Yajin aiki kan tashin farashin mai ya durƙusar da sufuri a Kenya

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Dubban ƴan Kenya da harkokin kasuwanci a ƙasar sun shiga wani hali bayan da masu ababen hawa na haya suka tsunduma yajin aikin gama gari domin nuna fushi kan ƙarin farashin man fetur da hukumomi suka yi.
Muhimman tituna sun zama kufai a Nairbo, babban birnin Kenya lamarin da ya sa jama'a suka zaɓi daɓa sayyadarsu zuwa wajen aiki yayin da wasu yankunan ƙasar suka shiga irin wannan yanayi na matsalar sufuri.
Harkokin kasuwanci a wasu yankunan Nairobi sun tsaya cak sannan makarantu sun buƙaci ɗalibai su zauna a gidajensu.
Masu zanga-zanga dai suna toshe tituna. Yajin aikin na zuwa ne kwana biyu bayan da hukumomi suka ƙara farashin mai zuwa matakin da bai taɓa kai wa ba inda aka ƙara farashinsa da kusan kashi 20 cikin 100.
Kenya, kamar sauran ƙasashen Afirka, ta dogara sosai kan man da ake shigowa da shi daga yankin Gulf, da a yanzu yaƙin Iran ya shafa.














