Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Talata 05/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan za mu rufe wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.

  2. Burkina Faso ta dakatar da tashar TV5 Monde ta Faransa

    Burkina Faso

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar kula da kafafen watsa labarai a Burkina Faso ta haramta watsa shirye-shiryen tashar talabijin ɗin Faransa wato TV5 Monde, inda take zarginta da yada bayanan da ba su dace ba dangane da rahotannin ta, kan hare-haren masu iƙirarin jihadi a kasar da kuma makwabciyarta Mali.

    Hukumar ta ce tashar ta aikata abin da ta kira maimaita saɓa dokokin aikin jarida da kuma ka’idojin aikin, musamman a rahotannin da suka shafi tsaro.

    A baya an taɓa dakatar da tashar har karo biyu a cikin shekaru biyu da suka gabata. Tun bayan da Kyaftin Ibrahim Traoré ya karbi mulki ta hanyar juyin mulki a watan Satumban 2022, hukumomin kasar sun dakatar ko haramta wasu kafofin watsa labarai na kasashen waje da dama.

    Har zuwa yanzu dai, ba a ji wani martani daga gidan talabijin ɗin ba.

  3. Hare-haren Rasha sun kashe aƙalla mutum 17 a Ukraine

    Akalla mutum 17 ne suka mutu a sabbin hare-haren da Rasha ta kai kan Ukraine. Hare-haren sun faru ne sa’o’i kadan kafin tsagaita bude wuta da Ukraine ta ayyana, da kuma wanda Rasha ta sanar gabanin bikin ranar tunawa da tarayyar Soviet da za a yi a birnin Moscow a ranar Asabar.

    Gwamnan yankin ya ce hare-haren sun lalata gidajen jama’a da kuma wuraren kasuwanci a birnin Zaparijiah, inda akalla mutum 12 suka mutu.

    Hare-haren sun haifar da shakku ga tunanin samar da dawwamamman zaman lafiya, ganin yadda ya haddasa gobara a wasu shaguna da motoci.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce akalla fararen hula biyar sun mutu sakamakon jefa bam daga sama da Rasha ta yi a yankin Donetsk.

  4. Shugaban Senegal ya kori mai ba shi shawara kan kafofin sadarwa

    Senegal

    Asalin hoton, PRESIDENCE SENEGALAISE

    A ƙasar Senegal, ana ci gaba da tattaunawa ne kan sallamar da shugaban ƙasar ya yi wa mai ba shi shawara kan kafofin sadarwa Ousseynou Ly, musamman a tsakanin ƴan jam'iyyar Pastef party wato Patriotes africains du Sénégal.

    Da yawa daga cikin ƴan jam'iyyar sun bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda Ly ya daɗe yana hidimta wa jam'iyyar, musamman wajen yaɗa manufofin Shugaba Bassirou Diomaye Faye da Firaminista Ousmane Sonko musamman a lokacin da suke kulle a gidan yari.

    ‎Wannan na zuwa ne kwan biyu bayan shugaban ya fito fili ya bayyanawa kafofin sadarwa wajen yana da ƴancin naɗawa da cire wanda ya ga dama a duk lokacin da ya so.

  5. Sabuwar ƙa'idar aikin hajjin 2026 da Saudiyya ta fitar

    Saudi

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Saudiyya sun gabatar da wata sabuwar ƙa'idar aikin hajjin 2026 ga maniyyatan bana.

    Tuni dai maniyyata daga ƙasashe daban-daban ciki har da Najeriya suka fara tashi zuwa Saudiyya domin sauke faralin.

    Aikin hajji na ɗaya daga cikin shika-shikan Addinin Musulunci, da aka wajabta wa wanda yake da damar yi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

  6. Akwai damarmakin zuba jari a ɓangarorin noma da al'adu a Najeriya - Wike

    Wike

    Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga ƙasashen tarayyar turai da su ƙara zuba jari tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumar birnin tarayya Abuja wajen bunƙasa harkokin al'adu da noma da yawon buɗe-ido da sauran su, domin moriyar ƙasashen su da Najeriya.

    Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da jakadun ƙasashen turai a Abuja a ranar Talata, inda ya ce zai cigaba da tabbatar da haɗin gwiwar ƙasashen da Najeriya domin ciyar da Abuja da ma Najeriya gaba.

    Taron, wanda shugaban jakadun ƙasashen tarayyar turai a Najeriya da ECOWAS Ambasada Gautier Mignot ya jagoranta, ya samu halartar jakadun Italiya da Faransa da Jamus da Spain da sauran su, inda ya bayyana Najeriya a matsayin babbar ƙawar kasuwancin ƙasashen turai.

    A nasa jawabin, Wike ya zayyano damarmakin kasuwanci da ke akwai a Abuja, inda ya ambata ɓangaren gidaje da nishaɗi da buɗe ido da noma a matsayin ɓangarori masu muhimmanci da za a iya zuba jari.

    Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar na ƙoƙari matuƙa wajen magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.

  7. Harin Boko Haram ya yi ajalin aƙalla mutum 23 a Chadi

    Chadi

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin Chadi ta ce wani harin ƴan Boko Haram ya yi ajalin aƙalla mutum 23, sannan wasu gommai suka jikkata.

    Sai dai duk da haka, rundunar ta ce ta samu nasarar daƙile harin ne da maharan suka kai a tsibirin Barka Tolorom da ke yankin Lake Chad.

    Dama can dai ana zargin yankin Tsibirin da zama matattara da ma maɓoyar ƙungiyoyi mayaƙa daban-daban, inda ake kitsa hare-hare.

    Mayaƙan Boko Haram na ƙara faɗaɗa hare-harensu zuwa wasu sassan ƙasashe daga Najeriya, inda suke kai hari har sansanonin soji.

  8. Ƴansanda sun tabbatar da kashe malamin addini a Pakistan

    A Pakistan kuma, ƴansanda sun ce wani fitaccen malamin addini ya rasa ransa sakamakon buɗe masa wuta da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai, a arewa maso yammacin kasar.

    Maulana Muhammad Idrees yana kan hanyarsa ta dawowa gida daga makarantar addini ne lokacin da wasu da ke kan babura biyu suka bude masa wuta, inda suka kashe shi nan take.

    Rahotanni sun ce jami’an ƴansanda biyu da ke cikin tawagarsa ta tsaro sun samu raunuka a harin.

    Babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin harin, amma ana danganta irin wadannan hare-hare da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin addini.

  9. Sudan ta mayar da jakadanta na Habasha gida

    Sudan ta sanar da mayar da jakadanta gida daga Habasha bayan zargin makwabciyar tata da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da taimakawa wajen kai harin jirgin sama mara matuki, a filin jirgin saman Khartoum, babban birnin ƙasar.

    Wakiliyar BBC ta ce harin na baya-bayan-nan ya haifar da fargaba a zuƙatan mazauna babban birnin, tare da ta'azzara rashin jituwa tsakaninta da Habasha.

    Gwamnatin sojin Sudan ta ce tana da ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa, dakarun RSF ne suka kaddamar da harin ta hanyar amfani da sararin samaniyar Habasha.

    Sai dai Habasha ta yi watsi da zargin, inda ta bayyana shi a matsayin wani sabon zargi maras tushe, tare da zargin Sudan da bai wa mayaƙan da ke adawa da ita makamai.

  10. Ƴan majalisar dokokin Romania na neman tsige Firaministan ƙasar

    Ƴan majalisar dokokin Romania sun kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da kuma neman tsige Firaministan ƙasar, Ilie Bolojan, yayin da aka yi a zaman majalisa.

    Babbar jam’iyyar, ta Social Democratic Party, ta fice daga ƙawancen gwamnati na jam’iyyu huɗu a watan da ya gabata, inda ta haɗa kai da bangaren masu ra’ayin riƙau domin neman a kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa.

    Shugaban ƙasar, Nicusor Dan, yanzu zai fara ƙokarin duba yiwuwar sake gina ƙawancen gwamnati karkashin sabon firaminista.

    Kafin kaɗa kuri’ar, ya amince cewa makonni masu zuwa za su iya kasancewa masu wahala, amma ya tabbatar da cewa Romania za ta ci gaba da riƙe matsayinta na goyon bayan Tarayyar Turai.

  11. Ƴan bindiga sun harbe wani malamin addinin Musulunci a Pakistan

    yan bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a Pakistan sun ce wasu ƴan bindiga sun harbe wani sanannen malamin addinin Musulunci a lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Sun ce Maulana Muhammad Idrees na kan hanyarsa ta zuwa gida ne daga wata makarantar koyar da addini a yayin da ƴan bindigar a kan babura biyu suka buɗe masa wuta inda suka kashe nan take.

    Ƴan sanda biyu da ke cikin tawagar masu bashi tsaro sun jikkata a harin da aka kai a yankin Charsadda.

    Zuwa yanzu babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai akan ɗaura lhakin ire iren waɗannan hare hare kan masu tsatsaurar ra'ayin addinin musulunci.

  12. An rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano

    Garo

    Asalin hoton, GARO/FACEBOOK

    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna, a fadar gwamnatin jihar. ‎

    ‎Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ce ta jagoranci rantsar da shi, a gaban manyan jami’an gwamnati da ‘yan majalisa da sarakunan gargajiya da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyya APC.

    ‎A makon da ya gabata ne majalisar dokokin Jihar ta amince da Murtala Garo, bayan tantancewar da aka yi masa.

    Gamnan Abba Kabir Yusuf ya ɗauki Murtala bayan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye muƙaminsa sakamakon dambarwar sauyin sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

  13. Za mu iya ƙaddamar da yaƙi ta ƙasa a Iran idan buƙatar hakan ta taso - Amurka

    kwamandan sojin Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    Kwamandan rundunar sojin Amurka Janar Dan Caine ya ce Iran ta kai hari kan dakarun Amurka fiye da sau 10 tun bayan cimma tsagaita wuta, amma a cewar sa hare haren ba su kai matsayin da zasu kai a gwabza faɗa ba.

    A yayin da ya ke jawabi a taron manema labarai a ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, Caine ya ce a shirye sojojin Amurka suke su ƙaddamar da hari ta ƙasa a kowane lokaci idan buƙatar hakan ta taso.

    Ya kuma ce za a ci gaba da ƙara yawan dakarun Amurka a yankin, kuma a shirye suke su faɗaɗa ayyukansu.

    Kwamandan sojin Amurkar ya kuma ce sun kai hari fiye da sau 100 kan jiragen ruwan Iran masu matuƙa da marasa matuƙa.

    A cewar sa sojojin Amurka 15,000 ne ke cikin shirin 'Project Freedom', shirin da Amurka ta ƙaddamar na yi wa jiragen kasuwancin da suka maƙale a Mashigar Hormuz rakiya, kuma za a ci gaba da aiwatar da shirin.

  14. Ba za mu bari Iran ta ci gaba da rufe Mashigar Hormuz ba - Hegseth

    Hegseth

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce 'ba faɗa Amurka ke nema ba'' amma '' ba za ta iya bari Iran ta toshe jiragen ƙasashen da babu ruwansu da kayayyakinsu daga bi ta Mashigar Hormuz ba''

    A yayin wata hira da manema labarai a ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon da ke gudana a yanzu, Hegseth ya ce shirin Amurka mai suna Project Freedom, an tsara shi ne da nufin '' kare jiragen ruwan da basu ji ba basu gani ba daga zaluncin Iran''.

    Da aka tambaye shi ko ayyukan da Amurka ke yi a Mashigar na nufin an dakatar da tsagaita wutar?

    Hegseth ya ce '' A'a, ba a kawo ƙarshen tsagaita wutar ba, wannan wani shiri ne na daban mai zaman kansa''.

    Sai dai ya buƙaci Iran da ta yi taka tsan-tsan a ayyukan da take yi kar ya kai ga ci gaba da yaƙin.

    Sakataren tsaron Amurkar ya kuma musanta cewa Isra'ila ce ta janyo Amurka cikin yaƙin, inda ya ce Shugaba Trump ya shiga yaƙin ne bisa ra'ayinsa da tunaninsa.

  15. Ƴan majalisar wakilan Najeriya 16 sun koma jam'iyyar NDC

    Majalisar wakilan Najeriya

    Asalin hoton, OTHER

    Aƙalla ƴan majalisar wakilan Najeriya 16 ne suka koma sabuwar jam'iyyar NDC, bayan ficewa daga jam'iyyar ADC.

    An sanar da sauya sheƙar ƴan majalisar ne a zaman majalisa na yau Talata.

    Ɗaya cikin ƴan majalisar da suka sauya shekar, Mukhtari Yarima da ke wakiltar Tarauni a jihar Kano, ya tabbatar wa da BBC.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne dai jiga-jigan adawar ƙasar biyu, Peter Obi da Kwankwaso suka sanar da sauya sheƙa daga jam'iyyar ADC zuwa NDC.

    Tun bayan ficewar ƴan siyasar biyu ne dai magoya bayansu ke tururuwar shiga sabuwar jamiyyar.

  16. Shugaban Kamaru ya ƙara wa'adin kansilolin ƙananan hukumomin ƙasar

    Biya

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya, ya kara wa'adin kansilolin kananan hukumomi, bayan da majalisar dokokin ƙasar ta ba shi ikon yin hakan a kwanakin baya.

    Matakin na nufin za a iya jinkirta zaɓen ƙananan hukumomi har zuwa watan Fabrairun baɗi.

    Wannan matakin na zuwa ne bayan da shugaban ƙasar ya tsawaita wa'adin ƴan majalisar dokoki zuwa watan Disamban shekarar da muke ciki bisa iƙirarin da gwamnatin ta yi na cewa ba ta da kuɗaɗen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da na yan majalisar.

    A hukumance an tsara gudanar da zaɓukan ne a bara, tare da na shugaban ƙasa da na yankuna.

    Sai dai gwamnatin mista Biya ta jinkirta zaben zuwa shekarar da muke ciki domin ta rage ayyukan hukumar zaɓ e da kuma rage kuɗin da gwamnati ke kashewa.

    Sai dai ƴan hamayya na ganin wannan wata dabara ce da jamiyyar CPDM mai mulki ke son amfani da ita domin ta cigaba da mulki da kuma hana wasu yan siyasa tsayawa takara.

    A baya dokar zaɓen ta ba shugaban ƙasa damar tsawaita wa'adin kansiloli har tsawon watanni 18, sai dai kundin tsarin mulkin da aka yi wa gyaran fuska ya cire wa'adin kuma ya bashi damar tsawaita wa'adin har lokacin da yake so.

    Wasu dai na ganin an jinkirta zaɓukan kananan hukumomi da yan majalisar dokokin ne da nufin kaucewa yiwuwar rasa kujerun jamiyya mai mulki, a dai dai lokacin da yan adawa ke kara ƙarfi.

  17. Fira ministan Pakistan ya yi Allahwadai da harin Iran kan UAE

    Shehbaz

    Asalin hoton, Getty Images

    Fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif, wanda ya kasance mai shiga tsakanin Amurka da Iran, ya ce ƙasarsa ta yi Allah wadai da babbar murya da hare haren makamai masu linzami da jirage maras matuƙa da Iran ta kai kan kayyayakin more rayuwa a Haɗaɗɗiyar daular larabawa a daren jiya.''

    Kamar yadda rahotanni suka bayyana, UAE ta ce ta kakkabo makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da dama a jiya Litinin, sai dai harin ya faɗa kan wata tashar samar da man fetir.

    A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Sharif ya ce '' yana da matuƙar muhimmanci a mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, domin ya bayar da damar yin tattaunawar diflomasiyya da za ta kai ga samar da zaman lafiya da daidaito a yankin.''

    Pakistan ɗin ta kuma ce har yanzu tana musayar bayanai tsakanin ɓangarorin biyu, tare da samar da damarmakin da za su ƙarfafa wa ɓangarorin yarda da juna, sai dai a cewar ta musayar wuta makamancin na jiya na dagula lissafi.

  18. Sudan ta zargi Ethiopia da Haɗaɗɗiyar daular Larabawa da kitsa kai mata hari

    Al Burhan

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Janar Abdel Fattah al-Burhan

    Sudan ta yi wa jakadanta da ke Ethiopia kiranye, bayan da ta zargi Addis Ababa da Haɗaddiyar daular Larabawa da kitsa kai hari da jirgi mara matuki kan filin jirgin sama na Khartoum.

    Zargin na zuwa ne bayan jerin wasu hare hare da jirage maras matuka da aka kai a jiya Litinin, waɗanda kuma suka shafi wasu sansanonin soji da ke Khartoum.

    Da safiyar yau Talata ne ministan harkokin wajen Sudan Moheiddin Salem sa kuma kakakin sojin ƙasar Asim Awad Abd al Wahab suka ce suna da shaidu masu karfi kan cewa an harbo jirage marasa matukan ne daga filin jirgin saman Bahir Dar da ke Ethiopia.

    Sai dai gwamnatin Ethiopia ta yi watsi da zarge zargen, inda tace basu da tushe balle makama.

    Gwamnatin ta ce ƙasashen Ethiopia da Sudan na da daɗɗaɗiyar tarihi, hakan ne ma yasa ta ƙi ta bayyana wasu manyan laifukan keta ƴancin iyakokinta da tsaron ƙasarta da wasu daga cikin masu yaƙin basasar Sudan ɗin suka yi.

    Daga ciki har da tallafawa mayaƙan sa kai na TPLF da kuɗaɗe da makamai da sojojin Sudan ke yi, wanda ke taimaka musu wajen yin kutse a yammacin Ethiopia.

  19. Mutum shida sun mutu a sabbin hare haren Rasha a Ukraine

    yadda gidaje suka lalace a ukraine bayan harin Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Hare haren Rasha da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami sun hallaka mutum biyar a yankin Poltava da ke tsakiyar Ukraine.

    Ma'aikata uku da masu aikin ceto biyu ne suka mutu a harin da aka kai wata cibiyar sarrafa iskar gas.

    Shugaba Zelensky ya ce ƙarin mutum ɗaya ya kuma mutu a wani harin cikin dare a yankin Kharkiv.

    Gwamnan yankin Leningrad na Rasha, Alexander Drozdenko, ya ce harin jirgi mara matuƙi ya tayar da gobara a wani yanki mai masana'antu da ke birnin Kirishi.

    Moscow ta ce na'urorinta na kare sararin samaniya sun lalata kusan jirage maras matuƙa ɗari uku cikin dare.

    Rasha da Ukraine sun ce za su tsagaita wuta don ƙashin kansu a kwanaki masu zuwa.

  20. Za a soma jigilar maniyyata aikin Hajjin bana na jihar Kano nan da mako guda

    Maniyyata aikin hajji suna shiga jirgi

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar kula da jin ɗaɗin alhazai ta jihar Kano ta sanar da ranar 14 ga watan Mayun 2026 a matsayin ranar da za a soma jigilar maniyyata daga jihar zuwa Saudiya domin aikin hajjin 2026.

    A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Sulaiman A Dederi ya fitar, shugaban hukumar Abubakar Ibrahim Matawalle ya sanar da ranar ne a yayin rufe taron bita kan aikin Hajji da aka gudanar a makarantar koyar da larabci da ke Kano.

    Ya ce an sanya ranar ne bayan da hukumar alhazai ta ƙasar ta fitar da jadawalinta, inda ya ƙara da cewa an zaɓi kamfanin Max Air a matsayin wanda zai yi jigilar maniyyata na jihar.

    Matawalle ya kuma ce hukumarsa ta kammala duk wani shiri domin tabbatar da kwashe dukkaninsu lami lafiya.

    Hukumar ta kuma buƙaci maniyyatan su ci gaba da bitar karatun da aka yi musu domin su fahimci yadda za su gudanar da ibadar har ta kasance karɓaɓɓiya.

    Hakazalika an buƙace su da su tabbatar sun bi dokokin da Saudiyya da Najeriya suka gindaya kan gudanar da aikin Hajjin bana.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne aka soma jigilar maniyyatan, inda aka soma da maniyyata 474 daga jihar Kogi waɗanda suka tashi daga filin jirgin saman Abuja, babban birnin Najeriya.