An saki magoya bayan tawagar Senegal da aka ɗaure a Maroko
Sarkin Maroko Mohammed na shida ya yi afuwa ga magoya bayan ƙungiyar kwallon kafa ta Senegal da aka ɗaure, bisa samun su da hannu a tayar da hatsaniya a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi a Rabat a watan Janairun 2026.
An saki magoya bayan ne domin nuna jin ƙai, da kuma alaƙar da ke tsakanin ƙasashen bisa la'akari da zuwan babbar Sallah.
Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya wallafa a shafinsa na X cewa nan ba da jimawa ba za a haɗa su da iyalansu.
"Ina miƙa godiya ta ga mai martaba bisa matakin da ya yanke na nuna tausayi da mutuntaka," in ji shugaba Faye.
A watan da ya gabata ne aka saki wasu magoya bayan Senegal uku daga gidan yari bayan sun kammala zaman watanni 3 da aka yanke musu.
An daure magoya bayan Senegal 18 a gidan yari saboda kutsawa cikin filin wasa lokacin da aka baiwa Maroko fenariti a lokacin wasan.