Batun addini ne ke taka rawa a shari'ar El-Rufai - NSCIA

Asalin hoton, El-Rufai/X
Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta nuna damuwa kan abin da ta kira alamun nuna wariyar addini a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
A wata sanarwa da Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce ta daɗe tana ƙoƙarin ganin ta kaurace wa yin tsokaci kan shari'ar, saboda tun farko ta ɗauke ta a matsayin shari'a ta yau da kullum, tare da tunanin cewa kotuna za su iya tabbatar da adalci.
Sai dai majalisar ta ce wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, sun sa ta fara ganin akwai alamun wariyar addini ce ke taka rawa a shari'ar.
Wannan ya biyo bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda ya zargi El-Rufai da shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.
NSCIA ta ce waɗannan kalamai sun sa ta sauya matsayinta na ƙin tsoma baki a batun, tana mai cewa akwai abubuwan da ke nuna yiwuwar wani "son zuciya na wariyar addini" a kan tsohon gwamnan.
Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ɓangaren shari'a da su tabbatar da cewa ba a yi amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari'a wajen aiwatar da wata manufa ta bangaranci a kan El-Rufai ba.
Ta kuma yi kira ga jama'a da su guji kalaman tunzura jama'a da ka iya yin tasiri kan shari'ar El-Rufai ko kuma ƙara dagula yanayin tsaro a Najeriya.
















