Sabuwar ƙa'idar aikin hajjin 2026 da Saudiyya ta fitar

Xajka

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Hukumomin Saudiyya sun gabatar da wata sabuwar ƙa'idar aikin hajjin 2026 ga maniyyatan bana.

Tuni dai maniyyata daga ƙasashe daban-daban ciki har da Najeriya suka fara tashi zuwa Saudiyya domin sauke faralin.

Aikin hajji na ɗaya daga cikin shika-shikan Addinin Musulunci, da aka wajabta wa wanda yake da damar yi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

A kowace shekara miliyoyin Musulmai ne daga ƙasashen duniya daban-daban ke sauke farali.

Ƙasar Saudiyya, wadda ake gudanar da aikin ibadar a cikinta kan fitar da ƙa'idojin aikin lokaci zuwa lokaci domin dacewa da dokokinta da kuma inganta aikin hajjin.

Wace sabuwar ƙa'ida aka fitar a bana?

Wasu maniyyatan Najeriya

Asalin hoton, Ahmed Mu'azu, NAHCON

Ma'aikatar kula da aikin Hajji da Umra ta Saudiyya ta saka ƙa'idar shekaru ga maniyyatan da za su je sauke farali a wannan shekara.

A yanzu Saudiyya ta haramta wa yara ƴan ƙasa da shekara 15 zuwa aikin hajjin, wanda ta gabatar a 2025, aka kuma fara aiki da dokar a bana.

Ma'aikatar ta ce ta saka sabuwar dokar ne domin tabbatar da kariya da kuma iya tafiyar da lamurran maniyyatan ba tare da tangarɗa ba, a lokacin aikin hajjin da miliyoyin mutane ke halarta a kowace shekara.

"Ana ɗaukar yara ƴan ƙasa da shekara 15 a matsayin masu rauni, waɗanda ba za su iya dogara da kansu ba, ko jure wa ƙalubalen da ke tattare da aikin hajjin,'' kamar yadda ma'aikatar ta yi ƙarin haske.

Ma'aikatar aikin hajjin ta ce akwai tarin ƙalubalen da ƙananan yara ke fuskanta a lokacin aikin hajjin da suka haɗa da gajiya da rashin ruwa a jikinsu da matse su cikin dandazon mutane, lamarin da ke jefa rayukansu cikin hatsari.

Akwai shekarun da suka tsufar wa aikin?

Tuni dai hukumomin Saudiyyar suka soke bizar da aka bai wa maniyyatan da ba su kai shekara 15 ba, inda aka buƙaci kamfanonin jirage su guje wa jigilar yaran.

Ma'iakatar ta ce za a mayar wa waɗanda lamarin ya shafa da kuɗaɗensu.

Duk da cewa a yanzu mafi ƙanƙantar shekarun da ma'aikatar ta amincewa maniyyata shi ne 15, babu iyakancewa a yawan shekarun da aka taƙaita ga maniyyatan ba, matuƙar za su iya.

Sai dai ma'aikatar ta ce maniyyatan da ba su kai shekara 18 ba, dole ne su riƙa tafiya da masu kula da su.

Masu ibada

Asalin hoton, Mansoreh Motamedi/Getty Images

Ko dokar ta shafi Umra?

Ma'aikatar ta ce sabuwar dokar ba ta shafi masu ibadar Umrah ba, inda yara ke da damar zuwa domin yin ibadarsu.

Sai dai ma'aikatar ta ce a Umarar ma akwai wasu keɓabtattun lokutan cunkoso da dokar hana ƙananan yaran za ta yi aiki.

Ma'aikatar Haji da Umrar ta ce an ɓullo da sauye-sauyen ne domin inganta tsarin kariya ga maniyyata aikin hajji, ɗaya daga cikin taron mutane mafi yawa a faɗin duniya.

Najeriya ta ja kunnen maniyyatanta

Mataimakin shugaban Najeriya

Asalin hoton, Ahmed Mu'azu, NAHCON

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta ja hankalin maniyyatan ƙasar kan abubuwan da ya kamata su kiyaye, domin kauce wa matsala a ƙasar ta Saudiyya.

NAHCON ta kuma jaddada wa maniyyatan muhimamcin ƙarɓar katin shaidar aikin Hajji, wanda ta ce yana ɗaya daga cikin abubuwa da suka riƙa janyo matsaloli a baya.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai hukumar ta fara jigilar maniyyatan ƙasar zuwa ƙasa mai tsarki.

An fara jigilar maniyatan ne da alhazan jihar Kogi da Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar ƙasar, da na jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar.

"Jirgin farko ya tashi ne daga Abuja babban birnin Najeriya, ɗauke da alhazan jihohin Kogi da na Nasarawa'', kamar yadda Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktar yaɗa labaran hukumar NAHCON ta shaida wa BBC.

Ƴan Najeriya nawa ne za su sauke farali a 2026?

Alhazan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar NAHCON ta ce maniyyatan ƙasar kimanin 50,000 ne za su sake farali a wannan shekara.

A shekarun baya dai adadin kan zarta haka, inda ake samun maniyyatan kusan 100,000 da ke sauke farali a shekara.

To amma sakamakon matsalolin tattalin arziki da hauhawar farashi da tsadar man jirgi ya sa adadin ya yi matuƙar raguwa.

A baya dai ana yawan samun jinkiri a aikin jigilar alhazan Najeriyar a duk shekara, wanda hakan ke sa wasu alhazan gaza samun damar sauke faralin, sai dai Fatima, ta ce tuni suka ɗauki mataki kan lamarin.