Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda dakarun Israila suka ci zarafin masu fafutuka da ke goyon bayan Falasɗinawa
Masu fafutuka da aka tasa ƙeyarsu gida waɗanda ke goyon bayan Falasɗinawa bayan da dakarun Israila suka kama jerin gwanon jiragen ruwan da ke ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza sun yi zargin cewa an ci zarafinsu yayin da ake tsare da su.
Kanada ta ce ta samu bayanai kan "mummunan cin zarafi" da ake yi wa ƴan ƙasarta , yayin da Jamus da Sifaniya suka tabbatar da cewa wasu ƴan ƙasashensu sun samu raunuka.
Waɗanda suka shirya shirin kai kayan agajin sun yi zargin cewa akwai aƙalla mutum 15 da aka cin zarafinsu" yayin da sauran mutanen da aka tsare sun ce an yi musu duka da kuma musguna musu. BBC ba ta iya tantance zargin ba.
Hukumar kula da gidajen yari ta Isra'ila ta yi watsi da zargin a matsayin ƙarya, tana mai cewa ''duk waɗanda ake tsare da su an tsare su ne bisa ga tanadin doka''.
An kuma tuntuɓi sojojin Isra'ila don jin ta bakinsu.
Jiragen ruwa fiye da 50 suka tashi daga Turkiyya a makon da ya gabata domin zuwa zirin Gaza da Israila ta toshe domin kai abinci da magunguna.
Gwamnatin Isra'ila ta yi watsi da matakin a matsayin wani shiri na tallata ƙungiya mai ɗauke da makamai ta Falasɗinawa, Hamas, sannan ta umarci kwamandojinta da su shiga jiragen ruwa daga yammacin Cyprus a ranakun Litinin da Talata.
An kwashe masu fafutuka da aka kama zuwa jiragen ruwa na Isra'ila kuma an wuce da su gidan yarin Isra'ila bayan sun isa tashar jiragen ruwa ta Ashdod.
A ranar alhamis, Isra'ila ta kori mutane 422 daga ƙasashe 41. Da yawa sun iso gida.
Ministar harkokin wajen Kanada Anita Anand ta faɗa a ranar Juma'a cewa "ta samu bayanai daga jami'ai da suka yi bayani kan mumunan cin zarafin da aka yi wa ƴan ƙasar Kanada a lokacin da aka tsaresu a Isra'ila", ba tare da yin ƙarin bayani ba.
Ta ƙara da cewa: "Kanada ba tare da wata shakka ba ta yi Allah wadai da mugun zaluncin da ake yi wa ƴan ƙasar ta a Isra'ila. Dole ne a hukunta wadanda ke da alhakin wannan mummunan cin zarafi."
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya ce jami'an ofishin jakadancin sun gana da masu fafutuka na Jamus a lokacin da suka isa birnin Istanbul a ranar alhamis ɗin da ta gabata inda suka bayar da rahoton cewa wasu da dama sun jikkata.
Ministan harkokin wajen Sifaniya José Manuel Albares ya shaidawa manema labarai cewa hudu daga cikin masu fafutuka na ƙasar 44 sun samu kulawar jinya sakamakon raunukan da aka ji musu.
Waɗanda suka shirya tafiyar sun ce: "An ci zarafin mutum aƙalla 15, ciki har da fyade da harbi da harsashi na roba a kusa. An karya kasusuwan mutane goma''.
Wasu masu fafutuka kuma sun yi bayani game da zarge-zargen lokacin da suka zanta da manema labarai bayan an kore su.
Bayan da ta koma Paris a ranar Juma'a, ƴar fafutukar Faransa Meriem Hadjal ta shaida wa ƴan jarida cewa "ta fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata ".
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar gidan yarin ta Isra'ila ta ce zarge-zargen "ƙarya ne kuma gaba ɗaya babu gaskiya a cikinta ".
A filin jirgin sama na Istanbul, ɗan gwagwarmayar Birtaniya Richard Johan Anderson ya shaida wa manema labarai cewa: "An yi mana duka, an azabtar da mu, da wulakanta mu ... mun ɗan danɗana irin ukkuba da Falasɗinawan ke ciki kowace rana."
A farkon makon nan ne Isra'ila ta fuskanci tofin Allah tsine daga ƙasashe sama da 20 ciki har da Birtaniya, a matsayin martani ga wani faifan bidiyo da Ministan Tsaron ƙasar Isra'ila mai tsatsauran ra'ayi, Itamar Ben Gvir, wanda ke sa ido kan ayyukan gidan yari da ƴan sandan Isra'ila ya wallafa a shafin intanet.
Bidiyon ya nuna shi yana ba'a ga masu fafutuka da dama yayin da aka nuna an tilasta musu durƙusawa a ɗaure da goshinsu na taɓa ƙasa.
Hakan ya haifar da suka daga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda ya ce abin da Ben Gvir ya yi , "bai dace da al'adun Isra'ila ba".