KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na 22/05/2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • wata mata
  • Ungozoma
  • BBC reporter
  • Wakilai
  • Nafiu Gombe
  • Fati Halidou
  • xxx
  • Zanga-zanga
  • Atiku Abubakar

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Ƙasashen Yamma bakwai sun yi Allah wadai da ƙaruwar gine-ginen Yahudawa a Gaɓar Yamma

    Ƙasashen Yammacin duniya bakwai sun yi Allah wadai da gine-ginen da Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna ke yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    Ƙasashen sun kuma buƙaci Isra'ila ta binciki rahoton cin zarafi da ƴan kama-wuri zaunan da sojojin Isra'ila ke yi.

    Sun ce tsare-tsaren na Isra'ila na janyo koma-baya kan batun samar da ƙasashe biyu masu ƴanci a yankin.

    Ana yawan samun ƙaruwar gine-ginen Yahudawa a yankin. A baya irin wannan kira ya taimaka wajen sauya matsayin Isra'ila.

  2. Iraƙi da Uzbekistan da Kazakhstan sun aika wa Iran kayan agaji

    Mataimakin shugaban ƙungiyar agaji ta Red Crescent a Iran ya ce ƙasashen Iraƙi da Uzbekistan da Kazakhstan sun aike wa Iran kayan agaji kuma tuni jiragen da ke ɗauke da kayan suka isa ƙasar.

    Razia Alishundi ya ce kayan agajin - waɗanda suka haɗa da kayan abinci da magunguna da kayan aikin asibiti - an miƙa su ga ƙungiyar Red Crescent domin taimaka wa marasa ƙarfi a ƙasar.

    A cewar ƙungiyar agajin Iraƙi ta aike da kayan agajin da nauyinsu ya kai tan 180, yayin da Uzbekistan ta aika da tan 300 sai kuma Kazakhstan mai tan 1,700.

    Mista Alishindi ya ce mafi yawan kayan da Kazakhstan ta aika da su fulawa ce da sukari.

  3. APC za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa a gobe Asabar

    Tinubu

    Asalin hoton, Multiple

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa a gobe Asabar ta hanyar ƴartinƙe.

    Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce za a gudanar da zaɓukan a faɗin mazaɓun ƙasar 8,809.

    Shugaba Tinubu da Stanley Osifo ne ke neman tikitin tsayawa jam'iyyar takara a zaɓen 2027.

    Jam'iyyar ta ce duk wanda ke da katin rajistar jam'iyyar na da damar zaɓar wanda zai yi wa jam'iyyar takara.

    Sanarwar ta ce za a tattara sakamakon zaɓukan kowace mazaɓa a ƙaramar hukuma, kafin akai shi babban cibiyar tattara sakamakon ta ƙasa da ke Abuja.

    Jam'iyyar ta kuma naɗa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Pius Anyim Pius a matsayin shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasar.

    Yayin da ta naɗa Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban kwamitin ƙarɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen.

  4. Babban hafsan sojin Pakistan ya sake komawa Iran

    Babban hafsan sojin Pakistan

    Asalin hoton, Iranian Parliament Communication Office/Handout via Getty Images

    Kafofin yaɗa labaran Pakistan sun ce babban hafsan sojin ƙasar, Field Marshal Asim Munir ya tafi Iran.

    Kamfanin dillancin labarai na AP a Pakistan ya ambato wasu majiyoyin tsaro na cewa Field Marshal Asim Munir zai tattauna batun ''yarjejeniyar Iran da Amurka da zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya da sauran batutuwan alaƙar ƙasashen biyu'' da jami'an Iran a lokacin ziyarar tasa.

    Kwana 40 da suka gabata ne babban hafsan sojin ya tattauna da Mohammed Baqer Qalibaf da mambobin tawagogin Amurka da Iran a tattaunawar da ƙasashen biyu ke yi.

    Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ministan cikin gida na Pakistan ya ziyarci Tehran karo na biyu cikin mako guda, kuma yake tattaunawa da jami'an Iran.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya faɗa yau cewa Washington na jiran bahasin Iran daga tattaunawar.

  5. Yadda ake noman zamani a cikin ɗaki

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Wani matashi mai noman zamani wanda ake kira ʼGreen houseʼ, da ba ya jiran zuwan damina ya bayyana mana yadda ake yin sa da kuma yadda tsarin ke ƙara samun karɓuwa a Najeriya.

    Shazali Na'ibi Muhammad ya ce wannan hanya ta noma na da alfanu mai yawa, saboda tarin dabarun da ke tattare da hanyar.

  6. Iraq da Uzbekistan da Kazakhstan sun aike da kayan jinƙai ga Iran

    Mataimakin ƙungiyar jinƙai ta Red Crescent Society ta ce ƙasashen Iraq da Uzbekistan da Kazakhstan sun aike da kayan jinƙai kuma tuni kayan suka shiga Iran.

    Ƙungiyar ta ce ƙasar Iraq ta aike da manyan motoci guda 9 ɗauke da tan 180 na abinci da magani.

    Ita kuma Uzbekistan ta aike da manyan motoci sai kuma Khazakstan da ta aike da tan 1,700.

  7. Amurka ta dakatar da sayar da makamai ga Taiwan kan yaƙi da Iran

    ..

    Asalin hoton, CQ-Roll Call, Inc. via Getty Image

    Ƙasar Amurka ta sanar da dakatar da sayar da makamai na kimanin kuɗi dala biliyan 14 ga Taiwan domin tabbatar da tana da isassun makamai a rumbunta ko da faɗa ya sake ɓarkewa tsakaninta da Iran.

    Muƙaddashin sakataren sojojin ruwa na Amurka, Hong Kao ya tabbatar da hakan ga ƴan majalisar dattawa a ranar Laraba.

    Wannan dai na zuwa ne duk da cewa shugaba Trump har yanzu bai fitar da matsaya ba dangane da sayar da makaman, inda ya ce zai tattauna batun da shugaban Taiwan tukunna.

  8. Sojojinmu a shirye suke a Gabas ta Tsakiya - Amurka

    CENTCOM

    Asalin hoton, CENTCOM

    Cibiyar ayyukan sojin Amurka da ke kula da yaƙi a kan Iran, CENTCOM ta sanar da cewa jirgin yaƙin Amurka, Abraham Linciln na cikin halin "jiran ko-ta-kwana".

    A wani saƙo a kafar sada zumunta , Centcom ta wallafa hotunan jiragen yaƙin Amurka da suka haɗa da F-35 da ke tashi daga wasu manyan jiragen yaƙi sannan ta ce dakarunta suna cikin shirin ko-ta-kwana "a daidai lokacin da suke ci gaba da toshe tashoshin ruwan Iran".

  9. Muna sauraron sakamakon tattaunawa a Iran - Marco Rubio

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce ƙsarsa na dakon sakamakon tattaunawar da ake yi a Iran.

    Mista Rubio wanda ya je ƙasar Sweden domin halartar taron ministocin ƙasashe ƙungiyar tsaro ta Nato domin tattaunawa kan Iran da hanyoyin da ya kamata a bi wajen tursasa mata buɗe mashigar ruwa ta Hormuz.

    Ministan cikin gidan Pakistan, Mohsen Naqvi ya je gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aragchi kan yadda za a warware rikicin tsakanin Amurka da Iran.

    Iran dai ta sha faɗin cewa ba za ta tattauna ba kan nukiliya a wannan lokaci inda ta ce sai bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

  10. Ministan Pakistan ya gana da Aragchi kan rikicin Iran da Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Pakistan a Tehran ya rawaito cewa ministan cikin gida na Pakistan ɗin, Mohsen Naqvi ya sake gana wa da ministan ƙasashen waje na Iran, Abbas Aragchi a karo na biyu a kwanaki biyu da suka gabata.

    Kamfan dillancin labarai na Fars News ya ce ganawar an yi ta ne da manufar "tattaunawa kan sabbin tsare-tsare na ganin an warware rikicin" da ke tsakanin Iran ɗin da Amurka.

    Mista Naqvi dai ya sauka a birnin Tehran ranar Laraba kuma tuni ya gana manyan jami'ai na jamhuriyar ta Musulunci ta Iran.

    Akwai yiwuwar cewa Filed Marshall Asim Munir babban hafsan hafsoshin sojin Pakistan shi ma ya garzaya zuwa Tehran domin taimakawa a warware taƙaddamar da ke tsakanin Iran da Amurka.

  11. Ƴansanda a Equador sun kama mutum fiye 20 kan safarar makamai a Columbia

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a Ecuador sun tsare mutum sama da 20, tare da tarwatsa wani gungun masu safarar makamai zuwa ƙungiyoyin ƴan daba a Colombia.

    Matakin wanda na hadin gwiwa ne tsakanin hukumomin Colombia da na Peru, ya kunshi sama da jami'an 'yan sandan Ecuador dari hudu wadanda suka kai samame a larduna da dama.

    Kungiyar masu aikata laifukan ta kasance tana safarar makamai da alburusai, da nakiyoyi daga Peru zuwa kungiyoyin 'yan tawayen Colombia da suka ɓalle daga kungiyar FARC da ta tarwatse.

    Wannan samamen dai ya zo ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke kara kamari a fadin Ecuador, inda aka kashe sama da mutum dubu tara a shekrar da ta gabata.

  12. Hare-haren bindiga sun kashe mutum fiye da 10 a Honduras

    Masu gabatar da kara a arewacin Honduras sun ce akalla mutum goma sha tara ne aka tabbatar da mutuwarsu a wasu jerin hare-hare bindiga.

    Mutum 13 ne suka mutu bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a wani Coci da ke cikin wata gona, inda suka bude musu wuta.

    Ministan tsaron Honduras Gerzon Velásquez, ya lashi takobin yin duk abin da ya kamata domin zakulo wadanda ke da hannu a harin.

    An tura wata runduna ta musamman zuwa yankin Bajo Aguán, inda kungiyoyin masu aikata laifuka suka saba zuwa su kwace gonakin jama'a ba bisa ka'ida ba.

    A jiya Alhamis, an kashe akalla jami’an ‘yan sanda shida da fararen hula a wani artabu da aka yi da wasu masu aikata laifuka a kan iyakar kasar da Guatemala.

  13. PDP tana zaɓen fidda gwani na majalisar dokokin jihohi

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Nan gaba a ranar Juma'ar nan ne babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, PDP za ta gudanar da aikin tantance ƴan takarar kujerun majalisun jihohi a faɗin ƙasar.

    A baya-bayan nan ne jam’iyyar ta tantance waɗanda za su yi mata takarar kujerun majalisar wakilai da na majalisar dattawa a babban zaɓen 2027.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida ke ci gaba da ƙamari, inda tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, shi ma ke gudanar da nasa aikin tantance ƴan takarar.

    A yanzu dai jam'iyyar ta PDP ta dare gida biyu tsakanin ɓangaren Tanimu Turaki da kuma ɓangaren da Nyesom Wike ko goya wa baya.

  14. Al-Nassr ta lashe Saudi Pro League

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta lashe babban gasar kwallon kafa ta Saudiyya (Saudi Pro League) ta farko tun shekarar dubu biyu da sha tara, inda fitaccen dan wasanta Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu don taimaka mata wajen lashe wasan karshe na kakar wasan bana.

    Sadio Mane da Kingsley Coman suma sun zura kwallaye daya-daya a cikin hudun da Al-Nassr ta jefa a ragar Damac.

    Nasarar ta sa kungiyar ta kammala gasar bana da maki biyu tsakaninta da Al Hilal a saman teburi.

    Wannan dai shi ne babban kofi na farko da Ronaldo ya lashe tun bayan da ya koma Al-Nassr a shekarar dubu biyu da ashirin da biyu.

  15. Wasu fusatattu mutane sun ƙona asibitin Ebola a DR Congo

    Wasu fusatattun mutane sun kona wani bangare na wani asibiti a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango bayan mutuwar wani mara lafiya da ake zargin yana dauke da cutar Ebola.

    A Lardin Ituri wani matashi ya mutu bayan ya kamu da Ebola sai yan uwansa suka nemi a basu gawar amma ma'aikatan asibiti suka hana su, sakamakon haka suka tayar da tarzoma.

    Ma’aikatan lafiya a asibitin Rwampara na karkashin kariyar sojoji yayin da ƴan sanda ke kokarin dawo da zaman lafiya.

    Jami’ai sun ce cutar ta kashe mutane sama da dari da hamsin (150), inda ake zargin sama da wasu mutum dari shida (600) sun kamu da cutar.

  16. Ministocin ƙungiyar tsaro ta NATO na taro kan yaƙin Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Juma'ar nan ne ministocin harkokin wajen ƙungiyar tsaro ta NATO ke taro a ƙasar Sweden a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar takun saƙa a cikin ƙawancen sakamakon da yaƙin Amurka da Iran da kuma tasirinsa a duniya.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya shaida wa BBC cewa za a tattauna batun rage yawan sojojin Amurka a Turai.

    Ya ƙara da cewa shugaba Trump ya ji taƙaicin ƙasashen NATO saboda rashin goyon bayansu.

    Tun da farko, Mista Trump ya sanar da cewa zai tura dakaru dubu biyar zuwa Poland, makonni kadan bayan da Washington ta ce ta janye dubban sojoji daga Jamus.

    Ana kuma sa ran ministocin za su tattauna kan ci gaba da goyon bayan Ukraine a yakin da take yi da Rasha

  17. Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar gwamna ya koma wurin Kwankwaso

    Rabi'u Musa Kwankwaso

    Asalin hoton, Kwankwaso/X

    Ɗan majalisar dokokin jihar Kano da ke wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, wadda ita ce ƙaramar hukumar gwamnan Kano, Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata ya fice daga jam'iyyar APC zuwa ta NDC.

    A ranar Alhamis ne dai tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran jam'iyyar NDC ya karɓi ɗan majalisar.

    Mai Riga ya sanar da sauya sheƙara tasa ne bayan gaza samun takarar yin tazarce a kujerar tasa a lokacin zaɓen fidda gwani da jam'iyyar APC ta gudanar, bisa zargin "rashin gaskiya da adalci".

    Ana dai ganin nan ba da jimawa ba za a yi ta samun masu sauya sheƙa sakamakon abubuwan da suka faru a jam'iyyu na zaɓen cikin gida.

    Da ma dai wata kotu a Abuja ta dakatar da wa'adin da hukumar zaɓe ta saka wa jam'iyyu dangane da ranakun rufe rijistar ƴaƴan jam'iyyu, wanda ake yi wa kallon shi ma zai ƙara bai wa ƴan siyasa damar ci gaba da sauya sheƙa.

  18. Da gaske Tinubu ya ce zai dakatar da shari'ar Musulunci a Najeriya?

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Fadar shugaban Nijeriya ta musanta wani labari da ta ce na jabu ne, da ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na yunƙurin yi wa tsarin mulkin Nijeriya gyaran fuska domin sauya sunan ƙasar da kuma rusa dokar shari'ar Musulunci.

    Ta ce labarin wanda aka wallafa ba tare da ambatar majiyarsa ba, wani ɓangare ne na "maƙarƙashiyar wasu ƴan siyasa da idonsu ya rufe a ƙoƙarinsu na haddasa ƙiyayya da janyo rikicin siyasa da tunzuri" gabanin babban zaɓen 2027.

    Labarin dai ya bayyana ne a shafukan sada zumunta a makonnin da suka gabata kuma ya sake bayyana a baya-baya nan.

  19. Cuba barazana ce ga tsaron Amurka - Marco Rubio

    Marco Rubio

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa, Cuba barazana ce ga tsaron ƙasar Amurka, kuma ya yi gargaɗin cewa abu ne mai wuya a iya warware rikicin da ke tsakanin ƙasasehn biyu cikin lumana.

    Jami'an Cuba dai sun sha zargin Washington da ƙoƙarin nemo hujjar ɗaukar matakin soji a kan tsibirin.

    A ranar Laraba, Washington ta tuhumi tsohon shugaban Cuba Raul Castro da kisan kai sakamakon wani hari da aka kai shekara talatin da suka wuce.

    Amurka ta girke jiragen ruwan yaki a yankin Caribbean, kuma ta kwashe watanni da dama ta na killace tsibirin.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da safiyar ranar Juma'a da fatan kun wayi gari lafiya. Kamar kowace rana mun dawo domin ci gaba a inda muka tsaya a shafinmu na kai tsaye da ke kawo muku wainar da ake toyawa dangane da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran.

    Har wayau, shafin yana kuma kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.