Abubuwa uku da za su iya wargaza yarjejeniyar Amurka da Iran

Asalin hoton, Getty Images/BBC
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Bayan shafe makwanni ana tattaunawa, Amurka da Iran sun cimma matsaya ta farko - sai dai tuni hankali ya karkata ga gagarumin ƙalubalen da ke tattare da yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin.
A ranar Laraba, manyan jami'an Amurka sun karanta wata yarjejeniyar fahimtar juna mai ɗauke da sharuɗɗa 14 ga manema labarai, ciki har da BBC.
Shugaban Amurka Donald Trump da na Iran Masoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar gabanin lokacin da aka tsara - a baya dai an shirya ƙulla yarjejeniyar a hukumance ne a ƙasar Switzerland ranar Juma'a - wanda zai ba da damar cimma "yarjejeniyar ƙarshe" cikin "kwana 60, wanda za a iya tsawaitawa tare da amincewar juna."
Yarjejeniyar ta gindaya sharuɗɗan fara ɗage shingen da sojojin ruwan Amurka suka yi, da maido da jigilar kaya da danyen man fetur ta mashigar Hormuz, da kuma tattaunawa kan ɗage "dukkan takunkuman" da ke kan Iran. Takardar ta kuma zayyana tsare-tsaren kafa wata gidauniya ta aƙalla dala biliyan 300 (£224bn) don sake gina Iran da farfaɗo da tattalin arzikinta, tare da sabunta alƙawarin da Tehran ta yi na yin watsi da batun ƙera makamin nukiliya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗin cewa wannan yarjejeniyar "ba ta ƙarshe ba ce" kuma ya ce Amurka za ta iya "komawa ta ci gaba da jefa bama-bamai" idan yarjejeniyar ta gaza aiki.
Kakakin majalisar dokokin Iran kuma babban mai shiga tsakani Mohammad Bagher Ghalibaf, ya shaida wa kafar yaɗa labaran ƙasar cewa har yanzu ba a amince da Amurka ba , kuma Iran ta "zauna cikin shirin ko ta kwana".
A nan ga uku daga cikin manyan barazanar da za su iya kawo cikas ga tattaunawar, a cewar masana:
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Lebanon

Asalin hoton, Reuters
Ɓangarorin biyu sun ba da sanarwar "katse ayyukan soji nan take kuma na dindindin a dukkan fagagen daga, ciki har da na Lebanon", in ji Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu shiga tsakani, a lokacin sanarwar yarjejeniyar farko.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yarjejeniyar, wadda aka karanta a ranar Laraba, ta kuma haɗa da Lebanon, da tabbatar da "yancinta da ikonta kan yankunan ƙasarta".
Sai dai kuma Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a kan Lebanon - ko da bayan Trump ya ce ya kamata takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kasance "ya yi taka tsan-tsan kan batun Lebanon" a taron G7 da aka yi a Faransa.
A ranar Larabar da ta gabata ce jiragen yaƙin Isra'ila suka kai farmaki a yankin Nabatieh al-Fowqa da kuma wajen makwabciyarta Kfar Tebnit, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar Lebanon NNA.
Ban da haka kuma jami'an Amurka sun ce yayin da ƙasar Lebanon ke cikin tsarin tsagaita wuta, janyewar sojojin Isra'ila daga yankin na Lebanon ba ya cikin sharuɗɗan yarjejeniyar. Isra'ila za ta ci gaba da tabbatar da ƴancin kariyar kai, in ji su.
Sai dai Iran ta ce kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Labanon wani ɓangare ne na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi da ba za ta haƙura da shi ba.
Ƙungiyar HEzbollah da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon ta yi maraba da wannan matsayi. Ofishin hulɗa da manema labarai na ƙungiyar Hezbollah ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, Iran ta tabbatar wa ƙawayenta cewa za ta buƙaci janyewar sojojin Isra'ila gaba ɗaya daga Lebanon a mataki na gaba.
Ita ma Isra'ila ta fito fili ta yi nuni da cewa, ba ta ganin cewa za ta iya amincewa da Iran fassarar da Iran ta yi wa yarjejeniyar. Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya ce sojojin Isra'ila za su ci gaba da kasancewa a yankunan ƙasar Lebanon "ba tare da ƙayyade lokaci ba" ya kuma ya yi gargadin cewa za su kai farmaki da ƙarfi idan Iran ta kai wa Isra'ila hari ta dalilin Lebanon.

Asalin hoton, Getty Images
Tel Aviv ta kasance "babban mai zagon ƙasa" ga ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya, in ji Dr H.A. Hellyer, masanin kimiyyar siyasa a Cibiyar Royal United Services, da ke Burtaniya.
Ya ƙara da cewa: "Ayyukan soji na Isra'ila, ko dai wadda ta yi kan Iran kkai-tsaye ko kuma wadda ta ke yi ta hanyar ɓarnar da ta ke ci gaba da yi a Lebanon, ita ce babbar barazana ga ci gaban ayyukan diflomasiyya."
Tsarin zai iya rugujewa kafin "tun ma kafin a fara tattaunawa mai ma'ana kan batun nukiliya" idan har aka tsokani Tehran ta shiga faɗa kai tsaye, in ji Hellyer.
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi maraba da yarjejeniyar ta farko, yana mai cewa yana fatan za ta rikiɗe zuwa "matakai masu inganci waɗanda za su kawo ƙarshen faɗace-faɗace".
Ga ita kanta Lebanon, sakamakon yaƙin ya yi muni matuƙa. Fiye da mutane 3,700 ne aka kashe, tare da raba mutane kusan miliyan ɗaya da muhallansu, sannan akasarin yankunan kudancin ƙasar sun fuskanci ɓarna mai yawa.
Shirin nukiliyar Iran

Asalin hoton, Getty Images
Wani abin da ya ɗaure kai shi ne sinadarin Uranium da Iran ke da shi, duk da cewa Trump ya ce babu gaggawar ƙwace shi.
A cewar Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Iran ta tara kusan kilogiram 400 na Uranium wanda aka inganta zuwa kashi 60% a bara. Don haɗa makamin nukiliya.
Tehran dai ta ci gaba da tabbatar da cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kuma ta nanata a yarjejeniyar cewa ba za ta nemi ƙera makaman ƙare dangi ba.
Duk da haka, mahimman batutuwa - gami da batun kula da sinadarin da ta ke da shi a ƙasa - an jinginar da su zuwa lokacin da za a ƙulla yarjejeniya ta ƙarshe, wadda har yanzu ba afara tattauna ta ba.
A ƙarƙashin yarjejeniyar nukiliyar 2015 da Shugaba Barack Obama ya ƙulla, Tehran ta ƙayyade inganta Uranium ɗin ta zuwa 3.67%. Bayan ficewar Amurka a cikin 2018 - a lokacin wa'adin Trump na farko - Iran ta faɗaɗa shirinta na nukiliya sosai.
Darin Selnick, tsohon mataimakin sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth, ya shaidawa shirin gidan rediyon BBC 4 cewa, shugaban zai "iya sake fara ayyukan soji" idan ya ji cewa Iran na sake inganta sinadarin uranium.
A halin yanzu, ana sa ran ɓangarorin biyu za su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki a cikin kwanaki 60 na tattaunawar: Iran ba za ta faɗaɗa ayyukanta na nukiliya ba, yayin da Amurka za ta ƙaurace wa ƙaƙaba sabbin takunkumai ko ƙara yawan sojojinta a yankin.
Mashigar Hormuz

Yarjejeniyar ta na kuma da niyyar sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, wanda ya tsaya cik tun a watan Fabrairu. Kafin yaƙin, kusan kashi 20% na albarkatun mai da iskar gas na duniya suna wucewa ne ta wannan hanyar jigilar kayayyakin.
Ta ce hanyar ruwan za ta sake buɗewa ne bayan sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Juma'a, inda ake sa ran ci gaba da gudanar da aiki cikin kwanaki 30, yayin da aka kawar da matsalolin fasaha da na tsaro, ciki har da nakiyoyin da Iran ta dasa a mashigar.
Yarjejeniyar ta ce mashigar ruwan ba za ta kasance kyauta ba na tsawon kwanaki 60 na farko, "daga Tekun Fasha zuwa Tekun Oman . Ta ƙara da cewa Iran za ta tattauna da Oman da sauran ƙasashen yankin Gulf kan yadda za a tafiyar da harkokin mashigar ruwan a nan gaba da kuma harkokin ruwa kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.
Wannan lamari ne da ke nuna yiwuwar cewa za a iya fara biyan kuɗaɗen wucewa ta mashigar a nan gaba.
Tuni dai Tehran ta nunar da cewa tana son taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da mashigar ruwan. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce za ta caji jiragen ruwa da ke wucewa a mashigar kudin hidima. Amma ba a san abin abin da wadannan kuɗaɗen za su kunsa ba.
Biyan harajin wucewa ta mashigar daio ba ya ƙunshe a cikin dokokin ƙasa-da ƙasa, amma dai ana bayar da damar karɓar kuɗi kan wasu ayyuka na musamman.
Sai dai ɓangaren Amurka ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa wucewa ta mashigar za ta kasance kyauta bayan tattaunawar.
Jami'in Amurka ya ce Iran na iya ƙoƙarin tabbatar da matsayinta, amma ƙasashen yankin Gulf ba za su amince da duk wani tsari da zai hana shiga ba tare da izini ba.
Trump ya ce Iran za ta yi aiki da "hankali" kuma ba za ta tilasta karɓar kuɗaɗe ba, saboda matakin na iya barazanar sake janyo ci gaban aikin soja. Amurka ta kuma yi imanin ƙasashen yankin Gulf ba za su taɓa amincewa da tsarin nan gaba da ya shafi biyan kudaɗen wucewa ba.
Har ila yau kwashe nakiyoyi na iya daukar makonni zuwa watanni," Admiral Mark Montgomery mai ritaya na sojojin ruwan Amurka ya shaida wa BBC.
Kamfanonin jigilar kayayyaki na iya tafiya cikin taka-tsantsan har sai sun tabbatar da ɗorewar tsagaita wutan.
"Sai an samu jajirtaccen direban jirgi ya wuce ta mashigar Hormuz, idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a yanzu," Martin Kelly na kamfanin EOS Risk Group ya shaida wa BBC Verify.
Hellyer ya yi gargadin cewa a halin yanzu dai yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ta kasance "takardar fahimta juna - tsarin tattaunawa, ba ƙuduri ba".
Ya ƙara da cewa "har yanzu akwai jan aiki a gaba."










