Amurka za ta kori ƴan Najeriya 157 daga ƙasar
Ma’aikatar Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta ƙara sunayen wasu ’yan Najeriya 24 a cikin jerin mutanen da take shirin kora daga ƙasar, wanda hakan ya sa jimillar ’yan Najeriyar da ke cikin jerin ta kai 157.
Hukumar ta ce ta kama mutanen ne bisa zargin aikata manyan lafuka a Amurka.
Bayanan da ke shafin hukumar cikin cikin gidan sun nuna cewa sabbin mutanen da aka ƙara a jerin an kama su ne bisa zarge-zargen laifuffuka da suka haɗa da damfara, halasta kuɗaɗen haram, laifuffukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, satar bayanai da kuma muzgunawa ƙananan yara.
To amma, wallafa sunayen mutanen a shafin hukumar ba yana nufin cewa an same su da laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba.
Hukumar ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Donald Trump na fitar da ’yan ƙasashen waje da ake zargi da aikata manyan laifuffuka daga Amurka.
A cikin bayanin da aka wallafa tare da jerin sunayen, hukumar ta ce tana ƙokarin cika alƙawarin Shugaba Trump na fitar da mafi munin masu laifi daga cikin baƙin haure da ke zaune a Amurka.
To sai dai hukumar ba ta bayyana lokacin da za a tisa ƙeyar mutanen zuwa Najeriya ba.
A watan Satumbar da ya gabata ne hukumar ta tsaron cikin gida ta Amurkan ta ce ta kama ’yan Najeriya 134 a cikin jerin masu fuskantar kora daga Amurka kan zarge-zargen damfara da halasta kuɗaɗen haram.
Tun bayan komawarsa kan karagar mulkin Amurka a 2024, Shugaba Trump ya ƙudiri aniyar rage baƙin haure a Amurka, ta hanyar korar wadanda ya ce sun shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida, ko wadanda takardun zamansu suka ƙare.
Amurka dai na daga cikin ƙasashen duniya da ke yawan fuskantar baƙin haure daga ƙasashe duniya daban-daban, musamman matalautan ƙasashen.
Baƙin haure kan je ƙasar ne sakamakon dalilai mabambanta da suka haɗa da gudun hijira da neman ingantacciyar rayuwa ko karatu da sauransu.