Yadda Kotun Duniya ta tabbatar an yi wa Musulman Rohingya kisan ƙare-dangi

    • Marubuci, Jonathan Head
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Kudu maso Gabashin Asiya
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kotun Duniya ta ICJ ta samu ƙasar Myanmar da laifin aikata kisan kiyashi kan tsirarun Musulman Rohingya.

Kotun ta cimma wannan matsaya ne bayan samun ƙuri'u tara da ke goyon bayan hukuncin cewa Myanmar ta aikata abin da ya nuna an yi niyyar hallaka al'ummar Rohingya gaba ɗaya ko kuma wani ɓangare mai yawa daga cikinsu.

Wakiliyar BBC ta ce wannan wani hukunci ne mai matuƙar tarihi kuma kotun ta yanke hukuncin cewa akwai shaidu goma da suka tabbatar da kisan ƴan Rohingya a 2017.

Wannan ne karo na farko a tarihin kotun da aka samu wata ƙasa da laifin aikata kisan kiyashi.

An kafa kotun ICJ a shekarar 1945 don taimakawa wajen sasanta takaddama tsakanin kasashe, ba don yin shari'a kan laifukan ƙasa da ƙasa ba. Duk da haka, an zaɓi ta ne don magance hare-haren da ake kai wa 'yan Rohingya a Myanmar saboda babu wasu hanyoyin da za a bi wajen rama wa waɗanda abin ya shafa.

Hukumomin Myanmar sun musanta zargin kisan kare dangi, suna masu cewa suna mayar da martani ne kawai ga ayyukan ta'addanci da 'yan tawayen Rohingya ke yi.

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2018, wanda ya dogara da daruruwan hirarraki, ya ce dabarun rundunar "ba su dace da barazanar tsaro ta gaske ba".

Ya ce dole ne a binciki manyan jami'an soji a Myanmar kan kisan kare dangi a Jihar Rakhine da laifukan cin zarafin bil'adama a wasu yankuna. Myanmar ta yi watsi da rahoton.

Ganin cewa Myanmar ba mamba bace a kan Kotun Manyan Laifuka ta Duniya, ba zai yiwu a shigar da ƙara a can kan jami'an da ake zargi da aikata laifuka a Jihar Rakhine ba.

Madadin haka a watan Nuwamba na 2019, Gambia, wacce ke samun goyon bayan Kungiyar Hadin Kan Musulunci, ta shigar da kara a kotun ICJ, tana mai jayayya cewa dukkan kasashe suna karkashin Yarjejeniyar Kisan Kiyashi.

Ta zargi gwamnatin Myanmar, ba sojoji kawai ba, da kisan kare dangi.

Wannan sabon abu ne a dokokin ƙasa da ƙasa, ƙasar da doka ba ta shafa kai tsaye ba, tana jayayya cewa tana da ikon yin ƙara saboda duk wani keta wannan muhimmin yarjejeniya ya shafe ta a kaikaice.

Myanmar ta yi adawa da wannan hujja, amma alkalan kotun ICJ sun yanke hukuncin cewa Gambia ce ke da hurumin shigar da ƙarar.

Shari'ar ta ƙara jan hankali ne lokacin da Aung San Suu Kyi, wadda a lokacin ke jagorantar gwamnatin da aka zaɓa a Myanmar, ta yanke shawarar kare ƙasarta a shari'ar farko da aka gudanar a kotun Hague. Matakin nata ya jawo mata suka sosai.

Tana da gagarumin tasiri kan ayyukan sojojin Myanmar a jihar Rakhine, amma ƙin yin Allah wadai da ayyukansu ya ɓata wa mutane da dama rai, musamman waɗanda a baya suka yaba da jarumtakarta da jajircewarta wajen kare ƙa'idojin dimokuraɗiyya.

Tun bayan hambarar da ita daga mulki a shekarar 2021 da kuma tsare ta a gidan yari, sojojin da suka karɓi mulki sun naɗa sabbin shugabanni domin tafiyar da harkokin ƙasar.

A tarihi, tabbatar da cewa an aikata kisan kare dangi abu ne mai matuƙar wahala. Alƙalan kotuna kan yi taka-tsantsan sosai wajen yanke hukunci kan irin waɗannan tuhume-tuhume.

A mafi yawan lokuta, idan babu wani takamaiman shiri na kisan kare dangi a rubuce, kamar yadda aka samu a lokacin mulkin Nazi, alƙalai kan buƙaci shaidu masu ƙarfi da za su tabbatar da cewa manufar kisan kare dangi ita ce kawai hanyar da za a iya fahimtar ayyukan waɗanda ake tuhuma.

Lokacin da Bosnia-Herzegovina ta shigar da ƙarar kisan kare dangi kan Serbia a kotun ICJ a shekarar 1993, kotun ta ɗauki shekaru 14 kafin ta yanke hukunci. Ta tabbatar da cewa wasu abubuwan da suka faru, ciki har da kisan kiyashin Srebrenica a shekarar 1995, sun kasance kisan kare dangi. Sai dai kotun ta ce babu isassun shaidu da za su tabbatar da cewa Serbia na da niyyar aikata kisan kare dangi, duk da cewa ta gano cewa ƙasar ta gaza ɗaukar matakan hana kisan kiyashin.

Lauyoyin Myanmar da Aung San Suu Kyi sun gabatar da irin wannan hujja a shari'ar.

Suu Kyi ta ce tawagar lauyoyin Gambia ta yi kuskuren bayyana rikicin da kuma matakan soji a matsayin wani abu mai sauƙin fahimta, alhali kuwa lamarin ya fi haka sarkakiya. Ta kuma amince cewa an aikata laifukan yaƙi kan al'ummar Rohingya, amma ta ce hakan ba ya zama hujjar cewa an aikata kisan kare dangi da niyya.

Amma ga dimbin 'yan Rohingya da ke zaune a ƙasashen waje, wannan hukuncin na da matuƙar muhimmanci.

"Wannan tamkar amincewa ce da irin wahalar da muka sha," in ji Mohammed Nowkim, wani ɗan kabilar Rohingya da aka tilasta wa barin garinsu na Buthidaung da ke jihar Rakhine a shekarar 2017, wanda a yanzu yake zaune a Kanada.

"Ga 'yan Rohingya, wannan shari'a na nufin amincewa da irin wahalar da muka sha bayan shekaru masu yawa ana musanta abin da ya faru da mu. Mun daɗe muna jiran ganin an yi mana adalci, ba wai daga wannan shekarar kaɗai ba."

Shi da sauran masu fafutukar kare haƙƙin 'yan Rohingya na fatan cewa matakin da Gambia ta ɗauka zai sa ƙarin ƙasashe su haɗa kai wajen neman mafita da za ta ba su damar komawa gidajensu a jihar Rakhine cikin aminci.

Fiye da mutane miliyan ɗaya ne suka makale a sansanonin 'yan gudun hijira a Bangladesh, inda ba a ba su damar yin aiki, yayin da tallafin kuɗi daga ƙasashen duniya ke ci gaba da raguwa.

Sai dai akwai manyan ƙalubale da ke hana cimma wannan buri.

Jihar Rakhine ta fada cikin rikici tsakanin sojojin Myanmar da rundunar 'yan tawayen Arakan, wadda a yanzu ke iko da mafi yawan yankunan jihar. Al'ummar Rakhine ta asali ce ke goyon bayan rundunar, kuma da dama daga cikinsu na adawa da ra'ayin mayar da 'yan Rohingya yankin.

An lalata ƙauyuka da dama na 'yan Rohingya gaba ɗaya. Haka kuma, tallafin da suke samu daga ƙasashen duniya ya ci gaba da raguwa tsawon shekaru.

Ko da wani hukunci na tarihi da Kotun Duniya ta yanke kan zargin kisan kare dangi ba zai iya sauya wannan mummunan yanayi kai tsaye ba.