Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/09/2026

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Talata 08/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir

Rahoto kai-tsaye

Daga Muslim Muhammad Yusu da Abdullahi Bello Diginza

  1. Hungary ta kori jami'an diflomasiyyar Rasha 10 yayin da dangantaka ke ƙara yin tsami

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministar harkokin wajen Hungary, Anita Orbán, ta bayyana cewa an umurci jami'an diflomasiyyar Rasha guda 10 su bar Budapest saboda abin da aka bayyana a matsayin 'shiga cikin ayyukan da ba za a amince da su ba.'

    'Wannan mataki yana tabbatar da tsaro da ƴancin ƙasar Hungary," in ji ta a shafukan sada zumunta, ba tare da bayar da cikakkun bayanai ba.

    Tsawon shekaru, ana kallon Hungary a matsayin babbar ƙawar Rasha a Tarayyar Turai a lokacin mulkin Viktor Orbán, amma tun bayan da ya sha kaye a zaɓen watan Afrilu, sabuwar gwamnatin ta sauya akalarta daga goyon bayan Kremlin da ya saba yi a baya.

    Firaministan Hungary, Péter Magyar, ya yi alƙawarin ƙulla dangantaka mai amfani da kuma dacewa da yanayi (mai ma'ana ta zahiri) tare da Moscow tun lokacin da aka zaɓi jam'iyyarsa ta Tisza a watan Afrilu.

    Shi da ministan harkokin wajen ƙasar sun yi kira ga Rasha da ta kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine.

    A watan Mayu, Anita Orbán ta kira jakadan Rasha domin nuna rashin amincewa da wani babban harin jiragen sama marasa matuƙa da aka kai yankin Transcarpathia na Ukraine, yankin da ke da yawan al'ummar tsirarun ƴan asalin Hungary.

  2. Tsarin harkokin kiwon lafiya na Sudan na gab da rugujewa - MSF

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ƙungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi gargaɗin cewa, tsarin kiwon lafiyar Sudan mai rauni na gab da rugujewa sakamakon rage tallafin kuɗi daga ƙasashen duniya, lamarin da ya haifar da rufe cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.

    Ƙungiyar agajin ta bayyana cewa, ƙungiyoyi da dama sun kasa samun hanyar samun kudaɗe ta daban bayan da Amurka—wadda ita ce babbar mai bai wa Sudan tallafi—ta rufe USAID, hukumar da ke kula da bayar da tallafi ga ƙasashen waje, a shekarar da ta gabata.

    MSF ta yi kira ga shugabannin duniya da suka taru a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York da su ɗauki mataki.

    Yaƙin da ya barke a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin ƙasar da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) ya haifar da ɗaya daga cikin munanan rikice-rikicen jin ƙai a duniya, inda mutane sama da miliyan 33 ke buƙatar tallafin kiwon lafiya.

    MSF ta ce duk da cewa Amurka ce har yanzu babbar mai bai wa Sudan tallafi, tallafin da ƙungiyoyi da dama ke samu daga USAID ya ƙare a watan Yuni—a daidai lokacin da gwamnatocin ƙasashen Turai su ma ke rage tallafin da suke bayarwa a matakin ƙasa da ƙasa.

  3. Labarai da dumi-dumi, Amurka ta mayar da martani kan iƙirarin Iran na kama jirgin ruwanta

    Jirgin ruwan Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedikwatar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta mayar wa BBC martani kan ikirarin da Iran ta yi na cewa ta kama wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka a mashigin Hormuz.

    A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun CENTCOM, Laftanar Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ruwan ƙarƙashin tekun ya lalace ne fiye da kwana ɗaya da ya gabata.

    Ya ce jirgin yana sintiri ne a ruwan yankin domin tallafa wa ayyukan da sojojin Amurka ke ci gaba da gudanarwa.

    Hawkins ya ƙara da cewa, "jirgin tsohon samfuri wanda ba ya tattara muhimman bayanan sirri, kuma ba ya ɗauke da na'urorin radar ko na'urorin gano bayanai masu sirri."

    Ya kuma ce ayyukan sojojin Amurka a ruwan yankin na ci gaba kamar yadda aka saba.

    A sa'o'in da suka gabata ne kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar juyin juya halin Iran, ya ba da rahoton cewa Iran ta "kama" wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku mai fasahar zamani na Amurka.

    A cewar Fars, jirgin na daga cikin sababbin jiragen ruwa marasa matuƙi masu zamani da sojojin Amurka ke amfani da su.

    Kamfanin ya kuma ce an kama jirgin ne a bakin shiga mashigar Hormuz.

  4. Ƴan sandan Jamus sun kama wanda ake zargi da yin ɓarna a tashar wutar lantarki

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An kama wani mutum mai shekaru 48 bisa zargin aikata jerin hare-haren zagon ƙasa kan cibiyoyin samar da wutar lantarki na Jamus, bayan ya shafe kwanaki yana ɓuya.

    Ƴan sandan birnin Cologne sun bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne ɗauke da abubuwan fashewa a kusa da tashar samar da wutar lantarki ta Weisweiler da ke yammacin Jamus a ranar Talata.

    Sun ƙara da cewa, an kuma gano wata tanti a cikin dazuzzukan da ke kusa da wurin, wadda aka sanya mata ƙarin abubuwan fashewa.

    Ana kyautata zaton cewa wanda ake zargin—wanda kafofin yaɗa labaran Jamus suka bayyana sunansa a matsayin Daniel V—shi ne ya rubuta wasikun da ke ɗaukar alhakin waɗannan hare-hare, waɗanda suka faru a jihohin Brandenburg da Saxony da ke gabas, da kuma North Rhine-Westphalia da ke yamma.

    Ƴan sandan sun ce ƙwararru kan kawar da bama-bamai na ci gaba da bincikar abubuwan fashewar da aka gano yayin kama mutumin, yayin da jami'ai ke duba ko akwai wasu na'urorin fashewa da ba a gano su ba a wuraren da ke kewaye da yankin.

  5. Labarai da dumi-dumi, Iran ta ce ta "ƙwace" jirgin ruwan Amurka mai sarrafa kansa

    Jirgin ruwan Amurka mai sarrafa kansa

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC), ya ce Iran ta ƙwace wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku na Amurka mai amfani da fasahar zamani da sarrafa kansa.

    A cewar Fars, jirgin ruwan na daga cikin sabbin jiragen ruwa marasa matuƙa, masu amfani da fasahar zamani da Amurka ke da su.

    Kamfanin ya ce an kama jirgin ruwan ne a mashigar Hormuz, muhimmin mashigin ruwa da ke haɗa Tekun Fasha da Tekun Oman.

    Ya zuwa yanzu, Amurka ba ta mayar da martani kan wannan rahoto ba.

  6. Aƙalla mutum biyu sun mutu bayan hare-haren Rasha Kyiv

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'ai sun ce aƙalla mutane biyu sun mutu bayan da Rasha ta sake fara kai hare-hare ta sama a babban birnin Ukraine na Kyiv da sanyin safiyar Talata.

    An kai harin ne bayan da ƙasashen biyu suka amince su dakatar da kai hare-hare a manyan biranen juna na tsawon kwanaki uku yayin da manyan wakilan shugaba Donald Trump na Amurka suka ziyarci Moscow da Kyiv.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce a ranar Litinin yana tunanin yaƙin zai ci gaba har zuwa lokacin hunturu, bayan tattaunawa da Steve Witkoff da Jared Kushner - ziyararsu ta farko zuwa Ukraine tun bayan mamayar Rasha.

    An samu jerin fashewar abubuwa a babban birnin Ukraine cikin dare, inda mutane biyu suka mutu, wasu goma kuma suka jikkata, a cewar hukumar agajin gaggawa ta birnin.

  7. Birtaniya ta sanya ƙarin takunkumai masu tsauri kan Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Birtaniya ta wallafa wani kuduri na neman ɗora takunkumai masu tsauri kan Iran da suka haɗa da faɗaɗa takunkumin ciniki da iko ga jiragen ruwa.

    An bayyana waɗannan matakan a matsayin wani ɓangare na babban ƙoƙari na daƙile shirin nukiliyar Iran da sauran ayyukan ƙiyayya.

    Gwamnatin Burtaniya ta ce matakan za su taƙaita damar Iran ta ke da shi na shiga tsarin kuɗi na Burtaniya da kuma faɗaɗa haramcin ciniki zuwa ƙarin wasu kayayyaki da fasahohi da ayyuka.

    Matakan za su kuma hana jiragen saman Iran sauka a ƙasar Birtaniya, sai dai a cikin wasu lokutan da aka keɓe.

    Stephen Doughty, babban jami'in Ofishin Harkokin Waje na Burtaniya, ya ce a cikin wata sanarwa cewa dokar "ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarinmu na daƙile burin mallakar nukiliya na Iran" kuma za su taimaka wa London wajen tabbatar da cewa Iran ba za ta taɓa samun makaman nukiliya ba.

  8. Qatar ta ce tana 'ƙoƙarin sake dawo da tattaunawa' tsakanin Iran da Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya sanar da cewa tana aiki "tare da abokan hulɗarta a yankin da ma sauran sassan duniya, ciki har da China," domin sake fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.

    A halin yanzu, Firaminista kuma Ministan harkokin wajen Qatar ne ke jagorantar tawagar da ta tafi birnin Beijing.

    A cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Pakistan ce babbar mai shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka a halin yanzu, amma jami'an Qatar ma suna taka rawa sosai a wannan aiki na shiga tsakani.

    An samu rahoton cewa, kwanan nan wata tawagar jami'an diflomasiyyar Qatar ta ziyarci Iran.

    A jiya ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, tawagar ta gana da Ministan harkokin waje Abbas Araqchi, inda aka bayyana cewa manufar ziyarar ita ce "ci gaba da ƙoƙarin rage tashin hankali" a yankin.

  9. 'Hamas ba za ta shiga cikin sabuwar gwamnatin Gaza ba'

    Hamas

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya yi kira ga Hamas da ta mika makamanta tare da rusa abin da ya kira “ginshikan ayyukan ta’addanci” na ƙungiyar.

    Miliband ya ce, a karkashin shirin zaman lafiya mai kunshe da yarjeniyoyi 20, “Hamas ba za ta taka wata rawa a shugabancin Gaza nan gaba ba.”

    Ya ce Isra’ila na da haƙƙin rayuwa ba tare da fargaba ba, amma ya kara da cewa an kashe mutane sama da 70,000 a Gaza, ciki har da yara 20,000.

    Miliband ya kuma ce ana ci gaba da hana kai agajin jinƙai da ceton rayuka zuwa Gaza, inda ya kara da cewa sama da kashi 60 na gidajen yankin “sun koma kufai.”

  10. Kenya ta bai wa baƙin haure wa’adin kwanaki 90 su mallaki takardun zama a ƙasar

    William Ruto

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Kenya ta bai wa baƙin haure da ke gudanar da ƙananan sana’o’i a ƙasar wa’adin kwanaki 90 su mallaki takardun zama da izinin aiki da kuma lasisin kasuwanci.

    Kakakin Fadar Shugaban Ƙasar, Hussein Mohammed, ya ce za a gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ofisoshin jakadancin ƙasashen da abin ya shafa, domin ba su damar daidaita takardunsu da harkokin kasuwancinsu cikin tsari.

    Ya ce cikin kwanaki 90 masu zuwa gwamnati za ta gudanar da aikin, kuma bayan cikar wa’adin, za a fara aiwatar da dokokin shige da ficen.

    Sanarwar ta biyo bayan umarnin Shugaba William Ruto na cewa ƴan Kenya ne ya kamata su riƙa yin wasu ƙananan sana’o’i, ciki har da masu tallace-tallace a kan titi da sana’ar sayar da kaya.

    Matakin ya haifar da fargaba tsakanin ƴan kasuwa ƴan ƙasashen waje, musamman ƴan Burundi.

    Sai dai gwamnatin ta yi gargaɗin cewa bai kamata a tsoratar da baƙin haure ba.

  11. Hare-haren Houthi sun dakatar da ayyuka a wasu cibiyoyin makamashi a Saudiyya

    An dakatar da ayyuka a wasu cibiyoyin makamashi a Saudiyya bayan hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da ƴan Houthi masu samun goyon bayan Iran suka kai daga Yemen.

    Mahukuntan Saudiyya sun ce mutane sama da mutum 70 sun jikkata, yayin da hare-haren suka shafi wurare da dama, ciki har da sansanin sojin sama na King Khalid, da filin jirgin saman Abha da wasu cibiyoyin kamfanin mai na Aramco mallakin gwamnatin kasar.

    Ma'aikatar Makamashin Saudiyya ta ce hare-haren sun haddasa gobara a wasu wurare, lamarin da ya tilasta dakatar da wasu ayyuka na dan lokaci domin gudanar da bincike da tabbatar da tsaron cibiyoyin.

    A nasu bangaren, ƴan Houthi sun ce hare-haren ramuwar gayya ne kan hare-haren sama da Saudiyya ta kai a Yemen.

    A halin da ake ciki, an samu ƙazamin faɗa tsakanin ƴan Houthi da dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen, inda kusan mutane 19,000 suka tilastawa barin gidajensu.

  12. Birtaniya ta amince Isra'ila ta aikata 'kisan kiyashi' a Gaɓar Yamma

    Ed Miliband

    Asalin hoton, House of Commons

    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar ta amince cewa Isra'ila na aiwatar da kisan kiyashi a wasu sassan Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

    Da yake jawabi a Majalisar Dokokin Birtaniya, Miliband ya ce gwamnatin Isra’ila ta yi ta “rufe ido” kan irin wannan lamari.

    Ya ce gwamnatin Birtaniya ta daɗe tana kallon matsugunan Isra’ila da ke Yammacin Kogin Jordan a matsayin waɗanda ba su halatta ba.

    Miliband ya kuma sanar da cewa gwamnatin Birtaniya ta ɗauki matsaya a hukumance cewa mamayar Yammacin Kogin Jordan ba ta dace da doka ba.

    Ya kuma sanar da cewa Birtaniya za ta haramta shigo da kayayyakin da ake samarwa daga matsugunan Isra’ila da ke Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

  13. Birtaniya za ta hana shigo da kayayyakin da aka samar a matsugunan Isra'ila

    Andy Burnham

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Birtaniya ta shirya hana shigo da kayayyakin da aka samar a matsugunan Yahudawa da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ciki har da kayayyakin amfanin gona.

    Matakin na daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin Birtaniya ke shirin yi kan manufofinta da Isra'ila, yayin da take ƙara matsa lamba kan batun faɗaɗa matsugunan Yahudawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    A makon da ya gabata, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya shaida wa 'yan majalisar cewa gwamnati na shirin sauya wasu daga cikin tsare-tsaren da ke tsakaninta da Isra'ila.

    Gwamnatocin Birtaniya da suka gabata sun bayyana matsugunan Yahudawan a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye a matsayin waɗanda suka saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da cewa faɗaɗa su na iya kawo cikas ga samun zaman lafiya da kafa ƙasashen biyu.

    Sai dai ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi gargaɗin cewa Birtaniya na shirin tafka kuskure, yana mai cewa za ta fuskanci martani kan matakin.

    Firaministan Birtaniya, Andy Burnham, ya kuma tattauna da Shugaban Amurka Donald Trump da wasu muhimman ƙasashen ƙawance, ciki har da Qatar, a ranar Litinin, domin sanar da su shirin gwamnatin Birtaniya kan yankin.

  14. Nijar ta tsaurara dokokin duba lafiyar motocin sufuri, Daga Tchima Illa Issoufou

    Shugaban Nijar Tiani

    Asalin hoton, AFP

    Ma’aikatar Sufuri da Jiragen Sama ta Jamhuriyar Nijar ta sanar da sabbin matakai na duba lafiyar motocin sufuri, domin inganta tsaron ababen hawa a kan tituna.

    A karkashin sabbin dokokin, daga yanzu za a gudanar da dukkan gwaje-gwajen fasaha na motocin sufuri ne kawai a Cibiyar Haɗin Gwiwa ta Yamai, wadda ita ce cibiya guda ɗaya tilo da ke da kayan aikin zamani da takardun shaidar da hukumomi suka amince da su.

    Bugu da ƙari, an bukaci kamfanonin sufuri su tanadi lokacin kai motocinsu domin gwaji tsakanin kwanaki 15 zuwa 30 kafin wa’adin takardar shaidar da suke da ita ya kare.

    Haka kuma, motocin bas da suka taso daga yankuna zuwa Yamai za su yi tafiyar ne ba tare da fasinjoji a cikinsu ba, tare da kasancewa dauke da takardar izinin wucewa ta musamman da hukumomin yankin da suka fito suka bayar.

  15. Kanada ta fara aiwatar da harajin ramuwar gayya kan kayayyakin Amurka

    Canada da Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon harajin da Kanada ta ƙaƙaba wa wasu kayayyakin Amurka da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 20 ya fara aiki.

    Hakan na zuwa ne bayan da tattaunawar ciniki tsakanin Amurka da Kanada ta wargaje a watan da ya gabata, lamarin da ya ƙara tsananta taƙaddamar ciniki tsakanin ƙasashen biyu.

    A baya, Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba harajin kashi 50 kan wasu kayayyakin da Kanada ke fitarwa zuwa Amurka, waɗanda darajarsu ta kai kusan dala biliyan 20. Kayayyakin sun haɗa da sandunan wasan ƙanƙara na hockey da siminti.

    Matakan ramuwar gayya da Kanada ta sanar sun haɗa da harajin kashi 15, 25 da 50 kan kayayyakin Amurka da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 20, ciki har da ƙarafa, kayan noma, kayan lantarki da sauran kayayyaki.

    A yayin da taƙaddamar ke ƙara tsananta, Shugaba Trump ya kuma yi barazanar hana sayen jiragen saman da kamfanin Kanada na Bombardier ya ƙera.

  16. An yi jana’izar mijin Shugabar Tanzania da ya rasu sakamakon ciwon zuciya

    TANZANIA

    Asalin hoton, STATE HOUSE TANZANIA

    An yi jana’izar Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan, a Kizimkazi da ke Zanzibar.

    Marigayin, wanda aka haifa a ranar 1 ga Janairu, 1946, ya rasu ne ranar Litinin 7 ga Satumba bayan fama da ciwon zuciya.

    Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, ya sanar da rasuwar, inda ya ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu da misalin ƙarfe 8 na safe agogon ƙasar, a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, inda yake karɓar magani.

    Tanzania

    Asalin hoton, State House Tanzania

    Tanzania

    Asalin hoton, State House Tanzania

    Marigayin ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya huɗu da jikoki 15.

    Babban Limamin Zanzibar, Sheikh Saleh Omar Kaabi, ne ya jagoranci sallar jana’izar, wadda manyan shugabannin siyasa da na addini suka halarta.

    Tanzania

    Asalin hoton, State House Tanzania

    Bayanan hoto, Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, da Shugaban Zanzibar, Hussein Mwinyi.
  17. Bene mai hawa uku ya ruguje a Abuja

    Bene mai hawa uku ya ruguje a Abuja

    Asalin hoton, Lere Olayinka/FB

    Wani bene mai hawa uku ya ruguje a yankin Wuse Zone 4 da ke Abuja, sa'o'i kaɗan bayan sashen kula da ci gaban birane ya rufe ginin tare da umartar mutanen da ke cikinsa su fice.

    Hotuna da bidiyon da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna ginin ya ruguje, yayin da mutane suka taru a wurin bayan faruwar lamarin.

    Ba a bayyana dalilin rugujewar ginin nan take ba.

    Haka kuma, ba a tabbatar da ko akwai mutane a cikin ginin lokacin da ya ruguje ba, ko kuma ko akwai wadanda tarkacen ginin ya danne.

    Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta ce ta samu kiran gaggawa game da lamarin da misalin ƙarfe 7:45 na daren Litinin.

    A cewar kakakin rundunar a Abuja, Josephine Adeh, an tura tawagar ’yan sanda zuwa wurin domin kai agajin gaggawa.

    Lere Olayinka

    Asalin hoton, Lere Olayinka/FB

    Lere Olayinka

    Asalin hoton, Lere Olayinka/FB

  18. INEC ta sanya ranar zaɓukan cike gurbi a Kano, Gombe, Bauchi da Delta

    INEC

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC, ta sanya ranar 19 ga watan Satumba domin gudanar da zaɓukan cike gurbi guda biyar a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta.

    Sakataren yaɗa labarai na shugaban INEC, Tunde Oketola, ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, cewa zaɓukan sun ƙunshina kujerar majalisar wakilai ta tarayya guda ɗaya da kuma kujerun majalisun jihohi huɗu.

    Ya ce za a gudanar da zaɓen kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta jihar Gombe.

    Zaɓukan kujerun majalisar jihohin kuma za su gudana a mazabar Disina da Sakwa a jihar Bauchi, sannan Udu a jihar Delta da Dawakin Kudu a jihar Kano.

  19. Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Jamus kan nasarar jam’iyyar masu ra’ayin riƙau

    Saxony-Anhalt protest

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar Brandenburg da ke birnin Berlin, domin nuna adawa da nasarar da jam’iyyar AfD mai ra’ayin riƙau ta samu a zaɓen jihar Saxony-Anhalt.

    Masu zanga-zangar sun yi kira da a haramta jam’iyyar, wadda hukumomin leƙen asirin Jamus suka ayyana a matsayin mai tsattsauran ra'ayi.

    Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce ya firgita da sakamakon zaɓen, inda AfD ta samu kusan kashi 44 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a Saxony-Anhalt.

    Wakiliyar BBC ta ce abin da ake gani shi ne yadda mutane da dama suka gaji da jam’iyyun gargajiya da suka saba bai wa ra'ayinsu.

    Jam’iyyar AfD ta ce za ta nemi goyon bayan sauran jam’iyyu ko kuma wasu daga cikin ƴan majalisar jihar domin samun damar kafa gwamnati a Saxony-Anhalt.

  20. NAHCON ta tunatar da maniyyata ranar da za a rufe biyan kuɗin Hajjin 2027 a Najeriya

    Hajj

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa ranar 26 ga Satumba ce wa'adin kammala rajista da biyan kuɗin aikin Hajjin.

    Hukumar ta yi wannan tunatarwa ne a wasu saƙonni da ta wallafa a safukanta na sada zumunta, inda ta buƙaci maniyyatan da ba su kammala rajista da biyan kuɗaɗen ba da su yi hakan kafin cikar wa'adin.

    NAHCON ta ce wa'adin shi ne jadawalin da hukumomin Saudiyya suka bayar domin shirye-shiryen aikin Hajjin 2027.

    Hukumar ta ce kammala wannan aiki cikin lokaci ya zama wajibi domin daidaita bayanan maniyyata da kuma rabon kujerun jirgi, tana mai gargaɗin cewa rashin cika wa'adin na iya janyo rasa guraben Hajjin da aka ware wa maniyyata.

    NAHCON ta kuma buƙaci hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da maniyyatan da kansu su kammala dukkan matakan da ake buƙata kafin lokacin Hajjin.

    A watan Agusta, NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajjin 2027, inda maniyyatan da za su tashi daga Maiduguri da Yola za su biya N7,560,822, yayin da na yankin Arewa za su biya N7,672,822.

    Maniyyatan yankin Kudu kuwa za su biya N7,882,822.