Ƴan asalin Najeriya 14 da za su buga kofin duniya a 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Super Eagles ba ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a fara daga ranar 11 ga watan Yuni ba a Amurka da Canada da kuma Mexico.

To sai dai tana da ƴan wasa 14 ƴan asalin Najeriya da za su wakilce ta da za a kara tsakanin kasashe 48 a karon farko a tarihin gasar.

Saboda haka, kasa shiga gasar da Najeriya ta yi ta bana, bai hanata samun ƴan ƙwallonta da za su wakilce ta a babbar gasar tamaula ta duniya.

Kenan Najeriya tana da wakilci na daban a gasar—wanda ba a kan sunan ƙasa kai tsaye bane—amma ta hanyar ƴan ƙwallo fiye da 14 masu asalin Najeriya da za su wakilci ƙasashe takwas daban-daban a gasar da za a gudanar.

Wannan yana nuna yadda ƴan wasan Najeriya suka bazu a faɗin duniya, suna taka rawa a manyan lig-lig na Turai da Amurka, har ma sun kai matakin wakiltar ƙasashen da suka taso ko suka girma a cikinsu.

Jerin ƴan Najeriya 14 da za su buga kofin duniya 2026

Ingila: Babbar cibiyar ƴan Najeriya a gasar kofin duniya

Ƙasar da ke da mafi yawan ƴan Najeriya a wannan jerin ita ce Ingila. A nan za a ga wasu manyan taurari da suka yi fice a Premier League:

Bukayo Saka (Arsenal) An haifi Saka a Ingila, amma iyayensa ƴan Najeriya ne daga kabilar Yarabawa

Eberechi Eze (Crystal Palace) An haifi ɗan wasan a Ingila, amma iyayensa ƴan Najeriya ne.

Noni Madueke (Chelsea) Wannan ɗan wasan an haife shi a Ingila, amma iyayensa daga Najeriya suke daga kabilar Igbo.

Waɗannan 'yan wasa sun riga sun zama ginshiƙai a cikin tawagar Ingila, kuma suna daga cikin manyan sunaye da ake dogaro da su a gasar.

A tawagar Faransa, akwai:

Michael Olise (Bayern Munich) An haifi Olise a Ingila, kuma mahaifinsa ɗan Najeriya ne da kuma mahaifiyarsa daga Aljeriya - ya samu damar wakiltar kasa uku da ya haɗa da Ingila da Najeriya da kuma Faransa - hakan ya sa ya zaɓi buga wa tawagar Faransa tamaula.

Ya taka leda tun farko a tawagar matasan Faransa da wakiltarta a Olympic, yanzu yana cikin babbar tawagar kasar.

Tuni kuma Olise ya zama ɗaya daga cikin sabbin taurari da ke ba Faransa ƙarin ƙarfi a gurbin kai hare-hare a tawagar.

A Jamus kuma, akwai:

Jamal Musiala (Bayern Munich) An haifi ɗan wasan a birnin Stuttgart a Jamus, yana da fasfo biyu da yake rike da shi na Jamus da na Ingila.

Tushen kuwa mahaifiyarsa ƴar Jamus ce da kuma mahaifinsa ɗan Najeriya da kuma Ingila. Ya fara buga wa matasan Ingila tamaula kafin daga baya ya zaɓi Jamus.

Felix Nmecha (Borussia Dortmund) An haifi Felix a Hamburg a Jamus, kuma mahaifiyarsa daga Jamus take da mahaifinsa ɗan Najeriya - yana kuma da tsatson Ingila, ya kuma samu damar wakiltar Jamus ko kuma Ingila, wanda ya fara taka leda a matasan Ingila daga baya ya sauya ya koma buga tamaula a Jamus.

Musiala musamman ya zama ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa a Bundesliga, kuma yana daga cikin matasan da ake ganin za su iya canza wasa a kowane lokaci.

A bangaren tawagar Austria:

David Alaba (Real Madrid) Yanzu ya bar Real Madrid, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a karshen kakar da aka kammala ta bana. Alaba yana wakiltar Austria, wanda aka haifa a birnin Vienna, shi ne ma ƙyaftin ɗin tawagar kasar.

Mahaifinsa ɗan Najeriya ne da kuma mahaifiyarsa daga Philippines.

Alaba ya shahara musamman a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun masu tsaron baya a duniya, sai dai kuma ya yi fama da jinya, watakila wannan ce gasar kofin duniya ta karshe da zai halarta.

Carney Chukwuemeka (Borussia Dortmund) An haifi Carney a birnin Vienna a Austria, kuma mahaifansa daga Najeriya, ya fara taka leda a matasan Ingila daga baya ya sauya zuwa buga wa babbar tawagar Austria tamaula.

A Switzerland kuma akwai:

Manuel Akanji (Manchester City) Tun farko Akanji ya samu damar wakiltar Switzerland ko kuma Najeriya - an haife shi a birnin Wiesendangen garin mahaifiyarsa a Switzerland, mahaifinsa kuwa daga Najeriya. Sai dai Switzerland yake yi wa tamaula tun daga matasa har zuwa babbar tawagar kasar.

Akanji yana daga cikin ginshiƙin masu tsaron bayan Manchester City, kuma yana taka muhimmiyar rawa a tawagarsa.

Noah Okafor (AC Milan) An haifi ɗan ƙwallon a birnin Binningen a Switzerland, wanda mahaifinsa daga Najeriya yake.

Ya fara buga wa babbar tawagar tamaula ta Switzerland tun daga 2019.

A tawagar Amurka akwai:

Folarin Balogun (AS Monaco) Ɗan ƙwallon ya samu damar wakiltar Amurka ko kuma Ingila, wanda aka haifa a birnin New York, amma a Ingila ya girma, iyayensa ƴan Najeriya ne.

Ya fara buga wa babbar tawagar Amurka tamaula daga 2023.

A tawagar Canada:

Tani Oluwaseyi (Minnesota United) Shima wannan ɗan wasan ya samu damar wakiltar Super Eagles ko kuma Canada.

An haife shi a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, amma sai iyayensa suka koma Canada suka zauna a Mississauga a Ontario a lokacin da Tani yake da shekara 10 da haihuwa. Daga nan ya fara buga wa tawagar Canada tamaula

Promise David (Union Saint-Gilloise) Tun farko Promise ya samu damar wakiltar kasa biyu tsakanin Canada da Najeriya.

An haife shi a Brampton a Ontario, kuma iyayensa ƴan Najeriya ne, harma ya fara buga wa matasan Najeriya tamaula daga baya ya zaɓi Canada, wadda ta fara saka shi a wasan babbar tawagar a watan Fabrairun 2025.

A tawagar Afirka ta Kudu kuma:

Ime Okon (SuperSport United) An haifi Ime a birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu, inda mahaifinsa ne daga Najeriya, kuma rayuwarsa gabaki ɗaya a Afirka ta Kudu ya yi ta, hakan ya sa ya zaɓi buga wa kasar tamaula.

Waɗannan ƴan wasa suna nuna yadda ƙwallon ƙafa ke zama wasan duniya, inda kenan babu wata iyaka ko katanga tsakanin ƙasashe.

Me wannan ke nufi ga Najeriya?

Wannan yana da ma'ana sosai ga Najeriya. Duk da cewa Super Eagles ba ta kai ga samun tikitin shiga gasar ba, Najeriya na da tasiri a ƙwallon kafa ta hanyar ƴan asalin ƙasar da ke taka leda a manyan ƙasashe a duniya.

Hakan yana nuna abubuwa uku masu muhimmanci:

Inganci da hazakar ƴan Najeriya – Yawan ƴan wasa masu asali daga Najeriya a manyan lig-lig a duniya, yana nuna irin baiwar da ƙasar ke da ita a fannin tamaula.

Rashin tsarin riƙe ƴan wasa – Wasu daga cikin waɗannan ƙwallon sun zaɓi wakiltar wasu ƙasashe saboda tsarin horo da kulawa da suka samu a can.

Tasirin Najeriya a duniya – Duk da rashin Najeriya a gasar cin kofin duniya a bana kuma karo na biyu a jere - kasar tana da ƴan asalinta da za su wakilce ta a wasannin.

Najeriya tana nan a ko'ina a fannin taka leda a duniya:

Kofin Duniya da za a buga a 2026 tsakanin Amurka da Canada da kuma Mexico zai nuna wani sabon salo a fannin ƙwallon ƙafa—inda ba ƙasa ce kaɗai ke buga gasar ba, har ma da asali da tarihin ƴan ƙwallon.

Duk da rashin Super Eagles, Najeriya ba ta ɓace daga gasar ba. A maimakon haka, tana nan a cikin kasashen da za su kece raini a manyan filayen wasannin, kuma a manyan lokutan da za a kafa tarihin a gasar.

A takaice, Najeriya ba za ta buga gasar cin kofin duniya a 2026, amma tana da wakilcin ƴan asalin kasar su 14 da za a ɓarje gumi tare da su.