Jihohi 7 da Tinubu zai fi fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu
Bayanan hoto, Shugaba Bola Ahmad Tinubu
    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da zaɓen shugaban Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara matsowa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar ƙalubalen siyasa a wasu jihohi da ka iya zama masa tarnaki, yayin da yake neman samun nasara domin yin wa'adi na biyu a zaɓen mai zuwa.

Ko da yake jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara faɗaɗa tasirinta a siyasar ƙasar, wasu jihohi na iya zama ƙalubale ga Tinubu, musamman idan aka yi la'akari da tarihin siyasarsu, matsalolin da suke fuskanta da dai sauransu.

Wani rahoto na Cibiyar Nazarin Zaɓe ta International Republican Institute (IRI) ya bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da rashin amincewar jama'a ga 'yan siyasa na daga cikin manyan abubuwan da za su iya tantance yadda zaɓen 2027 zai kasance.

Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja da ke Najeriya, ya yi tsokaci kan waɗannan jihohi da kuma dalilan da za su iya sa Shugaba Tinubu ya fuskanci ƙalubale a cikinsu.

1. Kano: Tasirin Kwankwaso

Jihar Kano na daga cikin jihohin da za su zama babban ƙalubale ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, idan aka yi la'akari da tasirin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a yanzu yake mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC.

A cewar Farfesa Abubakar Kari, Kano na da tarihin zaɓen ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa, sabanin jam'iyyar da ke mulki a matakin tarayya. Ya ce jihar na da wayayyun masu zaɓe masu, abin da ya sa ake wa siyasar jihar taken "Siyasar Kano, iya mata sai ɗan Kano".

A cewarsa, "Kanawa da dama na korafin cewa tun bayan da Shugaba Tinubu ya samu nasara a zaɓen 2023, bai aiwatar da wani babban aiki na a zo a gani a jihar ba da za a ce sun amfana da gwamnatinsa."

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Kwankwaso ya samu ƙuri'u 953,179 a Kano, yayin da Tinubu na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 513,846.

2. Legas: Karfin Peter Obi

Duk da cewa Legas ce mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, amma sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya nuna cewa ita ma jihar mace ce da ciki, ba a san abin da za ta haifa ba.

Masanin siyasa, Farfesa Abubakar Kari, na ganin cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ka iya taimaka wa Obi, tare da haifar wa Shugaba Tinubu cikas a Legas, shi ne kasancewar 'yan asalin Kudu maso Gabas da dama a jihar, yankin da Obi ya fito.

"Waɗannan mutane na daga cikin al'ummomin da ke zaune suna gudanar da harkokinsu na kasuwanci da sauran ayyukan yau da kullum a Legas. Kuma a duk lokacin zaɓe, sukan fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaɓar ɗan uwansu, kuma mun ga hakan a zaɓen 2023," in ji shi.

A zaɓen na 2023, Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ya samu ƙuri'u 582,454 a jihar, inda ya doke Tinubu na jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 572,606.

3. Adamawa: Tasirin Atiku

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A jihar Adamawa, babban abin dubawa shi ne tasirin tsohon mataimakin shugaban ƙasar, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya fito daga jihar.

Ko da yake gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, wanda a baya yake jam'iyyar PDP, ya fice daga jam'iyyar ya koma APC ta Shugaba Tinubu, ba za a iya tantance irin tasirin da sauya shekar tasa zai yi ga ƙoƙarin Tinubu na samun nasara a jihar ba.

Sanannen abu shi ne cewa tun lokacin da Atiku Abubakar, babban abokin hamayyar Tinubu, ya fara takarar shugaban ƙasa, bai taɓa rasa jiharsa ta asali a zaɓen shugaban ƙasa ba.

Wani abu da kuma zai iya zama ƙalubale ga Shugaba Tinubu a jihar shi ne kasancewar duka manyan 'yan siyasar da ke takarar shugaban ƙasar suna da tasirinsu a Adamawa, ciki har da Peter Obi na jam'iyyar NDC, wanda ke da goyon baya a kudancin jihar.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a Adamawa dai, Atiku ne ya lashe jihar da ƙuri'u 417,611, yayin da Tinubu ya samu ƙuri'u 182,881, sannan Peter Obi ya samu ƙuri'u 105,648.

4. Kaduna: Ci gaba da tsare El-Rufai

Jihar Kaduna, wadda ke matsayi na uku wajen yawan ƙuri'u a Najeriya, na daga cikin jihohin da za su iya zama ƙalubale ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

A cewar masanin, abubuwa da yawa za su iya zamar wa shugaban kalubale, ciki har da ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai wanda ke da farin jini a wajen mutane da dama, hakan na iya sa magoya bayansa nuna fushinsu ta hanyar fitar farin ɗango da kuma zaɓen 'yan takarar da ba na APC ba.

Dama kuma ko a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar na PDP ya lashe Kaduna da ƙuri'u 554,360, yayin da Tinubu ya samu 399,293, Peter Obi na Labour Party kuma ya samu 294,494.

Masanin ya ce ko da yake ana ganin jam'iyyar APC na farfado da tasirinta a kudancin jihar, duk da haka batun addini ba zai sa su ki zabar kirista, wato Peter Obi su zabi Bola Ahmed Tinubu musulmi, kuma mataimakinsa musulmi ba.

5. Zamfara: Matsalar Tsaro

A jihar Zamfara, babban abin dubawa shi ne yadda matsalar tsaro za ta iya tasiri ga zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Hare-haren 'yan bindiga, sace mutane da kuma korafe-korafen jama'a kan yadda ake yaƙi da rashin tsaro na daga cikin batutuwan da suka fi damun masu zaɓe.

"Babban abin shi ne Shugaba Tinubu ne shugaban ƙasa, don haka alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama'ar Zamfara ya rataya ne a wuyansa. Idan har ya gaza, jama'a za su yi wa kansu alkalanci," in ji masanin.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe Zamfara da ƙuri'u 298,396, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu 193,978.

Sai dai matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da matsalar tsaro da ke ƙara ta'azzara na iya zama manyan ƙalubale ga Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

6. Bauchi: Tasirin Bala Mohammed da ƙarfin APM

A jihar Bauchi, babban abin da zai ja hankali shi ne tasirin Gwamna Bala Mohammed da kuma ƙarfin jam'iyyar da yake cikinta, musamman yadda siyasar jihar za ta kasance gabanin zaɓen 2027.

A yanzu haka, jam'iyyar APM, wadda ke da ɗan takarar shugaban ƙasa nata, wato Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, na daga cikin jam'iyyun da za a sanya ido kan yadda za su taka rawa a zaɓen mai zuwa.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 426,607 a jihar, yayin da Tinubu na APC ya samu ƙuri'u 316,694.

Bauchi na da muhimmanci a siyasar 2027 saboda, a cewar Farfesa Abubakar Kari, sau da dama sauran jihohin Arewa maso Gabas, musamman Gombe, na la'akari da alkiblar siyasar Bauchi wajen tsara matsayinsu. Wannan na iya sa yadda siyasar jihar za ta kasance ya zama abin lura gabanin zaɓen mai zuwa.

7. Jihohin kudu maso gabas

Jihohin Kudu maso Gabas na daga cikin yankunan da za su iya zama ƙalubale ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A zaɓen 2023, Obi wanda ɗan yankin ne, ya lashe dukkan jihohin yankin guda biyar, inda ya samu ƙuri'u 327,095 a Abia, 584,621 a Anambra, 259,738 a Ebonyi, 428,640 a Enugu da kuma 360,495 a Imo. Jimillar ƙuri'un da ya samu a yankin ta kai kusan miliyan biyu, yayin da Tinubu na APC ya samu ƙuri'u 127,607 kacal a jihohin biyar.

Haka kuma, a zaɓukan shugaban ƙasa da suka gabata, Kudu maso Gabata, al'ummar yankin ba sa zabar APC.