Shin ya halasta a hana ƴan adawa amfani da wuraren gwamnati don yin kamfe?

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ƴan siyasa na ci gaba da nuna damuwa kan yadda suke fuskantar matsaloli wajen samun wuraren gudanar da yaƙin neman zaɓe a wasu jihohin Najeriya.

Yawanci, jam'iyyun adawa ne ke ƙorafin fuskantar irin wannan matsala. Sun yi iƙirarin sukan gabatar da buƙatar amfani da wani filin gwamnati domin gudanar da kamfe, amma daga bisani a sanar da su cewa "ba a amince da buƙatarsu ba".

A wasu lokutan, sukan koma yin tattaki a tsakiyar gari domin yaƙin neman zaɓe, yayin da wasu hukumomi ke bayar da hujjar cewa ana gudanar da ayyukan gyara a wuraren da suka nema.

Sai dai, a wasu lokutan, 'yan adawar kan yi ƙorafin cewa ko da sun yi ƙoƙarin yin hayar wuraren taro masu zaman kansu, ana yi wa masu wuraren barazana ko kuma a tura jami'an tsaro su toshe hanyoyin shiga wuraren.

Wannan lamari ya haifar da tambayoyi kan ko matakin hana jam'iyyun siyasa amfani da wuraren gwamnati domin gudanar da yaƙin neman zaɓe ya halasta a ƙarƙashin doka.

Wasu lokutan da aka hana 'yan siyasa amfani da filin yin kamfe

A baya-bayan nan, jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna ta hana ta amfani da filin wasa na Ranchers Bees domin gudanar da yaƙin neman zaɓenta na shugaban ƙasa. Sai dai gwamnatin jihar ta musanta wannan zargi.

A birnin tarayya Abuja ma, an sha samun saɓani tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da jam'iyyun adawa kan amfani da wuraren gudanar da tarukan siyasa.

A jihar Sokoto kuwa, ADC ta yi zargin an hana ta amfani da filin gwamnati domin gudanar da tarukanta, duk da cewa jam'iyyar APC mai mulki na amfani da wurin.

Haka kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya taɓa rubuta wa gwamnati wasiƙar neman izinin amfani da ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa, yana mai cewa kayan al'umma ne, kuma APC ta taɓa gudanar da taro a wurin.

Sai dai a jihar Bauchi, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa ba su damar gudanar da kamfe a jihar.

A gefe guda kuma, Peter Obi da wasu mambobin jam'iyyar NDC sun sha ƙorafin cewa ana hana su wuraren gudanar da kamfe saboda suna jam'iyyar adawa.

A Abuja ma, sun yi irin wannan ƙorafi a lokacin da suke shirin gudanar da taron bayyana shigar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso cikin jam'iyyar.

Haka kuma, jam'iyyar SDP a jihar Nasarawa ta fitar da wata takardar neman izinin amfani da wurin taro da wakilanta da na ƙungiyar Rainbow Coalition suka miƙa wa gwamnatin jihar, inda suka yi zargin cewa an hana su damar amfani da wurin.

Me dokar Najeriya ta ce?

A watan Yunin 2024, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta jaddada cewa bai kamata a hana jam'iyyu da 'yan takara damar amfani da wuraren gwamnati domin gudanar da tarukan kamfe ba. Hukumar ta ce irin wannan mataki na iya zama amfani da ƙarfin mulki wajen fifita wata jam'iyya ko ɗan takara a kan wani.

Barista Aminu Abdulrasheed, masanin dokoki a Najeriya, ya ce dokokin ƙasar sun haramta nuna bambanci wajen bai wa 'yan ƙasa damar amfani da abubuwan more rayuwar al'umma.

"Su masu riƙe da madafun iko, abin da ya kamata su yi la'akari da shi shi ne wuraren da suke mallakin gwamnatin tarayya ko ta jiha ba mallakin jam'iyyar da ke mulki ba ne, ko kuma mutanen da ke riƙe da madafun ikon," in ji shi.

Ya ce kowa na da haƙƙi a kansu, ko da kuwa ɗan jam'iyyar adawa ne ko mai mulki.

Baristan ya lissafo wasu daga cikin tanade-tanaden dokokin ƙasar da suka shafi wannan batu kamar haka:

  • Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanadi 'yancin faɗin albarkacin baki, ciki har da bayyana ra'ayi da yaɗa bayanai da ra'ayoyi ba tare da tsangwama ba.
  • Sashe na 40 ya bai wa kowa 'yancin yin taro da haɗa kai da wasu, musamman kafa jam'iyyar siyasa ko kasancewa mamba a cikinta.
  • Sashe na 42 ya haramta nuna wa ɗan ƙasa bambanci ko hana shi wasu hakkokinsa saboda ra'ayinsa na siyasa.
  • Sashe na 91(1) da (4) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadi cewa jami'an 'yan sanda su samar da isasshen tsaro domin gudanar da tarukan siyasa cikin lumana. Haka kuma, bai kamata a hana jam'iyyar siyasa mai rajista gudanar da taruka ko tattaki domin harkokin siyasarta na tsarin mulki ba. Idan aka samu saɓani kan lokaci ko wurin taro tsakanin jam'iyyu, 'yan sanda za su taimaka wajen warware matsalar ta hanyar shawarwari.
  • Sashe na 95(2) ya haramta amfani da kayan aikin gwamnati, ciki har da kafafen yaɗa labaranta, wajen fifita ko cutar da wata jam'iyya ko ɗan takara a zaɓe.
  • Sashe na 92(3) ya haramta amfani da wuraren ibada, ofisoshin 'yan sanda da ofisoshin gwamnati wajen gudanar da kamfe ko tarukan siyasa.

Wane mataki ya kamata 'yan siyasa su ɗauka?

Barista Aminu Abdulrasheed ya ce idan aka tauye wa ɗan siyasa haƙƙinsa a irin wannan yanayi, matakin da zai iya ɗauka shi ne shigar da ƙara a kotu, ko da yake ba lallai ne a kammala shari'ar ko a ɗauki mataki kafin lokacin zaɓe ya ƙure ba.

Sai dai ya ce akwai wasu matakan gaggawa da 'yan siyasa za su iya neman kotu ta ɗauka domin kare musu haƙƙinsu kafin lokaci ya kure.

"Suna iya garzayawa kotu su nemi umarnin tilastawa, wanda ake kira Order of Mandamus, domin tilasta wa duk wanda doka ta ɗora wa wani nauyin gudanar da aiki ya sauke wannan nauyi," in ji Baristan.

Ya ƙara da cewa 'yan siyasar na iya neman diyyar abin da aka yi musu, ko da bayan abin ya riga ya faru, domin a hukunta waɗanda suka tauye musu haƙƙi.

Me ya sa gwamnati ke hana ƴan adawa damar?

Barista Aminu Abdulrasheed yana ganin cewa gwamnatocin da ke ɗaukar irin wannan mataki kan yi hakan ne saboda fargabar cewa al'umma za su iya nuna goyon baya ga jam'iyyun adawa.

A wasu lokutan kuma, ya ce tsoron rasa goyon bayan masu mulki a matakin tarayya ne ke sa gwamnatocin jihohi hana 'yan adawa amfani da wuraren kamfe, domin kada a ga kamar sun ba su damar gudanar da yaƙin neman zaɓe a jiharsu.

Baristan ya nuna damuwa kan yiwuwar yaɗuwar wannan ɗabi'a, yana mai cewa matakin ya saɓa wa tsarin dimokraɗiyya da kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama barazana ga dorewar dimokraɗiyya.