KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 23/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 23/10/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa
  • Pantami
  • Mai zane
  • Atiku

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Imam Saleh

  1. Shugaba Macron na Faransa ya soke ziyarar da zai kai Najeriya

    .

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Najeriya da Senegal a watan Oktoba, sakamakon rikice-rikicen zamantakewa da zanga-zangar da ake fama da su a ƙasarsa.

    Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin Faransa na farfaɗo da dangantakarta ta tarihi da ƙasashen Afirka ta Yamma, bayan tabarbarewar alaƙarta da ƙasashen Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES).

    An zaɓi Najeriya, ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka, da Senegal a matsayin muhimman wuraren da Macron zai ziyarta domin ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Faransa da yankin.

    Rahotanni sun nuna cewa Macron ya yanke shawarar mayar da hankali kan matsalolin cikin gida sakamakon halin da ake ciki a Faransa.

    Sai dai, gwamnatin Faransa ba ta bayyana lokacin da za a iya sake tsara ziyarar ba.

  2. Ana zargin wani basarake da tilasta wa ƴan mata gwajin budurci a Najeriya

    Hukumomi a Najeriya na gudanar da bincike kan zargin wani basaraken gargajiya a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar, ya umarci a yi wa wasu ɗalibai mata 'yan makarantar sakandare gwajin budurci, domin a ba su tallafin karatu da littattafan rubutu.

    Ma'aikatar Ilimi ta bayyana zarge-zargen a matsayin abin takaici da tayar da hankali, lokacin da aka sanar da ba da umarnin yi wa daliban mata 16 wannan gwajin.

    Ta yi kira ga makarantu a faɗin jihar Rivers da su ƙarfafa matakan kare haƙƙoƙin yara da kuma tsaron ɗalibai.

    Ko da yake sarakunan gargajiya na da babban tasiri da iko a cikin al'umma, irin wannan lamari ba kasafai yake faruwa ba a jihar Rivers.

  3. Ukraine ta ce sojojinta na fama da matsalar sadarwa a filin daga

    Jami’an Ukraine sun ce har yanzu su na fuskantar matsalar na'urar sadarwa ta tauraron dan adam din kamfanin SpaceX na Elon Musk da sojoji ke amfani da ita.

    A cewarsu, jiragen yaƙi marasa matuƙa na ci gaba da fuskantar matsala da rashin gudu idan sun tashi, lamarin da ke kawo cikas ga sojojin Ukraine.

    Wakilin BBC ya ce abin da ake nufi shi ne da zarar an harba jiragen, su na gudun kilomita 160 cikin sa'a guda sai sigina ta dauke, lamarin da ke sanya ko dai su gagara matsawa gaba ko kuma su fado kasa.

    Ukraine ta kuma ce an samu matsaloli da Starlink, wanda shi ne tsarin intanet na tauraron dan adam da ake amfani da shi ga fararen hula.

  4. EU ta nuna damuwa kan zargin Rasha da kai hari Romania

    Shugabar hukumar gudawar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce tana cikin damuwa bayan da aka zargi Rasha da kai harin jirgi maras matuƙi da ya haddasa nutsewar wani jirgin ruwa na fararen hula kusa da ƙasar Romania.

    Von der Leyen ta bayyana lamarin a matsayin wani sabon mataki na ƙara tsananta rikici da Rasha ke yi a yankin tekun Bahar al-Aswad, wanda a cewarta ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

    Jirgin ruwan da harin ya rutsa da shi na ɗauke da ma’aikata daga ƙasashen Ukraine da Azerbaijan.

    Ƙawancen ƙungiyar tsaro ta NATO, ya sanar da tura ƙarin sojoji da ma'aikatan ceto yankin tekun, sakamakon ƙaruwar hare-haren da ake zargin Rasha na kai wa jiragen kasuwanci, waɗanda suka yi sanadin asarar rayuka a baya-bayan nan.

  5. 'Mutum 7 sun mutu sakamakon harbe-harbe a cocin Jordan'

    Gidan talabijin na ƙasar Jordan ya ruwaito cewa aƙalla mutum bakwai sun mutu, yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon harbe-harbe da aka yi a cikin wata coci a ƙasar.

    An ce wasu mutum biyu ɗauke da makamai ne suka zo a cikin mota sannan suka buɗe wuta kan mutanen da ke halartar jana'iza a cocin ƙauyen Hammoud, da ke yankin tsakiyar Karak.

    Hukumomi na ci gaba da bibiyar waɗanda ake zargi da kai harin, ana kuma ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.

  6. Najeriya ta tura sojojinta zuwa Indiya don samun horon yaƙi

    Sojoji

    Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta fara tura jami’anta 600 zuwa ƙasar Indiya domin samun horo na musamman kan yaƙi a dazuka da yankuna masu duwatsu.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Kanal Appolonia Anele ta fitar ta ce rundunar ta ɗauki matakin ne da nufin ƙara ƙwarewar sojojin wajen gudanar da aiki a wurare masu wahalar shiga tare da ƙarfafa rundunar wajen kare cikakken ikon ƙasar Najeriya.

    Sanarwar ta ce kashi na farko na jami’ai 300 sun tashi daga filin jirgin sama na Abuja a ranar Alhamis, 22 ga Oktoban 2026, cikin jiragen saman Indiya guda biyu.

    Sojojin Najeriya

    ''Ana sa ran horon zai bai wa jami’an sojin ƙwarewa ta zamani kan yaƙi a dazuka da tsaunuka da inganta ƙwarewa a fagen aiki, tare da ƙarfafa ƙarfinsu wajen hana masu aikata laifuka samun mafaka a wuraren da masu wahalar shiga'', in ji sanarwar.

    Sojojin sun ce nan gaba ne za a ci gaba da jigilar sauran dakarun zuwa Najeriya.

  7. Sojojin Isra'ila biyu sun mutu bayan harbe-harben Hebron

    sojojin Isra'ila

    Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa sojojin ƙasar biyu sun mutu sakamakon raunukan da suka samu a harbe-harben da aka samu yau da safe a birnin Hebron.

    Jami'an sojin Isra'ila sun kuma ce an harbe tare da kashe wasu mutane biyu da ake zargin Falasɗinawa a yayin harin.

    Sojojin Isra'ila biyar ne suka jikkata a harbe-harben da suka faru a birnin Hebron da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

    Har yanzu dai ba a fitar da wani bayani kan halin da sauran sojoji ukun da suka samu raunuka suke ciki ba.

    Lamarin ya faru ne a wani shingen binciken jami'an tsaro da ke kofar shiga birnin Hebron.

  8. Ya kamata ƴansiyasa su daina yaudarar ƴan Najeriya - Sarkin Katsina

    Sarkin Katsina

    Sarkin Katsina, Abdulmumini Usman, ya gargadi ƴansiyasa da su guji yi wa ƴan Najeriya alƙawuran da ba su da niyyar cikawa.

    Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Abdulaziz Yari, Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu da tawagarsa da suka kai masa ziyara fadarsa.

    Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin Arewa maso Yamma.

    A cikin jawabin Sarkin ya kuma koka kan yadda aka samu durƙushewar masana’antu a arewa maso yamma waɗanda a baya suke samar da ayyukan yi da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin arewacin Najeriya.

    A cewarsa, ya zama dole shugabannin siyasa su fahimci cewa shugabanci nauyi ne na yi wa al’umma hidima cikin riƙon amana da gaskiya.

    Ya kuma soki yadda ƴansiyasa suka mayar da hankali kan sukar junansu a maimakon hidimta wa al’umma inda ya ce “siyasa ba hauka ba ce, tana nufin jawo mutane su fahimci ko su karɓi ra'ayinka.”

  9. Atiku ya soki Tinubu kan ''bai wa hotunansa tsaro a Kaduna''

    Atiku Abubakar

    Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya soki shugaban kasar Bola Tinubu kan abin da ya kira bai wa allunan tallansa na siyasa tsaro fiye da yan Najeriya.

    Atiku ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallaf a shafinsa na sada zumunta don yin tsokaci kan labarin da wata jaridar ƙasar ta wallafa game da yadda ta ce jami'an tsaro na bai wa allunan hotunan tallan Tinubu tsaro a Kaduna gabanin taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a jihar gobe Asabar.

    Jaridar ta ce an ajiye jami'an tsaro domin bai wa allunan hotunan Tinubu tsaro a birnin Kaduna gabanin taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen.

    Atiku Abubakar - wanda ya sake wallafa labarin a shafin nasa - ya ƙara da tsokacin cewa ƴanbindiga na far wa ƙauyuka da garuruwa yayin da iyalai ke rayuwa cikin fargabar rashin tsaro, amma jami'an tsaro na bai wa hotunan Tinubu tsaro.

    ''Allunan hotunanka na samun tsaron da miliyoyin yan Najeriya ke fatan samu'', in ji shi.

    Ɗantakarar shugaban ƙasar na ADC ya nemi Shugaba Tinubu ya kare rayukan yan Najeriyar kamar yadda ya ce yana kare hotunansa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Dalilai 5 da suka hana shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

    Fitila

    Daga gidaje zuwa manyan masana'antu, daga ƙananan ƴan kasuwa zuwa asibitoci da makarantu, matsalar wutar lantarki na ci gaba da shafar kusan kowane fanni na rayuwa a Najeriya.

    Yayin da wasu ƴan kasuwa ke kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sayen man fetur domin janareta, wasu masana'antu na fama da tsadar samar da kayayyaki, lamarin da ke iya shafar farashinsu a kasuwa.

    A gidaje kuma, rashin ingantacciyar wutar lantarki na ƙara jefa jama'a cikin wahalhalun rayuwa da haifar musu da cikas a harkokinsu na yau da kullum.

    A asibitoci, da makarantu da sauran muhimman cibiyoyi, samun wutar lantarki mai ɗorewa na da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata, kuma ya kan taimaka wajen ceton rayukan al'umma.

    Duk wata gwamnati da aka yi a baya a Najeriya, ta yi alkawarin shawo kan wannan matsala, sai dai har kawo yanzu, tana nan daram, wasu ma na cewa tana sake taɓarɓarewa.

  11. 'Tinubu na harin miliyoyin ƙuri'un arewacin Najeriya'

    Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da shugabannin jam'iyyar APC, za su ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓensa a jihar Kaduna ranar Asabar, yayin da jam'iyyar mai mulki ke ƙara zage dantse wajen neman goyon baya a arewacin ƙasar, yankin da ke da masu rajistar ƙuri'a miliyan 56.01 cikin jimillar masu rajista miliyan 103.43 a faɗin Najeriya.

    Ana sa ran gwamnoni 31 da sauran manyan jiga-jigan jam'iyyar za su halarci taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen, inda APC ke fatan cin gajiyar abin da shugabanninta suka bayyana a matsayin karuwar goyon baya daga masu ruwa da tsaki da masu kaɗa ƙuri'a a Arewacin Najeriya domin tabbatar da nasarar Tinubu a 2027.

    Jam'iyyar ta kuma sanya wa kanta burin tattara ƙuri'u miliyan 40 ta hanyar wayar da kan jama'a daga tushe, musamman mata, inda shugabanninta ke nuna ƙwarin gwiwar cewa 'yan Najeriya za su sake ba shugaban ƙasar wa'adi na biyu.

    Sai dai jam'iyyun adawa sun ƙalubalanci ƙwarin gwiwar na APC, suna masu cewa matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro da ake fama da su na iya kawo cikas ga yunƙurin sake zaɓen Tinubu.

    Masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun dage cewa 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar da kuma mabiya addinai daban-daban a shirye suke su kaɗa ƙuri'ar kawar da jam'iyyar mai mulki daga karagar mulki.

  12. 'Mutanen gari sun tunkari ƴanbindiga tare da kashe 30 a Zamfara'

    Bindigogi

    Mazauna ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun ce sun kashe sama da ƴanbindiga 30 a wani artabu da ya ɗauki kwanaki uku bayan da maharan ɗauke da makamai suka kai wa al'ummar yankin hari.

    Mazauna ƙauyen sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa maharan, waɗanda aka ruwaito sun je a kan babura, sun kewaye ƙauyen tare da buɗe wuta kan mutanen garin.

    Mutanen sun ce ƴanbindigar sun kewaye ƙauyen da nufin kai masa hari, inda suka yi ƙoƙarin kare garinsu.

    Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun isa ƙauyen ne lokacin da wasu daga cikin mazauna ƙauyen suka tafi gonakinsu domin girbe amfanin gona.

    “Kafin mu ankara da abin da ke faruwa, 'yan bindigar sun riga sun kewaye ƙauyen daga kowane ɓangare, ɗauke da mutum uku a kan kowane babur ,” in ji shi.

    Mutumin ya ce dama wasu daga cikin mutanen garin na cikin shirinsu, lamarin da ya sa suka fuskance su domin kare kansa daga zama ƴangudun hijira.

    ''Mun kashe kusan yanbindiga 30 a wannan artabu,'' kamar yadda ya shaida wa Daily Trust.

    Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa a shirye take wajen tallafa wa mutanen ƙauyen wajen ba su kariya.

  13. 'Amurka ta kashe dala biliyan 11 wajen kare Isra'ila'

    Abbas Araqchi

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya zargi Amurka da kashe dala biliyan 11 daga kuɗaɗen masu biyan haraji wajen tallafa wa tsarin kariyar makamai masu linzami na Isra'ila a cikin shekaru uku da suka gabata.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Araqchi ya kuma yi ikirarin cewa Amurka ta harba makaman kariya masu linzami fiye da adadin da Isra'ila da kanta ta harba domin kare ƙasar.

    A ƙarshen saƙonsa, ministan ya yi tsokaci kan alaƙar da ke tsakanin Amurka da Isra'ila, inda ya ce: "Wannan ba alaƙa ce ta cin moriyar juna ba, alaƙa ce ta dogaro da wani ɓangare kan ɗayan."

  14. An ji ƙarar gargaɗin hare-haren makaman linzami a Saudiyya

    Jirgin yaƙi

    Hukumar kare fararen hula ta Saudiyya ta fitar da gargaɗi da safiyar Juma'a ga mazauna babban birnin ƙasar, Riyadh, inda ta buƙaci su koma wurare masu aminci domin kare kansu daga hare-haren da ake sa ran za su iya faruwa nan ba da jimawa ba.

    Sai dai bayan ƴan mintoci kaɗan hukumar ta cire wannan gargaɗi.

    A lokaci guda kuma, ta wallafa wani saƙo a shafinta na sada zumunta tana mai cewa haramun ne ɗaukar bidiyo ko yaɗa hotuna da bidiyon tsarin kariya daga hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    A halin da ake ciki, wasu kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa an ji ƙarar fashewa a birnin Riyadh, amma har yanzu babu wani cikakken bayani da hukumomi ko wasu majiyoyi masu zaman kansu suka tabbatar game da lamarin.

  15. Tinubu ya bai wa Yusuf Bichi tsohon shugaban DSS muƙami

    DSS

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NISS.

    Cikin wata sanarwa da daraktar cibiyar, Lilian Omo-Odigwe ta fitar ta ce naɗin zai fara aiki ne daga ranar 22 ga Oktoban 2026, na wa’adin farko na shekara huɗu, kamar yadda dokar kafa cibiyar ta tanada.

    Yusuf Bichi zai gaji A.A. Gadzama, wanda ya jagoranci kwamitin kafin wannan lokaci.

    A shekarar 2024 ne Mr Bichi ya yi ritaya daga shugabancin hukumar DSS, wada ya kwashe gomman shekaru yana aiki da ita.

  16. Amurka ba ta sauran iko da mashigar Hormuz - Iran

    Ali Azmaei, kwamandan rundunar sojojin ruwa ta Revolutionary Guards ta Iran, ya yi iƙirarin cewa "Amurkawa sun nesanta daga Tekun Fasha."

    Cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce: "A yau Amurkawa ba sa yankin Tekun Fasha, haka kuma sun bayar da tazarar kilomita 600 zuwa 700 daga mashigar Hormuz, kuma ba a ganin jiragensu a wannan yanki."

    Ali Azmaei ya ƙara da cewa: "Amurka ba ta da sauran matsayi a mashigar ruwa ta Hormuz."

    Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan Amurka ta umarci ƴanƙasarta su fice daga yankin Tekun Fasha.

    Sa'o'i kaɗan da suka gabata, shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Iran da ƙoƙarin tayar da farashin ɗanyen mai gadan-gadan kafin zaɓen tsakiyar wa'adin mulki na Amurka, ta hanyar "ƙirƙirar labaran ƙarya" game da fashewar nakiya da kuma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

    Shugaba Trump ya ce a yanzu ana jigilar mai ta mashigar Hormuz fiye da yadda ake yi kafin yaƙin, kuma saboda haka ne Iran ke neman amfani da duk wata hanya domin ta ɗaga farashin mai.

    A yau farashin gangar ɗanyen mai ta Brent ya haura dala 113, wanda shi ne mafi girman farashinsa cikin watanni biyar da suka gabata.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawi muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta