Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jiragen yaƙin da Amurka ta yi asara a rikicinta da Iran
Wani sabon rahoton majalisar dokokin Amurka ya bayyana yawan asarar kayan yaƙi da Amurka ta tafka a yaƙinta da Iran, inda rahoton ya ce an illata ko kuma lalata jimillar jiragen yaƙin Amurka 42 a yaƙin.
Sashen ayyukan bincike na majalisar dokokin Amurka ne ya haɗa rahoton ta hanyar amfani da bayanan da ya tattara daga ma'aikatar tsaro ta Amurka (Pentagon), da cibiyar harkokin tsaro ta ƙasar CENTCOM da kuma rahotannin kafafen yada labarai.
An wallafa rahoton a shafin intanet majalisar dokokin Amurka.
Sashen binciken ya samar da bayani kan matsalolin da aka fuskanta ta ɓangaren tsare-tsare ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ba.
Rahoton ya ce kayan yaƙin da aka yi asara sun hada da jiragen saman yaƙi, da jirage marasa matuƙa, da jiragen yaƙi masu saukar ungulu da kuma jiragen ayyukan soji na musamman.
Haka nan rahoton ya ambato wani jami'in hukumar tsaro ta Amurka, Jules W. Hurst na faɗi wa majalisar dokokin cewa kuɗaɗen da Amurka ta kashe kan yaƙin ya zarce dala biliyan 29, wanda ya hada har da kudin da aka kashe wajen kula da kuma gyaran jiragen da aka lalata.
Jirgin yaƙi na F-15E Strike Eagle
Daga cikin jiragen soji da rahoton ya ambato akwai jirgin yaki na F-15E Strike Eagle guda huɗu.
Cibiyar tafiyar da lamurran tsaro ta Amurka CENTCOM ta ce wasu daga cikin jiragen sun rikito ne a ƙasar Kuwait sanadiyyar abin da ta bayyana "harin kuskure na abokan ƙawance".
A wannan lamari, shida daga cikin matuƙa jiragen sun samu tsira lami lafiya.
A ranar 5 ga watan Afrilun 2026, Cibiyar ayyukan sojin Amurka ta Centcom ta ruwaito cewa jirgin yaƙin Amurka na F-15E ya rikito sa'ilin wani hari da ya kai a Iran, kuma an samu nasarar ceto dukkanin matuƙa jirgin biyu a wani gagarumin aikin ceto da aka gudanar.
Rahoton ya kuma ambato wani bayani na ranar 19 ga watan Mayu inda a ciki aka ce an samu asarar jirgin yaƙin Amurka samfurin F 350A wanda garkuwar kariya daga hare-hare ta Iran ta kakkaɓo.
A lokacin, Cibiyar ayyukan sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ta tabbatar cewa wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya yi saukar gaggawa bayan kai hari a cikin ƙasar Iran.
Bayanin ya ce jirgin ya sauka lafiya kuma shi ma matukin jirgin na cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai Cibiyar ayyukan sojin ba ta yi ƙarin haske kan lamarin ba, duk dai dai kafar yaɗa labarai ta CNN da ke Amurka ta ruwaito cewa sojojin Iran ne suka kai wa jirgin hari.
Haka nan rahoton majalisar dokokin Amurkar ya bayyana cewa a wani taron manema labarai na ranar 6 ga watan Afrilun 2026, shugaban manyan hafsan hafsoshin sojin Amurka, Janar Dan Kane ya ce a ranar 3 ga watan Afrilu maƙiya sun harbi jirgin Amurka samfurin A-10 wanda ya rikito daga baya, amma matukin jirgin ya tsira.
Jirgin kara wa jiragen yaki mai samfurin KC-135 tanker
Bugu da kari, jirgin tankar kara wa jiragen yaki mai samfurin KC-134 ya yi karo a sararin samaniyar kasar Iraqi, lamarin da ya kai ga asarar matuka shidda.
Haka nan an lalata wasu irin samfurin jirgin guda biyar a wani harin makami mai linzami da aka kai a kan sansanin soji na Yarima Sultan da ke kasar Saudiyya.
Haka nan rahoton ya tabbatar da lalata jirgin tattara bayanai na sojin Amurka samfurin E 3 Sentry a wani harin da aka kai a kasar Saudiyya.
Wasu hotunan da suka fito daga baya sun nuna yadda aka yi kaca-kaca da jirgin wanda ya rabe gida biyu.
Jirgin tsinkayo hadari na E 3 Sentry
Rahoton ya bayyana cewa a ranar 28 ga watan Maris an bayar da rahoton cewa wani harin makami mai linzami da kuma jirgi maras matuki na Iran a kan sansanin sojin Yarima Sultan a Saudiyya ya lalata jirgin E-3.
A ranar 7 ga watan Mayu an ruwaito cewa an ajiye jiragen ne a wuri maras cikakken tsaro.
A wannan lokaci wasu hotuna da suka fito daga filin jirgin sun numa yadda aka lalata jirgin na sojin saman na Amurka.
Sashen tabbatar da gaskiyar labarai na BBC ya tabbatar cewa an dauki hotunan ne a sansanin Yarima Sultan da ke da nisan kilomita 100 daga Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.
Gine-ginen da aka gani a hotunan kamar sorayen tattara bayanai da rumbunan ajiye kaya sun yi daidai da hotunan tauraron dan’adam.
Jirgin MC 130J Commando
A ranar 5 ga watan Afrilu rahotanni sun ce an kashe wasu jiragen Amurka biyu samfurin MC 130J wadanda ke taimakawa wajen ayyukan ceto bayan rikitowar jirgin yakin Amurka samfurin F 15E.
Rahoton ya ce jirgin ya gaza tashi a lokacin da yake kasa amma an ceto matukansa.
An gano cewa Iran ta kakkabo wani jirgin Amurka samfurin F-15E kuma ba a san inda matuki daya na jirgin yake ba, lamarin da ya sanya ala tilas aka fara aikin ceto shi.
Rahotannin wasu kafafen yada labarai na Iran sun ce an samu arangama tsakanin dakarun Amurka da na Iran a lokacin aikin ceto matukin jirgin a cikin Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana lamarin a matsayin wani gagarumin aikin ceto wanda aka yi amfani da jirage da dama a cikin Iran.
Jirgi mai saukar ungulu na aikin ceto
Rahoton ya ce a ranar 16 ga watan Afrilu Janar Dan Kane ya tabbatar a wata ganawa da manema labarai cewa an lalata wani jirgi mai saukar ungulu samfurin HH 60W a lokacin wani aikin ceto a ranar 5 ga watan Afrilu.
Yana nuni da aikin ceton wani matukin jirgin yakin Amurka da ke cikin jirgin F-15E, wanda ake da yakinin cewa wani hari na Iran ne ya kakkabo shi.
Jirgi maras matuki
Rahoton ya ambato wani labari da aka fitar a ranar 9 ga watan Afrilu da ya ce an lalata jirage marasa matuka 24 na Amurka a lokacin kai hare-hare a Iran.
Rahoton ya ce jiragen marasa matuka sun hada da samfurin MQ 9, wadanda ake amfani da su wajen tattara bayanai da kai hare-hare.
Haka nan an ruwaito cewa an lalata wani jirgin sama maras matuki mai tashi koli-koli da ke tattara bayanai samfurin MQ 4C.
Bayanai na cewa jami’an gwamnatin Amurka na ikirarin cewa sun cimma akasarin manufofinsu na shiga yakin na Iran.
Haka nan shugaban Amurka Donald Trump ya sha nanata cewa an durkusar da sojojin kasa da na sama da kuma na ruwan Iran.
A nata bangaren, har yanzu Iran ba ta fitar da cikakkun bayanai kan asarar da ta tafka a lokacin yakin ba, sai dai tana ci gaba da ikirarin cewa har yanzu tana da karfin ci gaba da yakar Amurka.