsi mai kyau yayin da muke tsufa.

Don haka, me yasa wasu mutane za su iya tsuguno ba tare da wahala ba yayin da wasu ke fafutukar tsayawa a tsaye?

Me nene Alfanun wannan tsugunnawar?

Ana ɗaukar tsugunnawa a matsayin ɗaya daga cikin mahimman abubuwan motsa jiki.

"Ba za ku iya yin komai ba tare da tsugunnawa ba," in ji Farfesa Christopher Powers, kwararre kan motsin jikin mutane a Jami'ar Kudancin California da ke Amurka.

"Ka na zaune kan kujera ko fitowa daga motar ka ko amfani da banɗaki sunkuyawa domin ɗaukar wani abu daga ƙasa."

Mutane da yawa sun saba da tsugunnawa na yau da kullum, wanda shi ne ɓangare na motsa jiki. Ya ƙunshi tsugunnwa kamar ana zaune, har sai cinyoyi sun yi daidai da ƙasa.

Amma squat na Asiya - ya bambanta. Ya haɗa da tsugunnawa har sai gwiwoyi sun sun lanƙwashe kuma a turo su waje, inda ake buɗe ƙafafu, a tsayar da ƙirji a miƙe, inda cinya zai kasance a kwance kan tsokar bayan ƙafa.

Matt Hsu, wani koci ɗan asalin Asiya da ya ƙware wajen taimaka wa mutane su inganta motsinsu da ƙarfin jikinsu, ya saka bidiyoyi a kafafen sada zumunta kan tsugunawa wanda ya jawo hankalin miliyoyin mutane. Amma ya ce sunan da kansana iya zama kamar yaudara.

"Za ku ga ƴan Afirka da ke iƙirarin cewa tasu ce ... Ƙasashen Slavic, da duk wani a Gabashin Turai zai ce 'wannan tsugunon ta mu ce'. Wannan tsugunawar dai ta kowa ce ," in ji shi.

Waɗannan tsugunnawar mai zurfi na buƙatar ƙarin motsi a kwankwaso da gwiyawu da idon kafa - kuma kuna jin shi a yawancin sassan jiki fiye tsugunnawa ta yau da kullum, in ji likitocin motsa jiki.

Nazarin ya gano wannan tsugunnawa zai iya taimakawa wajen haɓaka motsi da sassauci, da rage ciwon baya, da tabbatar da ƴancin kai gaba ɗaya a duk rayuwarmu.

Yara sukan iya irin wannan tsugunnawar cikin wannan yanayin ba tare da wani tashin hankali ba. Wannan na faruwa ne saboda suna iya motsa gaɓoɓɓinsu fiye da sauran mutane.

Amma sauye-sauye a jiki ba shine kawai dalilin da yasa manya da yawa ke rasa iya yin irin wannan tsgunnawar ba.

Salon rayuwa da aka gina a ka yadda ake zama – yin amfani da kujeru da banɗakuna masu bisa - yana nufin manya da yawa ba kasafai suke buƙatar tsuguno ba a cikin rayuwar yau da kullun, wanda hakan ke bayar da gudummawa wurin raguwar motsi da kuma ƙarfi bayan wani tsawon lokaci.

"Idan ba ku yi amfani da shi ba, za ku rasa shi," in ji Powers, wanda bincikensa yayi nazarin yadda canjin motsi ke taimakawa wajen raunin gwiwa.

Me yasa mutanen Asiya suka fi iya tsugunnawa mai zurfi cikin sauƙi?

Waɗannan sauye-sauyen na salon rayuwa ba su yaɗu sosai ba sassan Asiya kamar Japan, inda ayyukan yau da kullum kamar zuwa gidajen cin abinci suka haɗa da yin tsuguno.

Hsu, wanda shi ne ya kafa Upright Movement, kamfanin da ke ba da ilimin motsa jiki ya ce: "Har yanzu za ku buƙaci shiga wuraren cin abinci akai-akai, ku cire takalmanku, ku tsuguna kan tabarmar, sannan ku zauna ku ci abinci."

Ya ƙara da cewa "A wasu sassa na Asiya, suna da bandaki na tsuguno ne kawai. Idan za ku yi ta haka kowace rana, duk lokacin da kuke bukatar kewayawa, wannan hdama ta iya tsugunnawa ba za ta kufce muku cikin sauƙi ba," in ji shi.

Hsu ya yi magana da BBC tsawon mintuna 40 yayin da yake tsugune na dogon lokaci.

Ya ce mahimmancin motsi kamar tsugunawa ya bayyana ƙarara saboda irin abubuwan da dangins asuka fuskanta.

"Mahaifina ya faɗi har sai da aka kira motar ɗaukar marasa lafiya ta ɗauke shi daga kan titin domin ya kasa tashi daga ƙasa," in ji Hsu.

Duk da kasancewarsa asalin ɗan Asiya, Hsu ya ce ya yi fama da rashin iya tsugunawa sosai a cikin shekarunsa na 20 bayan da aka tilasta masa zama na dogon lokaci yayin da yake murmurewa daga raunin da ya samu a fagen wasanni.

"Na tuna ba na ko iya taɓa idon sahun ƙafafuna saboda rashin iya durƙusawa," in ji shi.

Dole ne Hsu ya horar da jikinsa don sake koyan yadda ake yi hakan - kuma ya ce za a iya koyan yadda ake tsugunawa, yadda ake koyan kowace dabara ta motsa jiki.

Ya ya mutanen Asiya ke tsugunawa

Ga mutanen da suke so su laƙanci yadda ake tsugunawa da kyau, Hsu yayi kashedin kada su kusanci neman yin hakan cikin gaggawa kafin jikinsu ya shirya.

"Ba za ku so ku yi gaggawar tafiya har ƙasa ba saboda wataƙila za ku iya cutar da wani ɓangare na jikinku," in ji shi.

Madadin haka, yana ba da shawarar farawa a hankali ta amfani da tallafi daga kayan ɗaki kamar kujera ko tebur.

"Idan kun yi haka sau biyu a kowace rana na ƴan makonni, za ku lura: 'Oh, na ji lafiya. Zan iya ƙara yin ƙasa'."

Wasu masu ilimin motsa jiki suna jayayya cewa babban batun ba shine ko mutum zai iya zama tare da kwankwasonsa yana daf da ƙasa ba , amma ko mutum zai iya ci gaba da motsi da kansa yayin da ya ke tsufa.

A halin yanzu babu wani binciken da zai tabbatar da tasiri na dogon lokaci ko fa'idodin tsugunawa ga lafiyar mutanen da ke yin hakan na tsawon lokaci.

Hsu ya ce makasudinsa iya tsugunawa shi ne bai wa mutune damar motsa ɓangarorin jikin su da yanayin rayuwar zamani ya ke iya hana su.

''Abin da na yi la'akari da shi, zan ce kuna buƙatar samun damar sarrafa jikin ku, ba tare da fuskantar wasu manyan matsaloli ba."