Da gaske ne Tinubu ya ce zai rusa shari'ar Musulunci a Najeriya?

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/Tinubu

Bayanan hoto, Shugaba Bola Ahmed Tinubu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Fadar shugaban Nijeriya ta musanta wani labari da ta ce na jabu ne, da ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na yunƙurin yi wa tsarin mulkin Nijeriya gyaran fuska domin sauya sunan ƙasar da kuma rusa dokar shari'ar Musulunci.

Ta ce labarin wanda aka wallafa ba tare da ambatar majiyarsa ba, wani ɓangare ne na "maƙarƙashiyar wasu ƴan siyasa da idonsu ya rufe a ƙoƙarinsu na haddasa ƙiyayya da janyo rikicin siyasa da tunzuri" gabanin babban zaɓen 2027.

Labarin dai ya bayyana ne a shafukan sada zumunta a makonnin da suka gabata kuma ya sake bayyana a baya-baya nan.

Abdul'aziz Abdul'ziz, mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya ya shaida wa BBC cewa an shirya labarin ƙarya ne domin shafawa shugaba Bola Ahmed Tinubu kashin kaji

''Mun ga labarin ƙarya yana yawo, kuma wani labari ne mara tushe akan cewa shugaban ƙasa zai kawo wasu sauye-sauye waɗanda su ka haɗa da hana shariar musulunci a wasu jihohi na arewacin ƙasar, da kuma canza wa ƙasar suna''

''Wannan magana ba haka take ba, kuma shi yasa mu ka fitar da wannan sanarwa domin ƙaryata wannan labari mara hujja, wanda dama an shirya shi ne domin kawo ce-ce ku -ce mara kyau tare da gogawa shi shugaban kasa kashin kaji'', in ji shi

Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga ƴan ƙasar da su yi watsi da labarin gaba ɗayansa saboda a cewarta masu yaɗa labarin bogin dillalai ne na kawo hargitsi da tashin-tashina.

Abdulaziz Abdulaziz ya kuma ce labarin na da alaƙa da siyasa

''Yanzu lokacin siyasa ne, ƴan adawa ba bu abin da ba za su iya ba , ba za mu iya cewa su waye suka haɗa wannan manaƙisa ba, domin sun yi ne a ɓoye''

''Amma dai aiki ne na waɗanda za a iya cewa maƙiya ko ƴan adawa ne waɗanda suna ƙoƙarin su ɓata sunan gwamnati da shugaban ƙasa'' in ji shi

Ko za a iya cire Shari'a daga tsarin mulkin Najeriya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A shekarar 20205 ma an taɓa irin wannan tattaunawa biyo bayan buƙatar da ɗan majalisar ƙasar Amurka, Riley Moore ya yi ga majalisar ƙasar na zargin "muzgunawa Kiristoci" a Najeriya.

Sai dai babban abin da ya fi jan hankali shi ne batun soke shari'ar Musulunci da dokar kisa kan ɓatanci, daga cikin matakai aƙalla shida da majalisar ta buƙaci Trump ya ɗauka.

Kuma a lokacin ne BBC ta tuntuɓi Barista Bulama Bukarti wanda lauya ne mai zaman kansa a Burtaniya dangane da cire Shari'ar Musulunci daga tsari mulkin Najeriya inda ya ce ba abu ne mai sauƙi ba.

"Maganar Shari'a da kuma ƙarfin da aka bai wa majalisun dokokin jihohi na cikin kundin tsarin mulki, wanda sauya shi na da wuya domin shugaban ƙasa shi kaɗai ba zai iya yi ba."

"Haka ma ƴan majalisar tarayya su kaɗai ba za su iya yi ba. Dole ne sai an haɗa da ƴan majalisar jihohi. Kuma ka ga majalisun jihohin da ke ɗabbaƙa shari'ar Musulunci da al'ummominsu ba za su yarda a cire shari'a da Hizba ba daga tsarin mulki ba," in Bukarti.

"Barista Bukarti ya ƙara da cewa hanyar cire shari'ar Musulunci da Hizba daga tsarin mulki guda ɗaya ce kawai, wato yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima wanda kuma zai yi matuƙar wuyar gaske."

"Sashe na 9 na kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi yadda za a yi wa tsarin mulki gyaran fuska kuma ya ce dole ne sai an samu kashi biyu bisa uku na dukkannin ƴan majalisar dattawa da wakilai sun goyi bayan ƙudirin yin kwaskwarimar. Sannan kuma daga nan za a tafi majalisun jihohi inda sai an samu kaso biyu bisa uku, wato jihohi 24 na jihohi 36 na ƙasar."

Yaushe Shari'ar Musulunci ta fara aiki a Najeriya?

Bukarti ya ce shari'ar Muslunci ta samu shiga kundin tsarin mulkin Najeriya tun 1979 duk da cewa ambatonta ya fi shahara a 1999 bayan gyaran fuska da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ya ce bayan yi wa tsarin mulin Najeriya a 1999 wanda ya bai wa jihohi damar yin dokoki kan laifi, sai aka samu raji daga wurin al'ummu na neman a yi hukunce-hukunce kan laifuka.

"Abin da ya faru har aka yi rajin dawo da shari'ar Musulunci a 1979 shi ne kundin tsarin shekarar ya tanadi shari'ar Musulunci ne a kan mu'amala kamar aure, gado da iyali da dai sauran su wanda ya janyo aka kafa kotunan shari'ar Musulunci.

To amma a 1999 sai aka samu masu rajin da ke son a samu shari'o'in kan laifuka. Kuma wannan ne ya sa ƴan majalisa suka yi dokokin laifuka bisa doron addinin Musulunci kuma har aka kakkafa kotunan addinin Musulunci. Ke nan da ma akwai shari'ar amma yanzu faɗaɗa ta kawai aka yi," in ji Bukarti.

Jihohin Arewa 12 da ke yin tsarin Shari'a

Aƙalla jihohin Najeriya 12 ne daga cikin 36 ke dabbaƙa dokokin Shari'ar Musulunci.

Ga jerin jihohin 12:

  • Zamfara State
  • Kano State
  • Sokoto State
  • Katsina State
  • Bauchi State
  • Borno State
  • Jigawa State
  • Kebbi State
  • Yobe State
  • Kaduna State
  • Niger State
  • Gombe State