Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ba na jin kunyar cewa ina ɗauke da ƙuraje a al'aurata'
- Marubuci, Lena-Zaharah Mohammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Wales
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A lokacin da take farkon shekaru 20, ba kasafai Melys Edwards ke fita daga gida ba tare da tubarau ba, ba wai saboda zarfin rana ba, sai don kunyar da take ji.
"Bana so mutane su ganni, saboda kunya," a cewar matashiyar wadda yanzu take shekara 29, yayin da take bayyana yadda ta ji lokacin da aka gano tana ɗauke da ƙuraje a al'aurarta da ake ɗauka ta hanyar jima'i.
Ma'aikatan lafiya sun ce wasu mutanen damuwar da suke shiga bayan gano suna ɗauke da cuta takan zarce wahalar da cutar ke yi musu.
A duniya baki ɗaya, ƙiyasin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da aka fitar a shekarar 2024 ya nuna cewa kusan mutum miliyan 846 masu shekaru tsakanin 15 da 49 na ɗauke da cutar ƙurajen ala'aura da ake ɗauka da hanyar jima'ia.
Hakan na nufin fiye da mutum ɗaya cikin kowane mutum biyar na wannan rukuni na shekaru na rayuwa da wannan lalura.
Wata cuta ce da za a iya rage tasirinta da magani da kula da ita, amma ba ta da maganin da ke kawar da ita gaba ɗaya.
A mafi yawan lokuta, masu ɗauke da cutar ba sa nuna alamomi ko kuma alamomin ba su da yawa.
Sai dai ga wasu mutane, cutar kan haifar da raunuka masu zafi da kumburi, waɗanda kan iya dawowa lokaci zuwa lokaci a tsawon rayuwa.
Melys, wadda take daga yankin Wales a Birtaniya, tana jin zafin da ma ba ta iya jure shi. ''A lokacin da na fara jinsa yana matuƙar yi min zafi,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.
Matashiyar mai wallafa bidiyoyi a shafukan sada zumunta, ta yi imanin cew ata kamu da cutar ne bayan jima'i da wani mutum da ta ce ya san yana ɗauke da cutar, amma yaƙi faɗa mata.
Gano cewa tana ɗauke da cutar ya jefa ta cikin baƙin ciki da fushi da kuma ƙin yarda da abin da likitan.
Ta ce ta riƙa jin kamar ba ita ba ce, kuma ta kasa yarda da kanta. "Dukkan rayuwata ta sauya a wannan lokacin," in ji ta.
Mene ne ƙurajen al'aura?
Cutar ƙurajen al'aura na samuwa ne sakamakon wata ƙwayar cuta da ake kira herpes simplex. Idan ka kamu da ƙwayar cutar ba za ta warke daga jikinka ba.
Takan haifar da kumburi da ƙuraje a al'aura amma ba ta yaɗuwa zuwa wasu sassan jiki. Takan tsaya a iya al'aurar yayin da za ta ci gaba da haifar da raunuka a wannan wuri.
Akwai nau'ika biyu na wannan ƙwayar cuta, kuma dukkansu na iya haifar da rashin lafiya iri ɗaya.
A cewar ƙididdiga, a shekarar 2020 kusan mutum miliyan 520 a duniya suna rayuwa da ɗaya daga cikin waɗannan nau'ikan cutar, wadda galibi ake yaɗa ta ta hanyar jima'i tsakanin mutane.
Ana kallon nau''in cutar na HSV-2 a matsayin mafi tayar da hankali ga fannin lafiya, saboda tana iya haifar da annoba, kuma kashi 90 cikin 100 na alamomin cutar da aka gani nata ne.
Mata sun fi maza kamuwa da wannan cuta fiye da sau biyu saboda yanayin danshin al'aurarsu na bai wa ƙwayar cutar damar shiga tare da rayuwa cikin sauƙi.
Nau'in HSV-1 ta fi yaɗuwa ga ƙananan yara ta hanyar yawu da taɓa fatar juna da baki, inda za ta haifar da ƙurajen baki.
Marian Nicholson, daraktar wata gidauniya a Birtaniya da ke yaƙi da cutar, ta ce mutane da dama ba su san cewa wannan ƙwayar cuta tana haifar da sanyi da ƙurajen al'aura ba.
''Jima'i da baki na ɗaya daga cikin hanyoyin kamuwa da wannan cuta'', in ji ta.
Ta ƙara da cewa ''idan wani na da ciwon sanyin al'aura, kuma ya yi jima'i da baki, to zai yaɗa cutar''.
Alamomin cutar
Alamomin cutar sun haɗa da:
- Kumburin al'aura
- Ƙuraje
- Alamar ƙonewar fata
- Ƙaiƙayin al'aura
- Jin zafi yayin fitsari.
Tana da magani?
Melys ta ce a lokacin da take neman magani a shafukan intanet, ta samu wasu bayanai da suka razanata.
"A lokacin da nake dubawa sai na ga wani abu kamar, ''rayuwarki ba za ta koma yadda take a baya ba, wa ya sani ko ba za ki iya haihuwa ba?'' duka waɗannan bayanai sun razana ni.
Amma Nicholson, wanda take ɗauke da cutar na tsawon fiye da shekara 30, ta ce cuta ce da za a iya rayuwa da ita ba tgare da matsala ba, idan aka ɗauki matakai.
"Akwai dai bayanai masu razani da za ka riƙa samu," in ji ta. "Mutane sun ɗauka laifin mutum ne yake janyo ta, amma ba haka batun yake ba."
Wasu mutanen ba sa nuna alamun suna ɗauke da cutar, amma ga waɗanda alamomin suka bayyanar musu, za su iya rayuwa da su idan suka ɗauki mataki.
Fitar alamomin farko na cutar ya fi ciwo da tsanani, sai dai bayan lokaci mai tsawo zafin kan ragu.
Amfani da riobar kariya yayin jima'a lkan rage hatsarin kamuwa da cutar ƙurajen al'aurar, a cewar WHO.
Hukumar Lafiyar ta Duniya ta gargaɗi mutane su guji yawaita jima'i ba tare da robar kariyar ba.
WHO ta kuma bayar da shawara ga mutane da ke da alamomin wannan cuta su yi gwajin cutar HIV.
Hukumar lafiyar Birtaniya ta ce rashin lafiya da gajiya da sauyawar kwanakin al'ada na ƙara ruruta cutar.
Tsawon lokaci, Melys ta ce ta fara fahimtar cewa gano mata cutar ya wayar mata da kai, inda a yanzu ta zama mai wayar da kai game da cutar a shafukan sada zumunta.
"Lokacin da aka fara gano ina ɗauke da cutar, kusan babu wani bayani muhimmi a intanet, sai wasu sakamakon bincike masu firgitarwa a shafin Google da kuma rubuce-rubucen mutane a Reddit," in ji ta.
"Saboda haka idan zan iya zama irin mutumin da nake buƙatar samu a wancan lokacin, to akwai wani alheri da ya fito daga wannan abin da na fuskanta," kamar yadda ta yi ƙarin haske.