Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aston Villa da Roma na son Endrick, Arsenal na tuntuɓar Barcola
Aston Villa da Roma sun nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Brazil, Endrick, mai shekara 22, a matsayin aro daga Real Madrid. (AS - in Spanish)
Ana sa ran kyaftin ɗin Ingila kuma ɗan wasan gaba na Bayern Munich, Harry Kane, mai shekara 33, zai tsawaita kwantiraginsa da kulob ɗin har zuwa shekarar 2029.(Times - subscription required)
Arsenal ta fara tuntuɓar wakilan ɗan wasan gaba na Faransa, Bradley Barcola, mai shekara 23, domin ƙoƙarin kwace shi daga hannun Liverpool, wadda ita ma ke zawarcinsa daga Paris Saint-Germain. (Give Me Sport)
Ɗan wasan gaba na Ingila, Marcus Rashford, mai shekara 28, na da niyyar farfaɗo da rayuwarsa ta ƙwallo a Manchester United bayan dawowarsa daga zaman aron da ya yi a Barcelona. (Sun)
Liverpool na iya amincewa da tafiyar ɗan wasan gaba na Netherlands, Cody Gakpo, mai shekara 27, zuwa Tottenham Hotspur idan ta samu wasu 'yan wasan gaba da take nema. (Football Insider)
Arsenal da Tottenham sun nuna sha'awar Ferran Torres kafin ɗan wasan gaba na Spain mai shekara 26 ya amince da sharudan kansa na komawa Paris Saint-Germain. (TeamTalk)
Crystal Palace ta fara tattaunawa kan sayen ɗan wasan tsakiyar Senegal, Lamine Camara, mai shekara 22, daga Monaco. (Nicolo Schira)
Manchester United da Arsenal na cikin kungiyoyin da ke neman ɗan bayan hagu na Belgium, Joaquin Seys, mai shekara 21, daga Club Brugge. (Sun)
An sanar da ɗan bayan dama na Sifaniya, Hector Fort, mai shekara 20, cewa zai iya barin Barcelona a wannan bazarar, yayin da Everton da Fulham ke cikin masu sha'awarsa. (TeamTalk)
Fulham ta cimma yarjejeniya da Southampton domin sayen ɗan wasan tsakiyar Arewacin Ireland, Shea Charles, mai shekara 22, kan kuɗin da zai iya kaiwa fam miliyan 30. (Athletic - subscription required)
Ɗan wasan gaba na Scotland, Robbie Ure, mai shekara 22, na dab da komawa Sevilla daga kungiyar Sweden ta IK Sirius kan yuro miliyan 9. (ESPN)
Sheffield United ta ƙara tayinta zuwa fam miliyan 8 domin sayen ɗan bayan Australia, Harry Souttar, mai shekara 27, daga Leicester City. (Football Insider)