KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da ƙudirin tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasa

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da ƙudirin tsawaita wa'adin shugaban ƙasa daga shekara biyar zuwa bakwai, wanda zai bai wa shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da yin mulki har zuwa shekara ta 2030.

    Fiye da yan majalisa 200 ne suka kad a ƙuri’ar amincewa da daftarin dokar a ranar Alhamis, wanda ya zarce matakin da ake buƙata na samun kashi biyu bisa uku domin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Ƙudirin ya kuma soke batun gudanar da zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye, inda daga yanzu ƴan majalisa ne za su riƙa zaɓen shugabannin ƙasar.

    Mnangagwa, mai shekara 83, ya karɓi mulki ne a shekarar 2017 bayan hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Robert Mugabe tare da goyon bayan sojoji - kuma ya ci zaɓe a 2018 da 2023 da ake takaddama a kai.

    A yanzu ƙudirin ya nufi majalisar dattiawa, inda kuma ake sa ran za a amince da shi kafin shugaban ƙasa ya zartar da shi a matasyin doka.

  2. Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Amurka da ta ƙunshi kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Lebanon, ana ci gaba da musayar wuta tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah da ke cikin Labanon.

    Jami'an kiwon lafiya na ƙasar Lebanon sun sanar da cewa hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 18.

    Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa ta kashe mayaƙan Hezbollah da dama a hare-haren da ta kai kan wurare 80 a faɗin ƙasar.

    Har ila yau, a cewar sojojin Isra'ila, kwamandan bataliya ta 52 masu sulke tare da sojojinsa uku sun mutu a musayar wuta da ƙungiyar Hezbollah.

  3. Ministocin harkokin wajen Saudiyya da Pakistan da Turkiyya za su gana a Masar

    Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa, ministan harkokin wajen ƙasar, Badr Abdel Ati, zai karɓi baƙuncin takwarorinsa na Pakistan da Saudi Arabia, da kuma Turkiyya a gobe.

    A cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Masar ɗin ta fitar, "Mista Abdel Baty zai gana a ranar Lahadi a wani taro mai ɓangarori huɗu da Faisal bin Farhan da Hakan Fidan, da Ishaq Dar, da ministocin harkokin wajen Saudiyya, Turkiyya, da kuma Pakistan.

    Wannan taron za a biyo bayansa da tattaunawa mai zurfi da kuma taron manema labarai na hadin gwiwa."

    Sanarwar ba ta ambaci maƙasudin tattaunawar ba, amma ƙasashen huɗu na shiga tsakani a ƙoƙarin samun maslaha a yaƙin Gabas ta Tsakiya.

    Ministocin waɗannan kasashen huɗu sun yi ganawarsu ta ƙarshe ne a watan Afrilu (watanni uku da suka gabata) a gefen taron diflomasiyya a birnin Antalya na ƙasar Turkiyya.

  4. Za a gurfanar da kyaftin ɗin Morocco bisa zargin fyaɗe

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kyaftin ɗin Morocco Achraf Hakimi zai gurfana a gaban kotu bisa zargin aikata fyade, kamar yadda masu gabatar da ƙara na Faransa suka tabbatar.

    Wata mata ta zargi ɗan wasan bayan Paris St-Germain da yi mata fyade a gidansa da ke babban birnin Faransa a shekarar 2023, lokacin tana da shekara 24.

    Ofishin mai gabatar da ƙara a Nanterre, wani yanki na yammacin Paris, ya fara bincike na farko a cikin Maris 2023.

    Wani alƙali mai bincike ya ba da umarnin a gudanar da shari'a a watan Fabrairun 2026 kuma kafofin yaɗa labarai na Faransa sun ruwaito cewa Hakimi, mai shekaru 27, bai yi nasara a yunkurinsa na ganinin an yi watsi da ƙarar ba.

    Hakimi, wanda ke shirin jagorantar tawagarsa a wasansu na biyu na gasar cin kofin duniya da Scotland a yau Juma'a, ya sha musanta zargin.

    Hakimi, wanda ya buga wa Morocco wasanni 97, ya buga wasansa na farko a shekarar 2016 yana da shekaru 17.

    Ya kasance jigo a tawagar Morocco wadda ta zama ƙasa ta farko a Afirka da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.

  5. An ɗage tattaunawar da za a yi tsakanin Amurka da Iran a Switzerland

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An ɗage wani sabon zagayen tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Iran bayan mataimakin shugaban ƙasar JD Vance ya jinkirta ziyarar da ya shirya zuwa ƙasar Switzerland.

    Fadar White House ta sanar da yammacin ranar Alhamis cewa Vance ba zai je tattaunawar ba.

    Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta janye ƙawanyar da ta yi wa Iran bayan da ƙasashen biyu suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya da nufin kawo ƙarshen rikicin.

    Yayin da yarjejeniyar ta kuma ce ya kamata a kawo ƙarshen faɗa a Lebanon, ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ce hare-haren da Isra'ila ta kai ya kashe aƙalla mutum 18 a kudancin ƙasar cikin dare.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, kuma an kashe sojojinta huɗu.

    Sa'o'i kaɗan kafin fadar White House ta fitar da sanarwar, kafofin yaɗa labaran Lebanon masu alaƙa da ƙungiyar Hezbollah sun ruwaito cewa, an dakatar da tattaunawar saboda hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa.

  6. Kotu ta ɗaure iyayen ɗan bindigan da ya harbe yara tara a Serbia

    ...

    Asalin hoton, Slobodan Maricic/BBC Serbian

    An ɗaure iyayen wani yaro da ya harbe yara tara da wani mai gadi a wata makarantar firamare a Sabiya, a wani shari'a da aka sake yi a birnin Belgrade.

    Yaron yana da shekar 13 da haihuwa a lokacin da ya harbe wasu yara ƴan mata bakwai, da namiji ɗaya da wani mai gadi a makarantar Vladislav Ribnikar da ke Belgrade a shekarar 2023.

    Wata yarinya kuma ta mutu daga baya a asibiti.

    Wanda ya yi harbin ya kasance a ƙarƙashin shekarun da za a kama shi da aikata laifuka kuma an tura shi cibiyar kula da masu lallurar ƙwaƙwalwa, amma an zargi iyayensa Vladimir da Miljana Kecmanović da rashin kulawa da cin zarafin ƙaramin yaro, yayin da ake zargin mahaifinsa da aikata babban laifi da ya shafi lafiyar jama'a.

    An yanke wa Kecmanović hukuncin ɗaurin shekara 14 da watanni shida a gidan yari ranar Alhamis, matarsa ​​kuma an daure ta na tsawon shekara biyu da wata 11.

    Ba kasafai ne ake samun harin bindiga a ƙasar Serbia ba, shi ya sa ƙasar ta kaɗu a lokacin da aka kai harin Belgrade a ranar 3 ga watan Mayun 2023. Yaron ya dauko bindigogi guda biyu daga ma'ajiyar mahaifinsa, ya sanya su a cikin jakarsa ya tafi makaranta, inda ya buɗe wuta a cikin zauren makarantar da kuma wani aji.

  7. Isra'ila ba za ta janye daga kudancin Lebanon ba - Natanyahu

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sake jaddada cewa ba shi da niyyar janye sojojin Isra'ila daga kudancin ƙasar Lebanon da kuma abin da ake kira "yankunan da ta dauka matsayin shingen tsaro."

    Mr. Netanyahu, wanda mambobin majalisarsa suka yi kakkausar suka kan yarjejeniyar Amurka da Iran, ya ce "Kamar yadda muka maido da tsaro da wadata a yankunan da ke kan iyaka da Gaza, za mu kuma maido da tsaro da wadata a birane da ƙauyukan arewacin Isra'ila."

    Ya ƙara da cewa: Wannan yana buƙatar kiyaye yankin tsaro a kudancin Lebanon, kuma saboda haka, ba za mu ja da baya daga nan ba matuƙar tsaron Isra'ila na buƙatar haka.

    A wani ɓangare kuma, yayin da Iran ta yi niuni da tanade-tanaden yarjejeniyar fahimtar juna, ta jaddada cewa, tilas ne a ɗauki matakin tsagaita wuta a ƙasar Lebanon da kuma tabbatar da yankin ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin ginshikan tabbatar da tsagaita wuta.

  8. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 16 a kudancin Lebanon

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar Lebanon ya ruwaito cewa an kashe aƙalla mutane 16 a hare-haren da Isra’ila ta kai a garuruwan Sharqiya, da Harouf da Kafr Raman da Kafr Jouz, da Kafr Sair da ke kudancin ƙasar.

    A cewar kafar yaɗa labaran ƙasar, tun da sanyin safiyar yau ne sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare da makaman roka kan birnin Nabatie da kewaye.

    Wannan dai na faruwa ne duk da cewa sakin layi na farko na yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka ya ba da tabbacin kawo ƙarshen ayyukan soji nan take a duka fagagen daga ciki har da ƙasar Labanon.

    Rashin jituwa tsakanin Amurka da Isra'ila kan dakatar da kai hare-hare a kudancin ƙasar lebanon na ci gaba da ƙamari.

    Mataimakin shugaban Amurka JD Vance, ya shaidawa wani taron manema labarai jiya cewa, Donald Trump shi ne kaɗai shugaban ƙasa daya tilo a duk faɗin duniya da ke nuna tausayawa da goyon bayan ƙasar Isra’ila a wannan lokaci, kuma shi ma ya kasance shugaban ƙasa mafi ƙarfi a duniya.

    Ministan tsaron cikin gida na Isra'ila Itamar Ben-Giver yayin da yake mayar da martani ga kalaman Mr. Vance ya ce: "Duk wanda ya goyi bayanmu zai amfana, kuma duk wanda ya juya mana baya zai sha wahala. Don haka kada ku yi mana barazana."

  9. Tsoffin Janar-Janar sun yi kira da a ingata harkar tsaro bayan rasuwar Rabe Abubakar

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Tsoffin hafsoshin sojin Najeriya kuma abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (rtd) sun yi kira da a yi wa tsarin tsaron Najeriya garambawul bayan rasuwar tsohon Janar ɗin a hannun wasu ƴan bindiga da suka sace shi a jihar Katsina.

    Sun yi wannan kira ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin wani taron manema labarai a Kaduna wanda Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (rtd) ya yi magana a madadin abokan aiki da kuma makusantan marigayin.

    Da ya ke magana yayint aron Brig.-Janar Maharazu Tsiga (rtd), tsohon darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ya yi kira da a ɗauki ƙwararan matakai don magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.

    A cewar sa, ana buƙatar a ƙddamar da dabarun da za a bi don wargaza ayyukansu da kuma dawo da zaman lafiya.

    "Waɗannan mutane ƴan adam ne kamar mu; suna tsoron mutuwa kuma suna tsoron a fuskance su gaba da gaba. Idan muka kawar da tsoro ta a zukatan mu kuma muka fuskanci su da gaske, za mu sami sakamako mai ma'ana fiye da tattaunawar da babu ranar ƙarewa," in ji shi.

    Da yake bayanio kan lokacin da ya kwashe a hannun ƴan bindiga, Tsiga ya ce da wuya ƙungiyoyin ƴan ta'adda da yan bindiga su miƙa wuya bisa radin kansu ta hanyar tattaunawa.

  10. Bolivia ta ƙulla yarjejeniyar dala miliyan 20 da Amurka don yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi

    ...

    Asalin hoton, Cancillería Bolivia

    Bolivia ta ce ta rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta haɗin gwiwa da Amurka domin yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce a ƙarƙashin yarjejeniyar, Amurka za ta samar da dala miliyan 20 (£15m) domin horas da sojojin Bolivia da kuma samar da kayan aiki a wani ɓangare na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

    Yarjejeniyar dai ita ce alama ta baya-bayan nan da ke nuna yunƙurin farfado da dangantaka tsakanin kasashen - shekaru 18 bayan da shugaban ƙasar na wancan lokaci Evo Morales ya kori hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Amurka daga ƙasar, wadda ita ce ƙasa ta uku a duniya wajen samar da ganyen Coca da ake amfani da shi wajen haɗa hodar iblis.

    A ƙarkashin sabon shugaba Rodrigo Paz, Bolivia ta shiga wani shirin tsaro da Amurka ke jagoranta a yammacin duniya.

    A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Amurka ya tabbatar da cewa "Amurka za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Bolivia domin ba da horo, da kayan aiki, da sauran nau'ukan tallafi".

  11. Amurka ta ɗage shingen sojojin ruwanta daga gaɓar tekun Iran

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta janye shingen sojojin ruwa da ta kafa a gaɓar tekun Iran bayan da ƙasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin gabas ta tsakiya.

    Cibiyar gudanar da al'amuran tsaro na Amurka ta tabbatar da kawo ƙarshen takunkumin a shafin X "bisa ga umarnin shugaban ƙasa", kuma ta ce wasu jiragen ruwa na Amurka za su ci gaba da kasancewa "a wasu sassan yankin".

    Jim kaɗan bayan haka, Jagoran Addinin Musulunci na Iran Mojtaba Khamenei ya ce ya amince da yarjejeniyar da Amurka duk da cewa ra'ayinsa ya bambanta, ba tare da yin wani ƙarin haske ba.

    Ya ce ya amince da yarjejeniyar ce bayan da shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya ba da tabbacin cewa zai kare haƙƙin al'ummar ƙasar.

    Wannan shi ne karon farko da Khamenei ya yi tsokaci kan yarjejeniyar.

    Bai fito bainar jama'a ba tun bayan hawansa karagar mulki a watan Maris ɗin da ya gabata bayan kisan mahaifinsa kuma magabacinsa Ayatullah Ali Khamenei a harin da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu wanda ya haifar da yaƙin.

  12. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Za ka iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.