Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Ramos, Aurier, Rojo, Yedlin, Rose, Dalot, Van Aanholt, Mustafi, Dzeko

Sergio Ramos

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan baya na Spaniya Sergio Ramos mai shekara 34 ya shirya tsaf domin barin Real Madrid kumaya fi son komawa Manchester United.(Mirror)

Serge Aurier, dan wasan baya dan kasar Ivory Coast mai shekara 28 na fuskantar kalubale a Tottenham bayan da ya nuna fusatarsa yayin wasan da Spurs ta buga da Liverpool. Aurier ya nuna bacin ransa bayan da aka sauya shi kuma ya bar filin wasan kai tsaye ba tare da sauran abokan wasansa ba. (Mail)

Dan wasan baya na Argentina, Marcos Rojo mai shekara 30 ya shirya barin Manchester United domin ya sami damar komawa Boca Juniors ta Argentina. (Sky Sports)

Dan wasan baya na Newcastle da Amurka DeAndre Yedlin mai shekara 27 zai koma Galatasaray kuma zai tafi Turkiyya domin a duba lafiyarsa bayan kungiyoyin biyu sun amince kan kudaden da za a biya. (ESPN)

Dan wasan baya na Tottenham Danny Rose na iya fuskantar cikas kan burinsa na komawa kungiyar Trabzonspor ta Turkiyya bayan da kungiyar ta ce saboda dokokin yaki da annobar korona, zai yi wuya a kamamla cinikin sayen dan wasan. (Talksport)

AC Milan na son dauko Diogo Dalot, dan wasan baya na Manchester Unitedkan fam miliyan 15. (Sun)

Arsenal na kwadayin dauko Patrick van Aanholt, dan wasan baya na Crystal Palace da kasar Netherlands mai shekara 30 da haihuwa. (Mirror)

Liverpool na sha'awar Shkodran Mustafi, dan wasan Arsenal da Jamus mai shekara 28. (Evening Standard)

Dan wasan baya na Manchester United Brandon Williams mai shekra 20 na iya barin kungiyar amma a matsayin dan aro inji Ole Gunnar Solskjaer. (Manutd.com)

Manchester City ta ki amincewa da damar da ta samu ta sake sayo Edin Dzeko, dan wasan gaba mai shekara 34 daga Roma.(Goal)