Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin Afirka 5 da suka sauya kundin tsarin mulki don ci gaba da mulki
Dimokuraɗiyya a ƙasashe da dama na Afirka na ci gaba da fuskantar ƙalubale daga shugabannin da ke amfani da sauye-sauyen kundin tsarin mulki wajen cire takunkuman da ke hana su ci gaba da riƙe mukami ko kuma kasancewa a kan karagar mulki.
Wasu sun soke wa'adin shugabancin ƙasa gaba ɗaya, wasu kuma sun sauya adadin wa'adin da shugaban ƙasa zai iya yi.
Haka kuma, akwai waɗanda suka ƙirƙiri sabon kundin tsarin mulki sannan suka yi amfani da fassararsa wajen sake ƙirga wa'adin mulkinsu daga farko.
A baya-bayan nan, wannan muhawara ta sake ɗaukar hankali bayan da Shugaban ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo), Felix Tshisekedi, ya sanya hannu kan wata doka da ta tanadi gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki a ranar 9 ga Nuwamban 2026.
Gwamnatinsa ta ce matakin na da nufin yin gyaran tsarin hukumomi, amma 'yan adawa na fargabar cewa hakan na iya zama wata hanya da za ta ba shi damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa karo na uku, abin da kundin tsarin mulkin ƙasar na yanzu bai amince da shi ba.
Tarihin Afirka ya nuna misalai da dama na shugabannin da suka yi nasarar kauce wa irin waɗannan ƙuntatawa, inda suka ci gaba da mulki bayan cikar wa'adin da aka fara tanada musu.
A wasu ƙasashe, kundin tsarin mulki ya ƙayyade wa shugaban ƙasa wa'adi biyu kacal, amma daga bisani aka yi gyare-gyare don cire wannan ƙa'ida kafin karewar wa'adinsu ko kuma a ba su damar sake fara kirga wa'adin nasu daga farko.
Sai dai ba duk ƙoƙarin da aka yi ba ne ya yi nasara. Wasu shugabanni sun fuskanci turjiya daga jama'a ko majalisa ko jam'iyyunsu ko ma kotuna, lamarin da ya hana su cimma canje-canjen da suke buƙata.
Ga wasu misalan shugabannin da suka yi nasarar sauya kundin tsarin mulkin ƙasashensu tare da ci gaba da mulki a Afirka.
Yoweri Museveni – Uganda
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya kasance kan karagar mulki tun 1986.
Kundin tsarin mulkin ƙasar da aka amince da shi a shekarar 1995 ya ƙayyade wa shugaban ƙasa wa'adi biyu ne kawai, kowanne na shekara biyar.
Bisa ga wannan tanadi, bayan nasararsa a zaɓukan shekarun 1996 da 2001, wa'adinsa na biyu zai ƙare ne a shekarar 2006, kuma ba zai kasance cikin waɗanda za su iya sake tsayawa takara ba.
Sai dai a 2005, yayin da yake wa'adinsa na biyu, majalisar dokokin ƙasar ta amince da wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin da suka soke iyakar wa'adin shugaban ƙasa gaba ɗaya.
Wannan sauyi ya ba Museveni damar sake yin takara a zaɓen shekarar 2006, wanda ya lashe, sannan ya ci gaba da shiga zaɓuka na gaba, inda ya riƙa samun nasara duk da korafe-korafen da 'yan adawa ke yi game da yadda ake gudanar da zaɓukan.
A 2017, gwamnatinsa ta sake yin wani gyara da ya cire iyakar shekaru 75 da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu neman kujerar shugaban ƙasa.
Wannan gyaran ya bai wa Museveni damar ci gaba da tsayawa takara duk da cewa ya haura shekarun da aka ƙayyade a baya.
Paul Biya – Cameroon
Shugaba Paul Biya ya fara mulkin Kamaru a 1982. Kundin tsarin mulkin ƙasar na 1996 ya ƙayyade wa shugaban ƙasa wa'adi biyu ne kacal, kowanne na tsawon shekara bakwai.
Tun da Biya ya lashe zaɓukan shekarun 1997 da 2004, an ƙiyasta wa'adinsa na biyu zai ƙare a 2011, wanda hakan zai kawo ƙarshen shugabancinsa bisa tanadin kundin tsarin mulkin a wancan lokaci.
Sai dai a watan Disamban 2007, Biya ya bayyana aniyarsa ta soke iyakar wa'adin shugabancin ƙasa.
Daga bisani, a 2008, majalisar dokokin ƙasar ta amince da wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulki wanda ya cire tanadin da ke hana shugaban ƙasa yin fiye da wa'adi biyu.
Wannan sauyi ya kawar da babban shingen da ake sa ran zai kawo ƙarshen mulkinsa a shekarar 2011.
Bayan waɗannan gyare-gyare, Biya ya ci gaba da tsayawa takara tare da lashe zaɓukan shekarun 2011, 2018 da 2025.
Hakan ya sa, maimakon sauka daga mulki a shekarar 2011 kamar yadda kundin tsarin mulkin da ya gabata ya tanada, ya ci gaba da jagorantar ƙasar a wasu ƙarin wa'adin mulki har zuwa yau.
Paul Kagame – Rwanda
Kundin tsarin mulkin Rwanda na 2003 ya ƙayyade wa shugaban ƙasa wa'adi biyu ne kacal, kowanne na tsawon shekara bakwai, kamar dai Kamaru.
An zaɓi Paul Kagame a matsayin shugaban ƙasa a 2003, sannan aka sake zaɓensa a 2010.
Bisa ga tanadin kundin tsarin mulkin a lokacin, wa'adinsa na biyu shi ne na ƙarshe, kuma an yi tsammanin zai sauka daga mulki a shekarar 2017.
Sai dai a shekarar 2015, Rwanda ta gudanar da ƙuri'ar raba gardama inda aka amince da wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin ƙasar da suka sauya tsarin wa'adin shugabancin ƙasa.
Sabbin tanade-tanaden sun bai wa Kagame damar sake tsayawa takara domin yin wani ƙarin wa'adi na shekara bakwai wanda ya fara a shekarar 2017, sannan kuma ya ba shi damar yin wasu ƙarin wa'adi biyu na shekara biyar-biyar.
Ta haka ne, maimakon sauka daga mulki a shekarar 2017, Kagame ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki bayan da ya lashe zaɓen shekarar da kusan kashi 98.8 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.
A shekarar 2024, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda ya shiga wani sabon wa'adi na shekara biyar.
Alassane Ouattara – Ivory Coast
Shugaban ƙasar Côte d'Ivoire (Ivory Coast), Alassane Ouattara, ya yi amfani da sabon kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a 2016 domin ci gaba da tsayawa takarar shugaban ƙasa duk da cewa ya riga ya yi wa'adi biyu.
Kundin tsarin mulkin ƙasar na 2000 ya ƙayyade wa shugaban ƙasa wa'adi biyu ne kacal, kowanne na tsawon shekara biyar.
An zaɓi Ouattara a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2010, sannan aka sake zaɓensa a 2015.
Bisa ga tanadin tsohon kundin tsarin mulkin, wa'adinsa na biyu zai ƙare ne a shekarar 2020, kuma ba zai kasance cikin waɗanda suka cancanci sake tsayawa takara ba.
Sai dai a shekarar 2016, gwamnatinsa ta amince da sabon kundin tsarin mulki, wanda ya haifar da muhawara kan yadda za a ƙirga wa'adin shugaban ƙasa.
Gwamnatin ta yi hujjar cewa wa'adin da aka yi a ƙarƙashin tsohon kundin tsarin mulkin bai kamata a haɗa shi da iyakar wa'adin da sabon kundin tsarin mulkin ya tanada ba.
Wannan fassarar ta ba Ouattara damar sake tsayawa takara a zaɓen 2020, wanda ya lashe duk da zanga-zanga da suka daga daga 'yan adawa masu adawa da matakinsa na neman wani ƙarin wa'adi.
A shekarar 2025, ya sake neman takarar shugaban ƙasa kuma ya yi nasara a zaɓen.
Ismail Omar Guelleh – Djibouti
Shugaba Ismail Omar Guelleh na ƙasar Jibuti (Djibouti) yana kan mulkin ƙasar tun 1999.
Kundin tsarin mulkin ƙasar na 1992 ya ƙayyade wa shugaban ƙasa wa'adi biyu ne kacal, kowanne na tsawon shekara shida.
Bayan an zaɓe shi a shekarun 1999 da 2005, ana sa ran wa'adinsa na biyu zai ƙare a shekarar 2011, kuma ba zai cancanci sake tsayawa takara ba.
Sai dai a 2010, yayin da yake dab da kammala wa'adinsa na biyu, majalisar dokokin ƙasar ta amince da wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin da suka soke iyakar wa'adin shugaban ƙasa.
Wannan sauyi ya buɗe masa hanya ta sake tsayawa takara a zaɓen shekarar 2011, wanda ya lashe.
Bayan haka, Guelleh ya ci gaba da lashe zaɓukan shekarun 2016 da 2021.