Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Kwankwaso ya sa na yi rantsuwar komawa APC – Abba Kabir
Kusan kimanin shekara ɗaya bayan komawarsa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya tare da fita daga jam'iyyar NNPP da kuma raba gari da ubangidan siyasarsa Rabi'u Musa Kwankwaso, a karon farko gwamnan Kano Abba Kabir ya yi bayani kan dalilansa na ɗaukar matakin da ya ɗauka.
A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2026, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.
Komawar Abba Kabir APC ba tare da Rabiu Kwankwaso na daga cikin sauya sheƙa da aka fi magana a kansu tun bayan komawar Najeriya tafarkin mulkin siyasa a 1999.
Wasu sun bayyana matakin na Gwamna Yusuf a matsayin ''butulci'', wasu sun ce "cin amana", yayin da masu ra'ayinsa ke ganin babu ko ɗaya daga cikin waɗannan, kamar yadda shi ma ya faɗa wa BBC.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, karon farko tun bayan sauya sheƙa. Abba Kabir Yusuf, ya yi bayanin yadda ya ce ubangidan siyasarsa Rabiu Kwankwaso ya jagoranci yin wata yarjejeniya da shugaban ƙasar Bola Tinubu, domin komawa jam'iyyar APC idan har shugaban ƙasar bai yi katsalanda ba a shari'ar da aka yi kan wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano tsakaninsa da ɗan takarar jam'iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna.
Abba ya ce bayan zaɓen 2023 ne suka zauna da shugaban Najeriya, Bola Tinubu, suka yi yarjejeniya cewa idan har bai tsoma baki a shari'ar da ake yi kan neman soke nasarar da ya samu a Kano ba, to za su koma jam'iyyar APC.
Ya ce daga baya Kwankwaso ya yi watsi da yarjejeniyar da suka yi, duk da cewa ya sa shi ya rantse.
"Shi da kansa [Kwankwaso] ya tura ni wajen Tinubu, ya roƙe ni cewa in je in samu Tinubu, in gaya masa mun yi masa wannan alƙawari, kuma ma idan ta kama in ɗauki Alƙur'ani in yi rantsuwa a wannan lokaci cewa idan Allah ya sa mun samu nasara, yana so mu ɗinke gaba ɗaya," kamar yadda Abba ya shaida wa BBC.
Abba ya ce kuma ya yi hakan, inda ya je wajen Tinubu ya yi masa wannan alƙawari.
Ya kuma ce sau da dama Sanata Kwankwaso ya gana da Shugaba Tinubu, kuma ya sha tura tawaga domin tattauna shirye-shiryen komawa APC.
Abba ya ce duk da cewa Allah ne ya ba shi mulki, a lokacin suna neman fahimtar juna da shugaban ƙasa ne, inda suka roƙe shi kada ya sa baki a shari'ar.
"Kuma an masa alƙawari cewa in Allah ya yarda, idan dai an yi nasara, saboda fahimtar juna da abokantakar da ke tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, an yarda cewa shi Sanata [Kwankwaso] da ni gwamna, a lokacin dukkan magoya baya, in Allah ya yarda, za su koma APC domin a samu haɗin kai," in ji Gwamna Abba.
A kan haka ne Gwamna Abba ya ce ba ya ji ko kaɗan cewa ya yi wa Kwankwaso butulci, a maimakon haka, ya cika alƙawarin da Sanata Kwankwaso ne ya kasa cikawa.
Waɗannan kalamai na gwamna Yusuf sun dai sha bamban da abin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya shaida wa BBC a wata tattaunawa jim kaɗan bayan komawar gwamnan na jihar Kano jam'iyyar APC.
A wancan lokacin Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam'iyyar NNPP ta zo da ba-zata ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.
''Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwan da suke faruwa haka su ke,'' in ji Kwankwaso.
A tsohuwar tattaunawar Sanata Kwankwaso ya ce ''Ni kaina idan na kwanta sai in waiwaya in ce me ya faru? waye ya yi laifi? Ni ne na yi laifi? jam'iyya ce ta yi laifi? ƴan jam'iyya ne suka yi laifi? amma na kasa samun amsa.''
Sai dai gabanin ficewar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi zuwa jam'iyyar APC, an ga Sanata Kwankwaso a lokuta da dama yana safa da marwa a fadar shugaban ƙasa, sai dai babu tartibin bayanin da ya bayar a wancan lokacin kan abubuwan da yake tattaunawa da shugaban ƙasar.
Amma duk da haka wasu bayanai dama sun nuna cewa akwai tattaunawar da ake yi ta komawar Kwankwason da gwamna Abba zuwa jam'iyyar APC.
Sai dai a wancan lokacin gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar ne bisa la'akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama'ar Kano baki ɗaya.
Ya kuma ce sai da ya yi tuntuɓa a tsakanin abokan tafiyarsa a siyasance da sauran masu ruwa da tsaki kafin yanke hukuncin sauya sheƙar.
'Da masaniyar jagora aka yi duk abin da aka yi'
Abba ya kuma musanta zargin cewa wani wasan kwaikwayo ne suka shirya da tsohon ubangidansa domin kashe 'yan adawa ko kawar da hankalin al'umma.
Ya ce "babu wannan magana," kuma har an yi zama da 'yan majalisa da shugabannin ƙananan hukumomi tare da Kwankwaso domin komawa APC.
"Da masaniyar jagora aka yi duk abin da aka yi," in ji Abba.
Saboda haka, Abba ya ce duk wasu tsare-tsare da aka yi, an yi su ne da sanin Kwankwaso, kuma yarjejeniya ce suka cimma, "shi kuma Kwankwaso bai cika ba".
Sai dai Gwamna Abba ya ce abin da ya kawo cikas ga yarjejeniyar shi ne kalaman da Kwankwaso ya yi masu zafi kwanaki kaɗan bayan shi Abban ya riga ya tabbatar wa Tinubu komawarsu APC, waɗanda har aka aika wa shugaban ƙasa, kuma lamarin bai yi daɗi ba.
Wane ne mai laifi?
Gwamnan Abba Kabir, ya kuma yi wa BBC bayanin alaƙarsa da tsohon maigidansa, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a yanzu ba sa inuwa guda.
Gwamna Abba ya ce bai yi wa Kwankwaso butulci ba, kuma ko bayan rabuwarsu sun yi magana, har ma a baya-bayan nan "nakan aika masa da saƙonnin gaisuwa".
Abba ya ce: "Dama ita siyasa abu ce da babu tabbataccen zama a cikinta." Sai dai ya ƙara da cewa rigingimun da suka rincaɓe a jam'iyyar NNPP da suke mulki a cikinta na daga cikin abubuwan da suka haifar da saɓani tsakaninsu.
Gwamna Abba bai amsa tambayar da BBC ta yi masa kan ko da gaske ne Kwankwaso ya sha matsa masa lamba, bai kuma bar shi ya yi aikinsa yadda ya kamata ba, ko kuma akwai wani laifi da Kwankwaso ya yi masa.
Ya ce ba abu ne da zai tattauna a kafafen yaɗa labarai ba, kawai "a bar maganganun yadda suke".
Abin da ya haifar da saɓani tsakanina da matata
A tattaunawarsa da BBC Hausa, Abba Kabir Yusuf ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka samu tangarɗa a zamantakewarsa da matarsa Zainab Musa Kwankwaso, wadda ƴa ce ga yayan tsohon gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya a jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso.
A ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba Gwamna Abba ya yi wasu kalamai a lokacin wani taron ƴan fansho a babban ɗakin taro na gwamnatin jihar da ke birnin Kano.
Hakan ya biyo bayan raɗe-raɗin da aka riƙa yi cewa gwamnan ya samu saɓani da matarsa, bayan rahoton jaridar Daily Nigerian wanda ya Zainab Kwankwaso ta shigar da ƙara a wata kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, tana buƙatar a raba aurenta da mijin nata.
Lamarin ya haifar da muhawara ganin irin alaƙar da ke tsakanin gwamnan da mariƙin Zainab, Rabiu Kwankwaso, wanda ya kasance ubangidan siyasa ga Gwamna Abba.
Me ya haifar da rikicin?
Sanye cikin farar babbar riga da jar hula mai tambarin shugaban Najeriya Bola Tinubu, Abba ya ɗan ja lumfashi sannan ya ci gaba da bayani, bayan da wakilin BBC ya tambaye shi: "mene ne bayani kan kalaman da ka furta da ake zargin magana ce game da iyalinka?"
"Irin wannan harka ta iyali abu ne mai matuƙar wahala," in ji Gwamna Yusuf.
Ya ci gaba da cewa: "Ita dai wannan mata, Zainab ƴar wansa ce (Kwankwaso), kuma ya yi masu aure amma ita auren nata bai daɗe ba, daga nan Allah Ya haɗa mu muka yi aure kimanin shekara 20 da suka wuce, kuma muna da yara.
"Abubuwa da yawa sun faru, har ta kai ga aka kwashe kaya sannan aka zo aka ɗauke ta daga gidana, kuma duk na yi hakuri ban yi magana," kamar yadda Abba Kabir ya shaida wa BBC.
Daga nan gwamnan ya ƙara da cewa har ya shaida wa yaransu cewa Zainab ɗin za ta dawo gidansa.
"Kwatsam sai ga shi ya sa ta ɗirka ni a kotu, kotun ma a Abuja, ba a Kano ba," a cewar gwamnan.
Ya ƙara da cewa "abu ne babu daɗi".
Ya ce duk da cewa ba zai faɗa wa duniya yadda aka bi wajen ɗauke matar tasa daga gidansa ba, amma yana da shaidu da bayanai dalla-dalla kan yadda lamarin ya faru.
A cewarsa wannan bai kamata ya zama abin cece-ku-ce kasancewa abu ne da aka saba ganin irin hakan.
Lokacin da aka tambaye shi me ya sa ya yi wannan magana a bainar jama'a?
Sai gwamna Yusuf ya ce: "Ai ba ni ne na siyasantar da abin ba, kai yanzu idan aka yi maka haka za ka ji daɗi?"
"A kwashe wa iyalinka kaya ba da sanin ka ba, a zo a ɗauke ta a garkuwa da ita ba da sanin ka ba, a tafi da ita gidan wani, ba da sanin ka ba, sannan kawai sai ka ji cewa ita ce ta kai ka ƙara kotu."
Gwamnan ya ce ana ci gaba da duba lamarin, kuma akwai yiwuwar cewa za a samu maslaha.
'Abin da ya fi ba ni wahala a mulkin Kano'
Gwamna Abba ya ce mulkin Kano abu ne mai wahala "ƙwarai da gaske", kuma dole ne mutum ya kasance mai haƙuri da jajircewa.
Ya ce babban abin da ya fi ba shi ciwon kai, kuma ya zama babban ƙalubale a gare shi, shi ne matsalar tsaro, musamman ayyukan 'yan daba, fashin waya da kuma shiga gidajen mutane ana aikata laifuka.
Sai dai kasancewarsa ɗan jam'iyyar adawa ma ya zame masa ƙalubale, saboda yadda ya sha fuskantar rashin haɗin kai daga jami'an tsaro.
"Na sha wahala ƙwarai da gaske, domin ban iya samun haɗin gwiwar jami'an tsaro ba."
Amma ya ce komawarsa jam'iyya mai mulki ta APC ya sa yanzu komai ke tafiya daidai, tun bayan da suka bai wa gwamnatin tarayya haɗin kai.
A cewar Abba, batun shari'ar da aka yi a Kotun Ƙoli na ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba shi ciwon kai a shekararsa ta farko a kan mulki, duk da cewa ya ce ya gudanar da wasu ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
BBC Hausa ta wallafa cikakkiyar wannan hira a shafin BBC Hausa YouTube.