BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Me ya sa mutane ke rububin taɓa dutaen Hajaral-Aswad?
"Akwai Hadisin da ya tabbata cewa Manzo Allah (SAW) ya ce asalin Dutsen ya zo ne daga Aljannah tun zamanin Sayyidina Ibrahim (AS) da Isma'il (AS) a lokacin da za su gina ɗakin Ka'aba."
Arsenal na harin Rogers, PSG da Liverpool na gogayya kan Diomande
Arsenal za ta dage kan zawarcin ɗanwasan gaba na Aston Villa da Ingila Morgan Rogers, yayin da Liverpool da PSG ke tattaunawa da ɗanwasan gaba na gefe na RB Leipzig da Ivory Coast Yan Diomande.
Me ya sa ministocin Tinubu suka kasa samun takara a zaɓukan fitar da gwani?
Aƙalla ministocin gwamnatin Tinubu biyar ne suka ajiye aiki da nufin tsayawa takarar kujeru daban-daban a zaɓen 2027 da ke tafe.
Kasashen da darajar kuɗaɗensu suka faɗi da waɗanda nasu suka tashi sanadiyyar yaƙin Iran
Rikicin ya girgiza kasuwannin duniya, inda kuɗaɗe suka rabu gida uku: wasu sun karye, wasu sun tashi, yayin da wasu kuma ke faɗuwa da tashi.
Manoman Najeriya sun yi barazanar daina noman kayan abinci sai na sayarwa
Wannan dai na da nasaba da karyewar farashin kayan a kasuwanni, yayin da kayan da ake noman da su kamar taki da maganin kwari kuma farashinsu ke hawa.
Iran ta sake gargaɗin Amurka kan sabunta hare-hare a ƙasar
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 26 ga watan Mayun 2026
Abin da ya sa ake yin wasu ayyukan ibada a lokacin aikin Hajji
Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.
Su wane ne ƙungiyoyin Premier da suka samu tikitin gasar Zakarun Turai ta baɗi?
Liverpool da Bournemouth da Sunderland da kuma Brighton duk sun samu gurbin buga gasar zakarun Turai a ranar karshe ta rufe Premier League's final day.
Wane ne zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC?
A yau ne ake sa ran bayyana sakamakon zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ADC domin sanin wanda zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen shekarar 2027 da zai kara da Shugaba Bola Tinubu.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 27 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 26 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 26 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 26 Mayu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, AC Milan ta kori kociyanta Massimiliano Allegri
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 25 zuwa Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.
Liverpool na son maye gurbin Salah da Diomande, Arsenal na son Alvarez
Tottenham ta koma zawarcin Savinho, Yan Diomande ne kan gaba a waɗanda Liverpool ke nema don maye gurbin Salah, yayin da Barcelona ke son saye Rashford, Arsenal kuwa za ta nemi Alvarez.
United da Arsenal da PSG na son Fernandes, AC Milan za ta riƙe Modric
Man United ta tuntuɓi West Ham ko za ta sayar mata da ɗan wasanta na tsakiya Mateus Fernandes, na Portugal, wanda Arsenal da PSG ma ke so, ita kuwa AC Milan na son riƙe Luka Modric, mai shekara 40 ƙarin shekara ɗaya.
Arsenal ta lashe Premier karon farko cikin shekara 22
Arsenal da ta jera zuwa ta biyu sau uku a baya, a yanzu ta yi nasarar lashe gasar bayan shekara 22
Premier League: West Ham ta faɗa Championship, Tottenham ta tsallake rijiya da baya
Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Alhassan Ɗantata: Ɗan Najeriya da ya je aikin Hajji a jirgin ruwa
Masana tarihi sun ce Alhaji Alhassan Ɗantata shi ne fitaccen ɗan Najeriya na biyu da ya je aikin Hajji a jirgin ruwa, bayan Sarkin Katsina, Muhammadu Dikko a 1921, abin da ya ɗauki hankalin duniya a zamanin.
Abubuwan da suka kamata Musulmi su yi a ranar Arfa
''Kamar yadda a cikin darare babu daren da ya kai na laylatul qadar falala, haka ma a cikin ranaku babu wadda ta kai ranar Arfa falala da daraja a wajen Allah'', in ji Sheikh Pantami.
Ƙalubale 7 da INEC za ta iya fuskanta a zaɓen Najeriya na 2027
Awwal Musa Rafsanjani, shugaban gamayyar ƙungiyoyin da ke sanya idanu a zaɓukan Najeriya, Transition Mornitoring Groups (TMG), ya bayyana wa BBC wasu daga cikin ƙalubalen da hukumar INEC ɗin za ta fukanta a zaɓen an 2027.
Shin Mahmoud Ahmadinejad zai zama raba-gardama ne a yaƙin Iran?
Shin me ya sa Amurka da Isra'ila za su yi amfani da mutumin da tsawon lokaci yake adawa da su?
Yadda ake samun koma-baya a ilimin 'ya'ya mata a Nijar
"Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa a cikin kashi 64 zuwa 83 cikin 100 na daliban da suke mata ne da ke karatu a matakin farko na firamare, da kyar ake samun kashi 20 cikin 100 a cikinsu da ke ci gaba da karatu.
Me ake ciki kan yiwuwar cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka?
Kafar yaɗa labarai ta Axios ta ruwaito cewa wani jami'in Amurka na cewa Tehran da Washington sun kusa ƙulla yarjejeniya da za ta tsaiwata yarjejeniyar tsagaita wuta da kwana 60, a buɗe Mashigar Hormuz sanan a bai wa Iran damar sayar da mai tare kuma da tattaunawa kan taƙaita shirin Nukiliyar Iran da kuma kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon.
Jihohin da Tinubu ya fi samun ƙuri'a a zaɓen fitar da gwani
''Zaɓen da aka yi a dubban rumfuna ya samu miliyan takwas da 'yan kai, to sai ga shi wanda aka ce an yi a ɗaiɗaikun wurare a ce an samu ƙuri'a fiye da miliyan 10, gaskiya za a yi shakku da tababa a kai"
Hajj 2026: Yadda ake yin aikin Hajji
Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.
Sojoji sun yi gargaɗin samun hare-haren ƙunar baƙin wake lokacin bukukuwan sallah
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 25 ga watan Mayun 2026
Kasashe 7 da suka fi ƙanƙanta a duniya
Akwai wasu ƙasashen duniya waɗanda saboda ƙanƙantar su, mutum zai iya zagaye su a cikin ƙanƙanin lokaci, hatta a cikin kwana ɗaya kacal.
Ko Najeriya ta shirya wa zuwan cutar Ebola?
Bazuwar cutar na ƙara janyo fargaba a tsakanin sauran ƙasashen Afirka musamman ganin cewa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fito a kwanakin baya ta bayyana cewa zuwa yanzu babu allurar rigakafin sabon nau'in cutar.
Wane ne Sadiqu, jakadan Shekau da ake zargi da sace ɗalibai a Oyo?
Sadiqu ya samu damar kafa sansaninsa ne a dajin Alawa, inda daga baya ya koma dajin Kainji da ke da hanya har zuwa gandun dajin jihar Oyo.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































