Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa masu gudun hijira daga Najeriya zuwa Nijar ke ƙaruwa?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Yayin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a wasu sassan Najeriya, abin da ke jan hankali shi ne yadda batun cikin gida na ƙara rikiɗewa zuwa matsalar shiyya baki ɗaya. Hare-haren ƴanbindiga da masu garkuwa da mutane sun tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, inda da dama ke tsallaka iyakoki domin neman mafaka a ƙasashe maƙwabta.
Wannan lamari ne da ya ja hankalin Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta yi gargaɗin cewa matsalar na iya ƙara haddasa matsalar jin ƙai a yankin Yammacin Afirka idan ba a ɗauki cikakken matakin daƙile tashe-tashen hankula ba.
Yayin da miliyoyin mutane ke fama da matsalar rabuwa da muhallinsu a Najeriya, ana kuma ganin ƙarin ƴan ƙasar na tsallaka iyakoki zuwa ƙasashe maƙwabta domin neman mafaka.
Wannan ya sa ake fargabar cewa yanayin na iya sa batun tsaro a Najeriya ya fara zama matsala mai tasiri ga yankin Yammacin Afirka baki ɗaya.
A bana kadai, kimanin mutum 64,000 ne suka tsere daga arewacin Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar saboda fargabar hare-hare da rashin tsaro. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen maƙwabta ke ƙoƙarin tinkarar nasu matsalolin tattalin arziki da na jin ƙai.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda adadin masu gudun hijira daga Najeriya ke ƙaruwa cikin sauri, tana mai gargadin cewa ƙasashen da ke karɓar baƙin na fuskantar ƙalubalen samar da isassun matsugunai, abinci da sauran muhimman ayyukan jin kai ga masu neman mafaka.
Yawan Ƴan gudun hijira na ƙaruwa
A cewar Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR), kusan mutum 64,000 ne suka tsere daga arewacin Najeriya zuwa Nijar a shekarar 2026 kaɗai.
Alƙaluma sun nuna cewa a Disambar 2023 akwai ƴan Najeriya 200,556 da ke matsayin ƴan gudun hijira ko masu neman mafaka a Nijar da Benin. Adadin ya ƙaru zuwa 245,883 a ƙarshen 2024, sannan ya kai 258,402 a Disambar 2025.
Sai dai mafi girman ƙaruwa ta faru ne a 2026, inda zuwa watan Satumba adadin ya haura zuwa 327,544.
Wannan na nuna cewa cikin ƙasa da shekaru uku, adadin ƴan Najeriya da ke neman kariya a ƙasashen maƙwabta ya ƙaru da sama da mutum 126,000.
A ɓangaren ƙasar Nijar kuwa, mutum 78 ne suka tsere zuwa ƙasar a 2023, 157 a 2024, 116 a 2025, sai kuma 2026 mutum 2,136.
Masana na ganin wannan alama ce cewa duk da ƙoƙarin da ake yi, mutane da dama har yanzu ba sa jin suna cikin aminci a yankunansu.
Hare-Hare na ƙaruwa duk da ƙarin kasafin tsaro
Najeriya ta ci gaba da ƙara kuɗaɗen da take warewa ga harkokin tsaro tare da ɗaukar ƙarin jami'ai aiki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya. Amma alƙaluman ACLED sun nuna cewa hare-haren da ke da alaƙa da rikice-rikice sun ƙaru sosai a ƴan shekarun nan.
A shekarar 2023 an samu hare-hare 1,319. Adadin ya ƙaru zuwa 1,721 a 2024. A 2025 kuwa, an samu gagarumin tashin gwauron zabi zuwa hare-hare 3,803, wanda shi ne mafi girman adadi a cikin lokacin da aka yi nazarin.
Ko da yake zuwa ranar 5 ga Nuwamba 2026 an samu hare-hare 3,443, adadin ya riga ya zarce na shekarun 2023 da 2024 da tazara mai yawa.
Wannan na nuna cewa matsalar rashin tsaro ta ƙara bazuwa zuwa sabbin wurare, tare da ƙaruwa a yawan hare-haren da ake kai wa al'umma.
Jihohin da suka fi fuskantar asarar rayuka
Borno na ci gaba da kasancewa jihar da ta fi fama da mace-mace sakamakon rikici. Daga mutum 2,767 da suka mutu a 2023, adadin ya kai 4,163 zuwa Nuwamban 2026. Wannan na nuna cewa duk da raguwar hare-haren Boko Haram idan aka kwatanta da wasu shekaru baya, yankin na ci gaba da ɗaukar babban nauyin rikicin.
A Zamfara kuwa, adadin mace-mace ya tashi daga 748 a 2023 zuwa 2,777 a 2025 kafin ya sauka zuwa 1,762 a 2026. Duk da raguwar, har yanzu alkaluman na nuna matsanancin tasirin ayyukan ƴan bindiga a jihar.
Katsina ta nuna ɗaya daga cikin mafi munin sauye-sauye, inda mace-mace suka tashi daga 419 a 2023 zuwa 1,862 a 2025. A Sokoto ma, adadin ya ƙaru daga 409 zuwa 914 a wannan lokaci.
A Kebbi da Yobe, waɗanda a baya ba sa cikin jihohin da suka fi fama da rikici, an kuma samu ƙaruwa a mace-mace. A Kebbi, adadin ya karu daga 141 a 2023 zuwa 463 a 2026, yayin da Yobe ta tashi daga 228 zuwa 430 a daidai wannan lokaci.
Waɗannan alƙaluma na nuna yadda tasirin rikicin ke bazuwa daga wuraren da aka saba dangantawa da matsalar tsaro zuwa wasu jihohin da a baya ba su fuskantar irin wannan matsin lamba.
Rikici da ya wuce iyakokin Najeriya
Abin da ya fi tayar da hankalin Majalisar Ɗinkin Duniya shi ne yadda rikicin ya fara zama ba matsalar Najeriya kaɗai ba. Yayin da dubban mutane ke ci gaba da tsallaka iyakoki zuwa Nijar da Benin, matsalar na ƙara zama ta shiyya baki ɗaya.
Idan ba a samu raguwar hare-hare da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da suka fi fama da rikici ba, akwai yiwuwar adadin masu gudun hijira ya ci gaba da ƙaruwa. Wannan ne ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ke kira ga ƙasashen duniya su ƙara tallafa wa ƙasashen da ke karɓar baƙi tare da taimakawa ƙoƙarin magance matsalar tsaro a Najeriya.
A yanzu, maganar da ake yi daga Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta shafi batun gudun hijira kawai ba ce, har ma da fargabar cewa rashin tsaro a Najeriya na iya ci gaba da yin tasiri ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin yankin Yammacin Afirka.
Hukumomin Nijar da sauran ƙasashen da ke karɓar masu gudun hijirar sun nuna haɗin kai ta hanyar ware filaye da samar da matsugunan wucin gadi. Sai dai ƙarfinsu na kula da yawan mutanen da ke ci gaba da shigowa na ƙara raguwa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai buƙatar ƙarin taimako daga ƙasashen duniya domin samar da abinci, ruwa, magani da matsuguni. Haka kuma tana fargabar cewa ci gaba da kwararar mutane zai iya sanya matsin lamba a kan albarkatu da ayyukan jin daɗin jama'a a ƙasashen da ke karɓar baƙin.
Me hakan ke nufi?
Da yake tsokaci kan rahotonnin, shugaban kamfanin Beacon Security Services, Dokta Kabiru Adamu, ya bayyana cewa rahoton ya fito ne daga wata sananniyar cibiyar da ta dade tana tattara alkaluman rikice-rikice da kashe-kashe a duniya.
"A wannan karon sun mayar da hankali ne kan Boko Haram da ISWAP, sannan suka kwatanta ayyukansu a ƙasashen da ke yankin Tafkin Chadi, wato Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru," in ji shi.
Ya ce rahoton ya nuna cewa an samu raguwar hare-haren waɗannan ƙungiyoyi a Najeriya idan aka kwatanta da wasu lokutan baya, yayin da a wasu ƙasashe musamman Kamaru aka samu ƙaruwa.
A cewar Dokta Adamu, masu rahoton sun danganta raguwar hare-haren da aka samu a Najeriya da wata yarjejeniya ko sulhun da gwamnatin Najeriya ta yi da wani ɓangare na masu tayar da kayar baya.
"Rahoton ya nuna cewa akwai alaƙa tsakanin wannan raguwar hare-hare da sulhun da gwamnatin Najeriya ta yi da wani sashe daga cikin ƙungiyar. A fahimtarsu, wannan ne ya taimaka wajen rage yawan hare-haren da ake gani a Najeriya," in ji shi.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa dole ne a fahimci iyakar abin da rahoton ya ƙunsa kafin a yanke hukunci game da yanayin tsaro gaba ɗaya.
Me ya sa ƴan Najeriya ke tsallakawa ƙasashe maƙwabta?
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fito fili a rahoton shi ne yadda ake samun ƙarin ƴan Najeriya da ke tsallakawa zuwa Nijar da Benin domin neman mafaka.
Dokta Adamu ya ce wannan ba sabon abu ba ne, domin tun tuni rahotanni daban-daban suka nuna cewa hare-haren 'yan ta'adda na tilasta wa mutane barin muhallansu.
"Ba wani dogon dalili ba ne. Hare-haren da ake kai wa ƙauyuka ne ke sa mutane gudun hijira," in ji shi.
Ya bayyana cewa duk da tsauraran matakan tsaro a manyan biranen jihar Borno, ƙauyuka da dama na ci gaba da fuskantar barazana.
"Idan ka fita daga cikin manyan birane zuwa karkara, za ka ga kamar ana fafatawa ne tsakanin gwamnati da waɗannan ƙungiyoyi kan wanda ya fi iko da yankin," in ji Kabiru Adamu.
A cewarsa, rashin tsaro a kan iyakokin Najeriya da makwabtanta na ƙara sauƙaƙa wa mutane tsallakawa.
"Wasu lokuta mafi sauƙi ga mazauna yankunan shi ne su tsallaka zuwa wata ƙasa domin neman kariya daga hare-haren da ake yawan kai musu."
Sai dai Kabiru Adamu ya yi watsi da ra'ayin cewa Nijar ta fi Najeriya tsaro a yankunan da matsalar take kamari.
"Idan ka dubi yankunan da ke kusa da iyaka, babu wani babban bambanci. Garuruwan da ke kewaye da Tafkin Chadi a Najeriya, Nijar da Chadi na fuskantar kusan matsaloli iri ɗaya," in ji shi.
Ya ce abin da ya bambanta wasu lokuta shi ne irin matakan kariya da gwamnatocin ƙasashen ke ɗauka domin kare al'ummominsu.
A cewarsa, ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai har yanzu suna anfani da ƙarancin tsaro a kan iyakoki wajen motsawa daga ƙasa zuwa ƙasa.
"Suna iya fita daga Najeriya zuwa Chadi ko Nijar idan an matsa musu, sannan su sake dawowa idan sun samu dama."
'Da sauran aiki a gaba'
Duk da rahoton na nuna raguwar hare-hare daga Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabas, Dokta Adamu ya yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki hakan a matsayin cikakkiyar nasara a yaƙin da Najeriya ke yi da rashin tsaro ba.
"Idan ka tsaya kan Boko Haram da kuma arewa maso gabas kaɗai, kana iya cewa an samu raguwar hare-hare da kashe-kashe," ya bayyana.
Sai dai ya ce idan aka faɗaɗa nazarin zuwa sauran yankunan ƙasar, sakamakon ya sauya.
"Idan ka haɗa arewa maso yamma da jihohin tsakiyar Najeriya, za ka ga alƙaluman ƙaruwa suke yi, ba raguwa ba."
Ya ƙara da cewa rahoton ACLED ya mayar da hankali ne kan Boko Haram da yankin arewa maso gabas kawai, abin da ke nuna cewa akwai buƙatar kallon matsalar tsaro daga faɗaɗɗen mahanga.
"Duk wanda zai karanta rahoton ya kamata ya fahimci cewa yana magana ne kan wani sashe na matsalar. Idan aka dubi ƙasar gaba ɗaya, har yanzu akwai ƙalubalen tsaro masu girma da ke bukatar kulawa," in ji Dokta Kabiru Adamu.