Jami'an Najeriya sun kashe 'yan bindiga sama da 30

Asalin hoton, Getty Images
An gano gawarwaki sama da 30 da ake zargin na ’yan bindiga ne a gonaki da ke kewaye da garin Bukuyum a Jihar Zamfara bayan wata arangama tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga, kamar yadda ’yan sanda suka bayyana.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce jami’anta, tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin tsaron sa-kai na cikin gida, sun daƙile wani yunƙurin hari da ’yan bindiga suka kai wa garin Bukuyum yayin da ake ci gaba da gudanar da samame domin kawar da ’yan bindiga a yankin.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta ce aikin ya fara ne a ranar 28 ga Disamba, 2026, bayan da ’yan bindiga suka yi yunƙurin kutsawa cikin garin.
A cewar ’yan sanda, jami’an tsaro sun fafata da maharan a wani mummunan musayar wuta, lamarin da ya hana su shiga cikin al’umma.
Rundunar ta ce daga baya an gano gawarwaki sama da 30 da ake kyautata zaton na ’yan bindigar da aka kashe ne a gonakin da ke kewaye da yankin, wanda ke nuna cewa maharan sun yi asara mai yawa.
Sai dai ta bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, tana mai cewa ’yan bindiga kan saba kwashe matattunsu da waɗanda suka jikkata daga wuraren da aka gwabza faɗa.
’Yan sandan sun ce nasarar kare garin ta hana yiwuwar asarar rayuka, lalata dukiyoyi da kuma ƙara yawan mutanen da za su bar gidajensu.
Sun kuma ƙara da cewa binciken farko na tsaro ya nuna cewa matsin lambar da sojoji da sauran jami’an tsaro ke ci gaba da yi ya tilasta wa wasu daga cikin ragowar ’yan bindigar barin jihar.
Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da ayyukan kawar da ’yan bindiga tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tsarkake yankin daga miyagun laifuka.
Haka kuma ta ce waɗannan ayyukan na da nufin dawo da amincewar jama’a da kuma tabbatar da tsaron mazauna yankunan da lamarin ya shafa.


























