Jose Mourinho ya yi amai ya lashe

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce burin da ya dauka na zama cikin kungiyoyin hudun farko a gasar Premier a karshen Disamba ya sauya.

Mourinho ya yi fatan ne kafin karawar da United ta tashi babu ci da Crystal Palace a ranar 24 ga watan Nuwamba.

Haka kuma bayan da kungiyar ta buga 2-2 a gidan Southampton, ya sa ta koma ta bakwai, ba ta cikin jerin wadanda za su buga gasar Champions League a wannan matakin.

Rabon da United ta yi nasara tun 3 ga watan Nuwamba da ta ci 2-1 a gidan Bournemouth.

Manchester United za ta karbi bakuncin Arsenal a ranar Laraba a gasar Premier wasan mako na 15.

Wasu karin labaran da za ku karanta