Me ya sa ake zargin Wike da cefanar da wuraren shaƙatawa a Abuja?

Wike

Asalin hoton, BBC Pidgin

Lokacin karatu: Minti 3

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zargin Ministan Abuja, Nyesome Wike da cefanar da wasu muhimman wuraren shaƙatawa a babban birnin tarayya Abuja, inda wasu ke ganin ana lalata tsarin birnin.

Wani faifan bidiyon da ya yi yawo a kafofin sada zumunta ya nuna wata malamar cocin Family Worship Center da ke Abuja ta tsuguna tana roƙon ministan ya haƙura da cefanar da wajen shaƙatawa na Jabi Lake.

An dai kwana biyu ana maganganu kan zargin ana cefanar da wasu wuraren da wasu ke ganin na shaƙatawa ne, wasu wuraren kuma ake ganin tamkar filaye da aka ware domin ƙawata birnin da fulawoyi.

Rahotanni na nuna cewa a yanzu haka akwai manyan wurare aƙalla guda huɗu da aka sayar ko kuma za a sayar ga masu zuba hannun jari domin mayar da su wurin shaƙatawa na kudi ko kuma rukunin gidaje.

Abin da Sarah Omakwu ta faɗi

A bidiyon, fasto Sarah Omakwu ta buƙaci ministan ya bar wajen shaƙatawar ya ci gaba da zama na kowa da kowa, inda ta ce cefanar da shi zai taɓa walwalwar jama'a.

"Ba zan iya faɗa da kai ba a matsayinka na ministan Abuja, amma ina roƙon ka a matsayina na uwa a wannan yankin da a haƙura da cefanar da wurin shaƙatawa na Jabi," in ji ta.

Ta ce wajen na da amfani ga mutane domin zuwa atisaye da kasuwanci, "sannan mutane suna zuwa shaƙawa, har wasu suna haɗuwa a wuri, har shaƙuwar ta kai ga yin aure," in ji Fasto Sarah.

Ta ce tana roƙon ministan da sunan Allah da ya haƙura da sayar da filin ga wasu mutane. "Ina roƙon ka da ka ji kokenmu, ka amsa mana buƙatarmu," in ji ta a faifan bidiyon.

Jerin filayen da ake taƙaddama a kai

  • Jabi Lake Parks: Rahotanni na cewa an sayar wa kamfanoni masu zaman kansu domin mayar da wurin shaƙatawar na kuɗi.
  • Filin shaƙatawa na Zone 6: Rahotanni sun ce za a mayar da wurin zuwa rukunin gidaje.
  • Filin shaƙatawa a Maitama: Shi ma wannan rahotanni na cewa za a mayar da shi.
  • Lambu a Guzape: Wannan ma rahotanni na cewa za a mayar da shi zuwa rukunin gidaje.

Martanin Nyesom Wike

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lere Olayinka, babban mai ba ministan Abuja shawara ne kan hulɗa da jama'a da kafofin sadarwa na zamani, ya ce ba sayar da filin wurin aka yi ba, gyara za a yi domin a bunƙasa shi.

A cewarsa, hukumar babban birnin tarayya Abuja tun a bara ta fara yunƙurin bunƙasa wajen da ma sauran wurare domin su yi daidai da zamani, domin a cewarsa hakan ne zai jawo masu zuwa ziyara da yawon buɗe ido.

"Babu wannan maganar ta wai za a sayar da filaye a wurin shaƙatawa na Jabi Lake. A watan Fabrairu ne hukumar babban birnin tarayya ta shiga yarjejeniya da kamfanonin Suburban Broadband Limited da Akida Hills Limited domin bunƙasa wajen domin ya zama wajen yawon buɗe ido na zamani," in ji shi.

Ya ce a zahiri aka sa hannu kan yarjejeniyar ba a ɓoye ba, "kawai akwai mutanen da ba sa so a riƙa bunƙasa wurare. Sun fi so kawai a bar su su cigaba da zama a yadda suke ba tare da samar da wani ci gaba ba," in ji Lere Olayinka a tattaunawarsa da BBC Hausa.

Ya ƙara da cewa burin gwamnati shi ne a mayar wajen ya zama wata babbar cibiyar yawon buɗe ido da shaƙatawa da za ta yi daidai da zamani, ta yadda da za a riƙa zuwa daga ƙasashen duniya baki ɗaya domin nishaɗi.

Muna bunƙasa Abuja ne - Wike

"Ba wajen kaɗai muke yunƙurin bunƙasawa ba. Ka je yankin babbar ƙofar Abuja, za ka ga aikace-aikacen da ake yi. Wurare irin su Jabi Lake bai kamata a bar su a yadda suke a baya ba. Suna buƙatar a bunƙasa su domin su yi kyau su yi daidai da zamani," in ji shi.

A game da wani zargin da ake yi cewa gwamnatin tana yanka wuraren da ake kira 'green areas' wato koren wurare da aka tanada domin kwalliya da ƙawata Abuja, Olayinka ya ce dama can gwamnati ta tanade su, kuma za ta iya gyara taswirar domin a yi wani abun daban.

"Ai dama fulotai na gwamnati ne. Idan ta ware wasu wurare domin ƙawata birni, sai ya kasance ci gaba ya riski wurin, gwamnati za ta iya cewa bari ta rage faɗin wurin, sai a ɗan ɗiba a yi wani abu daban a wajen," in ji shi.

A game da wuraren da aka mayar na kasuwanci a yankin Maitama da Wuse, Olayinka ya ce asali masu wurin ne suka samu sahalewar gwamnati a matsayin gidaje.

"Amma sai suka fara mayar da wuraren suna zama na kasuwanci. To maimakon gwamnati ta ce sun yi laifi, sai kawai ta ce masu wurin su zo a mayar musu da shi ya zama na kasuwanci a hukumance. Abin da aka yi ke nan," in ji shi.