Iran ta gargaɗi Isra'ila ta fice daga Lebanon
Esmail Ghaani, kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci reshen ƙasashen ƙetare, ya gargadi Isra'ila cewa sojojinta su fice daga ƙasar Lebanon.
A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa nma X Mista Qaani ya ce: "Idan ba ku janye a yau ba don ra'ayin kan ku, gobe za a tilasta muku ku gudu a wulaƙance cikin ƙasƙanci."
Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Labanon wani ɓangare ne na yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, kuma a ko da yaushe gwamnatin Iran ta ɗauki tabbatar da shi a matsayin wani muhimmin sharaɗi na wannan yarjejeniyar.
To sai dai kuma ana ci gaba da arangama tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah, kuma firaministan ƙasar Isra'ila Benyamin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa a cikin ƴan kwanakin nan domin mayar da martani kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka inda ya ce: "Za mu ci gaba da zama a cikin yankin tsaro a kudancin Labanon matuƙar akwai buƙatar yin hakan, a matsayina na firaministan Isra'ila, ina mai jaddada hakan kuma babu abin da zai canza hakan.''