Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kama man fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ƙara tsaurara matakanta na yaƙi da satar ɗanyen mai da safarar mai ba bisa ka’ida ba, inda ta tarwatsa wata sabuwar matatar mai ta haramtacciyar hanya tare da kama wani jirgin ruwa mai dauke da kusan lita 17,000 na man fetur da ake zargin an tace ba bisa ka’ida ba a yankin Neja Delta.
Jaridar The Guardian ta ruwaito a ranar 8 ga watan Agusta cewa rundunar ta ce a wani samame daban a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya, ta kuma kama kusan lita 24,000 na wani abu da ake zargin ɗanyen mai ne da aka sata, tare da tarwatsa wasu wurare da ake zargin an kafa domin satar ɗanyen mai.
Kakakin rundunar, Kyaftin Abiodun Folorunsho, ya ce kamen ya nuna ƙudurin rundunar na dakile hanyoyin safarar man fetur ba bisa ka’ida ba, hana masu yin zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa samun damar gudanar da ayyukansu, da kuma kare muhimman ababen more rayuwa na man fetur da iskar gas daga amfani da su wajen aikata laifuka.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da samame bisa bayanan sirri domin tarwatsa wuraren tace mai ba bisa ka’ida ba, yaƙi da satar ɗanyen mai da kuma safarar mai ba bisa ƙa’ida ba, kare muhallin teku da kuma kare muradun tattalin arzikin Najeriya.
Rundunar ta ce ayyukan nata sun fi mayar da hankali ne kan muhimman wuraren da ake aikata laifuka a yankin Neja Delta, ciki har da jihohin Rivers da Delta.
Najeriya na asarar miliyoyin gangar ɗanyen mai a kowace shekara sakamakon yawaitar satar mai, huda bututun mai ba bisa ka’ida ba da kuma lalata ababen more rayuwa a yankin Neja Delta.