Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kebbi sun cafke wani mutum da ya ɓuya cikin jakar Ghana Must Go a gidan wata matar aure a yankin Badariya a Birnin Kebbi.
Daraktan shari'a a hukumar, Sirajo Kamba ne ya tabbatar da kame mutumin a wata sanarwa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Kamba, mazauna yankin sun ankarar da Hisba ne a ranar 18 ga watan Mayu bayan da suka gano wani mutum yana shiga gidan matar.
"Mazauna unguwar sun yi zargin akwai mu'amalar da ta saɓa shari'ar musulunci tsakanin mutanen biyu, abin da ya sa suka sanar da hukuma.
"Da samun rahoton ne kuma, hukumar Hisba ta jihar Kebbi ta aike da jami'anta zuwa gidan matar.
Daraktan ya ce a lokacin da jami'an suka isa gidan, sun nemi su yi bincike a gidan sai dai matar ta ƙi bayar da dama inda ta musanta cewa babu kowa a cikin gidan.
Daraktan ya kuma ce daga bisa ni ne matar ta amince a yi bincike lamarin da ya sa aka gano wanda ake zargi cikin wata jakar Ghana Must Go.
Ya ƙara da cewa binciken da aka zurfafa ya nuna cewa akwai alaƙa ta soyayya tsakanin matar mai aure da kuma mutumin.
Kamba ya ce masoyan sun tabbatar da zargin da ake musu inda ya ce za a gurfanar da su gaban kotu domin fuskantar shari'a bisa tanadin musulunci.